DAGA ZAUREN
HANYAN***TSIRA
YAUSHENE YAFI DACEWA AYI SAHUR ???
AMSA
------------------------------------
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
A sunnace anaso a Jinkirta yin sahur zuwa kusan ketowar Alfijir.Hadisi ya tabbata daga Anas dan Malik, daga Zaid
Bn Thabit (R.A.) yace:"Munyi Sahur tare da manzon Allah (S.A.W.) bayan wannan sai manzon Allah (S.A.W.) ya tashi zuwa sallah.Sai Anas ya tambayi Zaid bin Thabit cewa:Menene tsakanin cin sahur dayin sallar Asuba ?
Sai yace:Gwargwadon Aya 50 (watau mutum ya karanta Aya 50)".(Kuduba Sahihul Bukhari, 1921)(Ko sahihu muslim 1097).
Akwai kuma hadisin Sahl ibn Sa'ad yace:-
"Na kasance inayin sahur cikin iyalina bayan wannan sai inyi gaggawa domin samun Sujada (Sallah) da manzon Allah (S.A.W.)".Wannan yanuna cewa ana yin sahur ne dab da ketowar Alfijir.(Kuduba Sahihul Bukhari, 1920).
www.hanyantsira.mywapblog.com
09039016969
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
No comments:
Post a Comment