FALALAR WATAN AZUMIN RAMADAN DA IRIN ROMON DA YAKE CIKINSA.
DAGA ZAUREN
HANYAN***TSIRA
FALALAR WATAN AZUMIN RAMADAN DA IRIN ROMON DA YAKE CIKINSA.
TAMBAYA ???
MENENE FALALAR WATAN AZUMIN RAMADAN ???
AMSA
------------------------------------
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
Azumin Ramadan yanada falaloli da yawa.Daga cikin falalar azumin sun hada da:-
1. Yana kankare zunubin mutum kamar yadda yazo a hadisin Khuzaifah (R.A.) Yace
Manzon Allah {S.A.W} yace:"Fitinar mutum acikin iyalansa, da dukiyarsa ko makwabcinsa sallah da azumi da sadaka suna kankaresu (Bukhari).
2. Yazo a hadisai da dama cewa:Dukkan aikin Dan Adam nasane Malaikune suke rubuta shi, amma azumi wannan na Allah ne Shi Yake sakawa wanda yayi shi (hadisin ya tabbata
acikin targhib wattarhib, juz'I na farko shafi na 75).
3. Hadisi kuma ya tabbata daga Jabir dan Abdullahi(R.A.) daga Manzon Allah {S.A.W.} cewar:Azumi garkuwane da dan Adam zaiyi garkuwa
dashi daga wuta.
3. Sannan hadisi ya tabbata daga Mu'azu dan Jabal (R.A.) cewa:
Hakika Manzon Allah {S.A.W.} yace dashi shin bazan nuna maka kofofin alheriba ?Sai yace na'am ya Rasulullah.Sai yace azumi garkuwane.
4. Sannan akwai hadisin Abi Umamata (R.A.) yace:"Nacewa Manzon Allah (s.a.w) ka umarceni da wani aiki da Allah Zai amfanar dani dashi sai yace ka lizimci azumi, domin babu kamarsa"
(dukkan wadanna hadisai sun tabbata a targhib, tahakikin Sheikh Albani juzu'I na farko shafi na 578).
6. Azumi kuma shine sababin tsoron Allah.
7. A lokacin azumin Ramadan ana bude kofofin Aljanna, kuma ana kulle kofofin Jahannama sannan
a daure shaidanu kamar yadda ya tabbata a hadisin Abi Huraira.(Kuduba Sahihul Bukhari 1899).
8. Hadisi ya tabbata wanda Imam Tirmizi ya ruwaito cewar Manzon Allah {S.A.W.} yace:"Warin bakin mai azumi yafi kamshi fiye da turaren Al-miski a wurin Allah.Hadisine sahihi.
9. Sannan wani hadisin ya tabbata daga Sahl bin Sa'ad (R.A) daga Manzon Allah {S.A.W.) yace:
Acikin Aljanna akwai wata kofa ana kiranta
Rayyanu, masu azumi zasu shigeta ranar tashin kiyama, babu wanda zai shigeta sai su.Idan sun shiga sai a kulleta babu wanda zai sake shiga(Kuduba Sahihul Bukhari 1896).
Tirmizi yakara bayani a cikin riwayarsa cewar wanda ya shigeta bazaiji kishin ruwaba (Qishirwa
ba) har abada.
www.hanyantsira.mywapblog.com
whatsapp
09039016969
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Home »
FATAWA AKAN AZUMI.
» FALALAR WATAN AZUMIN RAMADAN DA IRIN ROMON DA YAKE CIKINSA.
FALALAR WATAN AZUMIN RAMADAN DA IRIN ROMON DA YAKE CIKINSA.
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
No comments:
Post a Comment