GASKIYA DA 'DACI YAKE, AMMA SAI NA FA'DA
DAGA ZAUREN
HANYAN***TSIRA
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
Kayi abota da wanda ke rike sirrinka ya rufe
aibunka, ya fadi alkhairinka. Idan baka sameshi ba to kazama kaine abokin kanka.
Idan kana son kaji dadin zama da mutane ka nisanci mugun zato da yawan ikirari da leken asirin mutane.
Abokin kwarai yana da wuyar samu, yana da wuyar bari,kuma ba a mantashi.Alamomin wadanda suka auri duniya suka saki
lahira guda biyar ne;
1* Basu jiran sallah kafin atayar da ita.
2* Basu karanta Alkur'ani sai lokacin bukata.
3* Ba karbar nasiha ballantana suyi amfani da ita.
4* Basu zuwa wurin wa'azi ballantana su saurareshi.
5* Basu neman sanin addini ballantana suyishi yadda ya kamata.
Ababuwa ukku suna hana arziki;
* Yawan bacci
* Yanke zumunta
* Cin amana.
Bebe yana sha'awar karanta Alkur'ani, #Kurma yana son saurarenshi
Makaho yana son ya kalle shi.Kai da Allh ya baka ji da gani da magana, sau nawa kake karantashi?
Mutanen kirki kamar iccen mangwaro suke; mutane na jifar su da dutse su kuma suna sako musu nunannun'ya'ya masu dadi.Allah yasa mu dace Ameen.
Naku; Muh'd Abba Gana
No comments:
Post a Comment