Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

FALALAR YIN TASBIHI

FALALAR YIN TASBIHI.
===================
Abu hurairi Allah ya yarda dashi yace:
Manzon Allah (s.a.w) yace:
Akwai wasu kalmomi guda biyu masu sauqin fada
a harshe, masu nauyi akan mizanin (awon ayyuka
ranar alqiyama).
Masu soyuwa ga Allah (s.w.t) mai yawan jinqai.
Ga kalmomin.
ﺳﺒﺤﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺑﺤﻤﺪﻩ ﻭﺳﺒﺤﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ ¤
Translation
SUB-HANAL LAHI WABI HAMDIHI WA SUBHANAL
LAHIL AZEEM.
Fassara.
Tsarki ya tabbata ga Allah tare da godiya a
gareshi.
Tsarki ya tabbata ga Allah mai girma.
Ya Allah kasa duk cikinmu babu dan wuta.
Dan Allah kudinga yin like da comment ko kuma
kuyi share dinsa domin 'yan uwanku su amfana.

hanyantsira.mywapblog.com
Share:

Alamomin maiyin Riya guda 3.

MAI RIYA YANA DA ALAMOMI GUDA UKU.
Sayyadina Ali (R.a) Yace:
"Mai RIYA yana da alama guda Uku.
1. Idan shi kadaine kasala tana hanashi.
2. Idan kuma yana tareda mutane to yana zama
mai nishadi, saiya kara yawan aiki duk yayin da
aka yabeshi.
3. Yana ragewa idan aka zarge shi.
Al-Fudail dan Iyadh yace:
"Idan kabar gabatar da aiki don jin tsoron Mutane
to kayi Riya.
Idan kuwa kayi aiki don mutane su gani to kayi
karamar shirka.
Yin Ikhlasi kuwa shine Allah ya kareka ga barin yin
guda biyun.
Muna Rokon Allah Yaa Karemu Daga Shirka da
Riya, Ya azurtamu Da Ikhlasi cikin ayyukanmu da
zantukanmu, motsinmu dayin shirunmu.

hanyantsira.mywapblog.com
Share:

KADA KA SHAGALTU DA LAIFUKAN MUTANE [08:49 PM, 18-Mar-15]

"KA SHAGALTU DA LAIFUKANKA KADA KA
SHAGALTU DA LAIFUKAN MUTANE"
Duk yayin da ka shagaltu da ganin laifukan
mutane, kakutsa cikin neman inane kura-kuran
mutane suke ???
Ma'ana: Kai baka yiwa kanka muhasaba (Hisabi),
to, laifunka zasu yawaita batare daka ankara ba.
Masu iya magana suna cewa:
LAIFI TUDU NE.... Saika take naka sannan zaka
hango na wani!
Duk mutumin da bai d'auki kansa mai laifi ba, baya
dinga bibiyar irin aikin da yake aikatawa yana
tantancewa, baya zama mai ganin kura-kuran
kansa! To, lallai akwai nadama a qarshen
rayuwarsa.
Domin kuwa zai tattara zunubai masu tarin yawa a
kansa, tunda ya kawar da kansa daga ganin
laifukansa, ya shagaltu da laifukan al'umma, ta
inda ganinsa ya taqaitu ga ganin laifukan mutane.
'Yan'uwa mu gyara ayyukanmu, mu wanke
zuqatanmu, mu rinqa yiwa kawunanmu hisabi, mu
kasance masu tsanin tuhumar kawunanmu, tareda
tuba daga munanan ayyukanmu, ta wannan sai mu
kasance bayi na qwarai, dalilin haka sai Allah ya
tausaya mana ya gafarta mana ya shigar damu
cikin rahmarsa.
*******************
Ya Allah ka gafarta mana ka rabamu da son zuciya,
ka shiryar damu hanya madaidaiciya, ka tabbatar
damu a kan tafarkin tsira yazuwa Al-jannah.


www.hanyantsira.mywapblog.com
Share:

SIRRIN ZAMA DA MIJI

SIRRIN ZAMA DA MIJI

{KASHINA 3}

(AMSA KIRAN MIJI)


BY

MUHD*ABBA*GANA
09039016969

yazo a cikin hadisin manzon Allah (SAW) cewa idan miji yayi kiran matarsa to ya zama dole ta je koda tana akan deruna don haka wannan hadisi wani ban garene dayake nuna wajab ci akan mace ta je kiran mijinta ako wane hali take,kuma yana nuna cewa wajibine ta amsa kiran mijinta domin biyan bukatarsa koma wace iri ce, dan haka ya kamata mata su kiyaye domin jin dadin mazajensu. kuma har yanzu dai shi wannan hadisi yana nuna watsar da yanga ko kuma jan aji a gurin ma aurata, don haka babu zancen jan aji agurin ya mace indai a cikin sha'anin aure kuma in ya zama umurnin bai sabawa koyarwar addininmu ba. Allah bamu ikon gyarawa
Share:

DANNE ZUCIYA A LOKACIN FUSHI.

DANNE ZUCIYA A LOKACIN FUSHI. kada kayi gaba da mai son yin gaba dakai, idan ka ganshi kayi masa sallama. Kada kadamu da hassadan mai hassada, bashshi muguntansa zata koma kansa. ************** "Duk wanda yace duniya itace mafi mahimmanci a gareshi, To tabbas bakin cikinsa zai yawaita". ************** kayi hakuri wurin barin sabon Allah, domin wani abun kanaso amma babu yadda zakayi, hakanan zaka bashshi don jin tsoron azabar Allah. ************** "Ba abin alfahari bane don kayi rinjaye ga mai karfi, Abin alfahari shine ka yi adalci ga mai rauni". ************** Wanda yafada maka magana mai zafi, kalma mai daci da 'kuna, mayar masa da tattausa mai taushi kamar ruwan sanyi. ************** "ALLAH yabamu ikon ruqo da gaskiya!! www.hanyantsira.mywapblog.com
Share:

ABUBUWA 19 SUNA KASHE ZUCIYA

ABUBUWA GUDA (19) SUNA SANYA BUSHEWAR
ZUCIYA DA KUMA MUTUWA BABU IMANI:
1. Rashin yarda da Qaddara.
2. Wulakantar da Sallolin Farilla.
3. Mu'amala da Kudin Ruwa (interest).
4. Cin dukiyar Al'ummar Musulmi ta hanyar haram.
5. Shan giya da sauran kayan maye.
6. Bijire ma Iyaye tareda wulakantar da zancensu.
7. Chanpi da tsafe-tsafe.
8. Zarcewa cikin Zina, Madigo, Luwadi etc.
Batare da tuba ba.
9. Halasta duk wani abinda Allah ya haramta.
10. Rashin Girmama Abubuwa ko mutanen da
Allah ya girmama su.
11. Sakin baki akan Manzon Allah, ko Ahalin
gidansa ko Sahabbansa masu tsarki.
12. Kisan kai cikin ganganci.
13. Debe kauna daga samun rahamar Allah.
14. Qin karatun Alkur'ani da zikirin Allah..
15. Dogon buri tare da rashin tunanin lahira.
16. Cin amana, da rashin tsayawa kan gaskiya, da
kuma rashin cika alkawari.
17. Zaluntar marayu da Makobta da masu Qaramin
Qarfi.
18. Rashin jin zafi idan an ta'ba hakkin Allah da
Manzonsa.
19. Bayar da shaidar Zurr.
Muna roqon Allah ya kiyaye mana Imaninmu.

www.hanyantsira.mywapblog.com
Share:

AKWAI WATA KASUWA ACIKIN ALJANNAH.

MANZON ALLAH (S.A.W) YACE:
Lallai acikin aljannah akwai wata kasuwa da
ake zuwanta a ranar juma'a Idan mutane sukaje
wannan kasuwa sai wata iska tazo musu ta arewa
saita shafi fuskokinsu da rigunansu, Sai suqara yin
kyau
Sai sukoma wajen iyalansu.
A lokacin suma sun qarayin kyau
sai iyalansu suce musu wallahi anqara muku kyau.
Sai suma sukalli iyalansu suga sunqara kyau.
Sai suma suce musu lallai kuma anqara muku kyau
bayan fitarmu.
Sahih Muslim:2833
Ya Allah kasa muna cikin wadannan salihan bayi.
Share:

SIRRIN ZAMA DA MIJI

mamatan-kwarai.jpg

SIRRIN ZAMA DA MIJI

(TSARIN MU'AMALA TSAKANIN ANGO DA AMARYA)

BY

MUHD*ABBA*GANA
09039016969

Akwai abubuwa da suka zama wajibi a gurin ma aurata domin koruwar zamanci da soyayyar a tsakanin su, kamar na musulunci to da farko dai Allah madaukakin sarki ya fada a cikin alqur'ani mai girma cewa yana daga cikin ayoyinsa cewa ya sanya mana mataye daga garemu domin mu samu nutsuwa dasu. to a nan yakamata a ce a duk lokacin da ango da amarya suke tare a matsayin ma auratan juna ana son bukatarsu da zaman lafiya da kwanciyar hankali atsakaninsu. dan haka ashe a duk lokacin da amarya tatare a gidan mijinta ana bukatar tazama wacce take kwantar da hankalin mijinta ta kuma samar masa da nutsuwa ba waccce zata sa mijinta a cikin tashin hankali da damuwa ba. yana da kyau amarya takiyaye wasu abubuwa da kyau domin sune zasu taimaka mata izuwa samun dorewar zaman lafiya da kuma soyayya atsakanin ta da mijinta ga abubuwan kamar haka:

A KYAUTATA MU'AMALAR MIJI

wajibine a gurin mace ta kyautata mua mala atsakaninta da mijinta a lokacin da suke tare a gida ta zamai mai kiyaye duk wani abinda zai bata masa rai, karta zama mai cutar dashi da har shenta ko kuma da ai kinta koda kuwa zayi yarane don haka yana da kyau mace tayiwa har shen ta cin zami daga barin fadar abunda zai janho fushin mai gidan ta. insha Allah gobe zan daura daga inda na tashi
Share:

SIRRIN ZAMA DA MIJI

SIRRIN ZAMA DA MIJI

(TSARIN MU'AMALA TSAKANIN ANGO DA AMARYA)

BY

MUHD*ABBA*GANA
09039016969

Akwai abubuwa da suka zama wajibi a gurin ma aurata domin koruwar zamanci da soyayyar a tsakanin su, kamar na musulunci to da farko dai Allah madaukakin sarki ya fada a cikin alqur'ani mai girma cewa yana daga cikin ayoyinsa cewa ya sanya mana mataye daga garemu domin mu samu nutsuwa dasu. to a nan yakamata a ce a duk lokacin da ango da amarya suke tare a matsayin ma auratan juna ana son bukatarsu da zaman lafiya da kwanciyar hankali atsakaninsu. dan haka ashe a duk lokacin da amarya tatare a gidan mijinta ana bukatar tazama wacce take kwantar da hankalin mijinta ta kuma samar masa da nutsuwa ba waccce zata sa mijinta a cikin tashin hankali da damuwa ba. yana da kyau amarya takiyaye wasu abubuwa da kyau domin sune zasu taimaka mata izuwa samun dorewar zaman lafiya da kuma soyayya atsakanin ta da mijinta ga abubuwan kamar haka:

A KYAUTATA MU'AMALAR MIJI

wajibine a gurin mace ta kyautata mua mala atsakaninta da mijinta a lokacin da suke tare a gida ta zamai mai kiyaye duk wani abinda zai bata masa rai, karta zama mai cutar dashi da har shenta ko kuma da ai kinta koda kuwa zayi yarane don haka yana da kyau mace tayiwa har shen ta cin zami daga barin fadar abunda zai janho fushin mai gidan ta. insha Allah gobe zan daura daga inda na tashi
Share:

Malam gidanmu yana kusa da masallaci, muna jiwo kiran sallah da ikama ta lasifika, koya halatta in bi sallar jam’i daga laspika ???

tambaya-da-amsa.jpg Assalamu Alaikum Malam gidanmu yana kusa da masallaci, muna jiwo kiran sallah da ikama ta lasifika, koya halatta in bi sallar jam’i daga laspika ??? (Daga Husna Ahmad). AMSA: ----- DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI. To ‘yar’uwa wannan mas’alar takasu kashi biyu: 1- Idan ya zamana dakinki yana like da masallacin, to tabbas wannan ya halatta, saboda Nana A’isha (R.A) tabi sallar kisfewar rana daga ‘dakinta, a zamanin Annabi (s.a.w) kamar yadda Bukhari ya rawaito hakan a hadisi mai lamba ta: 184, sannan Abdur Razzaq ya rawaito cewa: Ta kanbi ragowar salloli daga dakinta” kamar yadda yazo a littafinsa na (al-Musannaf, hadisi mai lamba ta: 4883). Saboda ‘dakinta ajikin masallacin Annabi (s.a.w) yake. 2. Idan ya zama ‘dakin baya kusa da masallacin, to zance mafi inganci shine: Bai halatta kibi ba, saboda a zamanin Annabi (s.a.w) sahabbai suna haduwa a wuri ‘daya ne idan zasuyi sallar jam’i, basa rarrabuwa. Wannan sai yake nuna cewa, hakan shine siffar sallar jama’i, sannan jera sawu a sallah, wani yana bin wani dole ne a sallar jam’i. Allah Shine Masani.
Share:

Hadith 2

Abu Musa Al-Ash'ari (May Allah be pleased with
him) reported:
The Messenger of Allah (peace be upon him) said,
"When a slave's child dies, Allah the Most High
asks His angels, 'Have you taken out the life of the
child of My slave?"
They reply in the affirmative. He then asks, 'Have
you taken the fruit of his heart?' They reply in the
affirmative.
Thereupon he asks, 'What has My slave said?'
They say:
'He has praised You and said: Inna lillahi wa inna
ilaihi raji'un (We belong to Allah and to Him we
shall be returned).
Allah says:
'Build a house for My slave in Jannah and name it
as Bait-ul- Hamd (the House of Praise)."' [At-
Tirmidhi]
Share:

Hadith 001

Narrated Anas bin Malik:
The Prophet (peace be upon him) said,
“None of you should wish for death because of a
calamity befalling him; but if he has to wish for
death, he should say:
“O Allah! Keep me alive as long as life is better for
me, and let me die if death is better for me.’ ”
Sahih Al-Bukhari – Book 70 Hadith 575
Share:

Yadda ake wankan janaba

YADDA AKE YIN WANKAN JANABAH.
==============
Salam, malam dan Allah kayi mana karin bayani
akan wankan janaba da wankan haila dan har
yanzu akwai masu damuwa akai.
(daga Abdullahi mani babba)
AMSA
====
Da farko Idan Mutum yashiga Ban-'daki (bathroom)
Zai farane da wanke Najasar dake tare dashi.
Ma'ana, Zai Fara wanke Al'aurarsa, da kuma duk
wuraren da Maniyyi (ko jinin) ya taba ajikinsa.
(Misali tun daga Cibiyarsa har zuwa cinyoyinsa).
* Kuma Zai Qulla niyyah ne yayin da yake wanke
Al'aurarsa.
* Sannan saiya wanke dukkanin Gabobinsa na
Alwala.
Amma sau dai-dai ko 2 ko 3 duk wanda mutum
yayi daidaine.
* Idan kaga dama zaka bar Qafafunka, Sai akarshen
wankan.
* Sannan Saika wanke Kanka Sau Uku.
(tare da wuyanka da fuskarka gaba dayanta).
* Saika wanke tsagin Jikinka na Dama, har zuwa
Kafarka ta dama.
* Sai kuma tsaginka na Haggu, kahada har
Qafarkata haggu din.
* Ya zama wajibi kacire zobe daga hannayenka
(Idan ya matseka) kuma dole ka Tsetsefe dukkan
yatsunka na hannu dana Qafa.
* Ka chuda Kafarka sosai.
Musamman idan inhar kanada kaushi.
* idan kazo wanke kowanne tsagi, ka tabbatar da
cewa kana Chutchuda Bayanka sosai.
* Idan kuma hannunka baya iya kaiwa, sai kasamo
wani Tsumma ko Kyalle mai tsafta, KaJiqa-shi,
Sannan ka Chutchuda dashi.
* dole ne ka chutchuda Ko ina ajikinka.
Musamman ma idan kana da Qiba.
* Dolene Ka wanke Duburarka sosai tun farko.
Kada kayi la'akari da cewar "Ai bakayi bahaya ba".
A'a. Ai nan dinma jikinka ne.
Idan baka wanke taba, to wankanka bai yiwu ba.
* Ka kula da Ramin cibiyarka.
Ka tabbatar cewa Ruwa yashiga har nan.
* Ya zama dole 'yan uwa mata su tabbatar cewa
Ruwan ya ratsa har cikin Kitsonsu yayin wankan.
* Namiji idan yanada gemu, to lallai ne ka tabbatar
cewa ka Tsetsefe shi komai Kaurinsa da duhunsa.
~ ~ ~ ~ ~ ~ ~
NOTE: Zaka iya amfani da wannan alwalar wacce
kayi yayin wankanka.
Indai har baka sake ta'ba al'aurarka ba bayan kayi
alwalar.
HAKA AKE YIN WANKAN JANABA, HAILA, NIFASI,
DA KUMA WANKAN SHIGA MUSULUNCI.
Wallahu A'alam.
Share:

Gyaran gashi

{1}. Danyen ganyen lalle ko na magarya.
{2}.Garin hulba ko tsaba.
{3}. Zaitun laun, wato (man dinya).
{4}. Zaitu sim sim, wato (man ridi)
{5}. Man danyen zaitun.
{6}. Man habbatus sauda.
{7}. Man kwakwa, wato (coconut oil).
YADDA AKE HADAWA
Da farko zaki hada garin hulba da danyen ganyen
lalle kona magarya kisa a tukunya kizuba kofin
ruwa ko pure water uku kisa a wuta ya tafasa ki
sauke lokacin da zaki dora lallen nan da hulba zaki
hada sauran mayukan naki sai kiyi oiling kanki kisa
a leda ki daure zaki barshi a kanki kamar mintuna
15 ki dinga diban ruwan dafaffen lallen nan kina
wanke kanki dashi.
Idan kingama saiki barshi yabushe, kikara oiling
kije ayi maki kitso.
NOTE:
Zaki iyayi sau 2 a wata.
ALLAH YA BAYAR DA SA'A.
Share:

Bambanci tsakanin, Maniyyi, Maziyyi, Waziyyi

BANBANCI TSAKANIN ♣ MANIYYI ♠ MAZIYYI ♣ WADIYYI. A kwai sakonni da dama daga 'Yan uwa da sukayi tambaya (wata tambayarma tafi wata guda) akan banbancin wadannan ruwaye. Hakan yanuna kishinsu ga addini wanda yasa mukayi tunanin sanyawa a fili wadanda basu tambaya bama su amfana. Nadade ina tunanin sawa dan sauwakewa kaina amsa tambayoyi daya bayan daya. Amma inajin NAUYI wajen bada amsa yasa nakasa, yauda aka kumayi mini tambayar naga yadace in sanya tunda. "INNALAAHA LA YASTAHYI MINAL HAQ. Nana A'isha tana cewa: "Allah ya jikan MATAN MADINA kokadan KUNYA bai taba hanasu neman sanin addininsu ba" Idan mukace zamuci gaba dajin nauyin tambaya ko bada amsawa saboda KUNYA to zamu rayu cikin jahilci, wanda wannan ba uzuri bane a wurin Allah. Dan haka ga banbancin dake tsakaninsu: {1}. MANIYYI ========== Maniyyin namiji: ruwane mai kauri FARI wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji. Sannan yana tunkudo juna lokacin dayake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko damammen gari, Idan yabushe yana kamshin kwai. {1A}. MANIYYIN MACE: Ruwane TSINKAKKE, MAI FATSI-FATSI, wani lokacin kuma yana zuwa FARI, wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji. Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, zataji tsananin sha'awa da dadi lokacin fitowarsa. Kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino ko damammen gari, Idan ya bushe shima yana kamshin kwai. Sannan sha'awarta zata yanke bayan fitowarsa. HUKUNCIN FITAR MANIYYI shine: YANA WAJABTA WANKA. {2}. MAZIYYI: ========== Ruwane tsinkakke dayake fitowa, yayin karamar sha'awa, kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce kakeso, ko matarka, ko kallon matar ko namijin da kike sha'awa. Haka kuma yana fitowa yayin wasa tsakanin miji da mata, saidai shi baya tafiyarda sha'awa, kuma wani lokacin ba'a sanin yafito. Malamai suna cewa: Maziyyi yafi fitowa mata, fiye da maza. HUKUNCINSA SHINE: A WANKE FARJI GABA DAYA, DA KUMA INDA YA SHAFA, KUMA A SAKE ALWALA. {3}. WADIYYI ========== Wani ruwane mai KAURI dayake fitowa a karshen fitsari, ko kuma karshen bahaya ga wanda yajima baiyi jima'i ba, yana fitowa ga wadanda basuda aure, ko wadanda sukayi nisa da abokin rayuwarsu ta aure, ina nufin namiji ko mace. YANA DAUKAR HUKUNCE-HUKUNCEN FITSARI. Allah shine mafi sani. NAN GABA KADAN ZAN KUMA BAYANI AKAN YADDA AKE WANKAN HAILA DANA JANABA IDAN ALLAH YASO KUMA YA YARDA.
Share:

Fitar da maniyyi batare da wanka ba.

ASHE AKWAI YANAYIN DA WANI ZAI FITAR DA MANIYYI AMMA BABU WANKA AKANSA SAI DAI YAYI TSARKI KAWAI ??? ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ Assalamu Alaikum. Yau ina dauke da wani jawabi mai ban mamaki. Kamar yadda kowa dai yasani ita janaba duk wanda ya tsinci kansa acikinta to ya wajaba a gareshi da yayi wanka. HANYOYIN DA MUTUM IDAN YA SAMU JANABA ZAI WANKA SUNE KAMAR HAKA: ♦Duk wanda ya sadu da iyalinsa, ko kuma boyewar hashafa [kan kaciya] a cikin farjin mace, to ya wajaba yayi wanka koda kuwa bai fitar da maniyyi ba. ♦ Duk Wanda yayi mafarki kuma yatashi yaga Maniyyi a jikinsa, to ya wajaba akansa yayi wanka, koda kuwa ya bushe. Amma idan ya tashi ya tabbatar bai ga maniyyi ba, to babu wanka akansa. - Wasu kuma zakuga Allah yayi musu karfin sha'awa, mace idan suka gani ko suka shafi jikinta, to zaku ga sun fitar da maniyyi. To shima wannan yanayi wanka za ayi. - A Takaice Wanda duk ya fitar da maniyyi ta hanyar jin dadi kamar tunani, kallo, ko a lokaci da yake waya da budurwarsa [mafi akasari anfi fitar da maziyyi a wannan lokaci, to tsarki kawai za ayi]. Amma idan maniyyi ne to wanka za a yi. HANYOYIN DA ZA'A FITAR DA MANIYYI AMMA MAIMAKON AI WANKA SAI KAWAI AYI TSARKI IRIN NA ALWALA BA WANKA BA. Akwai hanyoyi da dama wadanda idan wani ya tsinci kansa a ciki har yafitar da maniyyi, to wanka bai wajaba akansa ba, sai dai kawai yayi tsarki ya canja tufafi koya wanke wajan janabar. Wadanne hanyoyi ne wadannan ? Sune kamar haka: HAWA KAN DOKI: Duk wanda yahau kan doki, walau yana kilisane ko yana sassarfa koma dai me yake, inda wannan hawa kan dokin ne silar da tasa ya zubar da maniyyi to tsarki kawai zai yi. Babu wanka a kansa. WAHALA: Wanda wahala tasa yazubar da maniyyi shima babu wanka akansa. Misali: Idan mutum yana cikin wani mawuyacin hali ko bashi da lfy wannan radadin wahalar yasa ya zubar da maniyyi, to shima babu wanka akansa, tsarki kawai zaiyi. Haka ma wanda yake dakin jarrabawa sai kawai yaji ya kawo, watakila chajin kwakwalwa ne yai masa yawa harya fitar, to babu wanka akansa. (Zanci Gaba Idan Allah Yaso ya yarda...) TUNATARWA: Bawai dole saita hanyar jin dadi kawai ake zubar da maniyyi ba. Akwai hanyoyi da dama. Domin wahala ma tanasa mutum ya kawo. WALLAHU A'ALAM.
Share:

Hukuncin ganin maniyyi da safe.

HUKUNCIN GANIN MANIYYI DA SAFE.
Assalamu alaikum malam mutum ne yakwanta
barci kuma baiyi mafarkiba amma yatashi yaga
maniyi a jikinsa to ya zaiyi ???
{2}. mutum ne yaje fitsari bayan yagama sai maniyi
yafito to shin yazaiyi ???
Malan Allah yasaka da alkhairy.
(Daga Nazeer Yahaya Hashim).
AMSA
=====
wanka ya wajaba akansa koda baiyi mafarkiba,
indai harya kwanta babu maniyyi a jikinsa sannan
yafarka yaganshi.
Amsar tambaya ta 2.
Wannan wanda yake fitowa bayan fitsari ba maniyyi
bane sunansa wadiyyi yana fitowa ga marasa aure
ko mutumin daya haura shekaru 40 a duniya.
MENENE HUKUNCINSA.
Hukuncinsa daya da fitsari zakayi tsarki idan yafita
kamar yadda kakeyin tsarkin fitsari.
WALLAHU A'ALAM.
Dan Allah kudinga yin share dinsa ta facebook
domin 'yan uwanku su amfana
Share:

Abubuwan da aka haramtawa mai janaba.

ABIN DA AKA HARAMTAWA MAI JANABA YINSA (MAZA DA MATA). Sau da yawa mukan samu kanmu a halin janaba, kuma mu aikata wasu abubuwa da shari'a bata halatta mana ba. Amma yanzu InSha Allah zan sanar da 'yan uwa abubuwan da basu halatta muyi suba a yayin da muke cikin Janaba. 1- Assalat (Sallah) 2- Adawaf (Dawafin dakin Allah) 3- Shafar Alqur'ani Mai Girma ko kuma Daukarsa. 4- Karatun Qur'ani: An haramtawa mai janaba karatun Qur'ani, bai halatta ba a gareshi, saidai wasu malaman suna cewa, zai iya karanta wata aya domin neman tsari. Janhurun Malamai sun hadu akan haka. 5- Shiga Masallaci: Ya haramta akan mai janaba ina mai kafa hujja da hadisin Nana Aisha (R.A) tace: "Manzo (S.A.W) yace: Ku fuskanci wadannan gidajen daga masallaci, domin cewa baya halatta ga mai Haidha da Janaba shiga Masallaci". Abu dawud ya rawaito. An karbo daga Ummu Salmah (R.A) tace: "Annabi (S.A.W) yashiga masallaci, sai yayi magana da murya mai karfi, yai kira da madaukakiyar muryarsa, yace: Hakika masallaci baya halatta ga mai Haidha da kuma mai Janaba." Ibn Maja da Dabari. Allah yasa mugane kuma mu amfana da abin da muke karantawa.
Share:

YADDA AKEYIN SALLAR JANA'IZAH

YADDA AKEYIN SALLAR GAWA. DAN ALLAH KUTSAYA KU KARANTA. Dukkanin Malamai na Mazhabobi sunyi ittifaqi akan cewa SALLAR GAWA (JANAZAH) FARILLAH CE TA KIFAYAH. (wato irin farillar nan wacce wani zai iya daukewa wani). Saidai an ruwaito daga Asbag (daya daga almajiran Imamu Malik) cewar Shi Sunnah ce awajensa. Za'a iya yin Sallar gawa a kowanne Lokaci ko dare ko rana, Inji IMAM SHAFI'IY (R.A). Amma IMAMU AHMAD DA IMAM ABU HANEEFAH (R.A) Sunce: Makruhi ne ayi sallar Janazah a lokutan nan guda Uku. 1. bayan Sallar asubah har zuwa fitowar rana. 2. Bayan sallar la'asar har zuwa faduwar rana.. 3. Lokacin da Limamin Jumu'a yahau kan mimbari yake khudubah. Shi kuwa IMAMU MALIK (R.A) Yace: Za'a iya yin Sallar Janazah a kowanne lokaci in banda lokacin fitowar rana da kuma lokacin faduwarta, yace Makruhi ne. SHARUDANTA: Dukkan Maluman Mazhabobin sunyi ittifaqi akan cewa: Wadannan sune sharudan ingancin Sallar Janazah: Tsarki da alwala. Suturce Al'aurah. * Kallon Alqiblah. Amma Sha'aby da Ibnu Jareer sunce: Za'a iya yi ko ba tareda alwala ba. Imam Shafi'iy da Abu Yusuf sunce Limami yana tsayawane adaidai kan mutum Namiji. Ita kuma mace Liman zai tsayane adaidai tsakiyar ta. Amma IMAMU MALIK DA IMAM ABU HANEEFAH Sunce: Liman zai tsayane adaidai Qirjin Namiji, ita kuma mace zai tsaya ne adaidai adaidai tsakiyarta. KABBARORINTA: Anayin Kabbarori hudu asallar janazah abisa ittifakin Mazhabobin nan hudu. Saidai an ruwaito Kabbara 3 daga Imam Ibnu Sireen. Sannan akwai wata ruwayar daga Abdullahi bn Mas'ud (rta) yace: "Manzon Allah (saww) yayi kabbara 9 abisa Janazah, Sannan yayi 7, Sannan yay 5, Sannan yayi 4. Kuyi ta kabbarawa mutukar Limaminku ya kabbara. Koda ya Qara abisa hudu to sallar bata 'baci ba". Imamush-Shafi'iy yace Zaka cira hannuwanka zuwa kafadunka ayayin dukkan kabbarorin. Amma IMAMU MALIK DA IMAM ABU HANIFAH sunce bazaka cira hannuwanka ba saidai akabbarar farko kawai.. Karanta Fatiha bayan kabbarar farko, Farilla ne awajen Imam Shafi'iy da Imamu Ahmad. Amma Imamu Malik da Abu Haneefa Sunce: BA ZAKA KARANTA KOMAI BA DAGA CIKIN AYOYIN ALQUR'ANI. Sannan anayin Salatun Nabiyyi (saww) sannan kuma sai Addu'a ga mamacin da sauran al'ummar musulmi abayan Kabbara ta biyu data uku da ta hudu respectively. Sannan mutum zaiyi sallama ne guda biyu abisa Mazhabobi uku. Amma Hanbaliyya sunce Sallama daya zakayi a damanka. Aduba Samrud-dany Babin Sallar Janazah da kuma Rahmatul-Ummah shafi na 81. WALLAHU A'ALAM. Allah ya yasa mu cika da imani. www.hanyantsira.mywapblog.com
Share:

ABUBUWAN DA AKE YIWA TSARKI

Abubuwan Da Ake yiwa Tsarki: Anayin tsarkine daga dukkan abin daya fito ta daya daga mafita guda biyu kota duka biyun, amma banda hutu wato (tusa). Ana yiwa ♠ Fitsari. ♠ Bayangida. ♠ Maniyyi. ♠ Maziyyi. ♠ Jinin al'ada. ♠ Tsarki. kawai dai idan mutum yanada alwala sai yayi tusa to alwalar kawai zai sake basai ya dauki buta yayi tsarkiba. Hukuncin Tsarki: Tsarki wajibine, saboda haka dukkan wanda dayan wadancan abubuwa da makamantansu suka sameshi to dole ya tabbata ya gabatar dayin tsarki. Darasi mai zuwa zanyi bayani akan rabe-raben tsarki. Insha Allah.
Share:

Ladabin shiga bandaki (4).

(12) Nisa Da Jama'a: Ana bukatar dukkan wanda zaiyi bayan gida yayi nesa da jama'a ta yadda ba zasu ganshiba kuma baza suji nishin saba, bazai yi kyauba ace kana bayan gida mutane suna ganinka ko suna jin nishinka, koda a bayan bishiya ko ganyan kargo sai ka boye, amma sau da yawa mutane suna tafiya a mota da motar ta tsaya sai kaga kowa ya tsaya dab da motar, sannan ba za'a tafi a barshiba. (13) Kada Ya Fuskanci Alkibla: Wato inda mutum yake kallo lokacin sallah, kuma kada ya juya mata baya, wannan idan a dajine, amma idan a gidane to da sauki. Darasi mai zuwa zanci gaba. Insha Allah.
Share:

Ladabin shiga bandaki (4).

(12) Nisa Da Jama'a:
Ana bukatar dukkan wanda zaiyi bayan gida yayi
nesa da jama'a ta yadda ba zasu ganshiba kuma
baza suji nishin saba, bazai yi kyauba ace kana
bayan gida mutane suna ganinka ko suna jin
nishinka, koda a bayan bishiya ko ganyan kargo
sai ka boye, amma sau da yawa mutane suna
tafiya a mota da motar ta tsaya sai kaga kowa ya
tsaya dab da motar, sannan ba za'a tafi a
barshiba.
(13) Kada Ya Fuskanci Alkibla:
Wato inda mutum yake kallo lokacin sallah, kuma
kada ya juya mata baya, wannan idan a dajine,
amma idan a gidane to da sauki.
Darasi mai zuwa zanci gaba.
Insha Allah.
Share:

Ladabin shiga bandaki (3).

(8) Yarufe Kansa:
Anason wanda yake bayan gida yarufe kansa a
daidai lokacin da yakeyi.
Domin koda wani yayi kuskuren ganinsa toshi bai
ganshiba, abin zaizo da sauki, amma ba zakaji
dadiba kana bayan gida kahada ido da wani, wanda
zai iya zama dalibinka ne ko suruki ko da'.
(8) Kada Ayi Magana:
Anhana mutum yana bayan gida yana Magana,
saidai idan akwai dalili mai kwari.
Kamar kaga makaho ya nufi rijiya ko karamin yaro.
(9) Kada A Tari Iska:
An hana idan mutum zaiyi bayan gida a (daji)
yatari iska, domin zai busowa jama'a warin bayan
gidansa, sai yayi nesa, ya kuma duba ina iska take
kadawa.
(10) Kaucewa Rami:
Ba'a yarda idan zakayi fitsari ko bayan gida kayi a
ramiba saidai idan kaika haqashi, domin bakasan
menene yake cikin ramin ba, takan yiwu akwai
mugun abu.
(11) Kaucewa Wuraren Tsinuwa:
Wadannan wurare sune wuraran da mutane suke
yawan tsinema dukkan wanda yayi musu
bayangida a wurin, wadannan wurare sune:
(a) Inda mutane suke zama su huta, jikin bangone
ko karkashin bishiya komadai inane.
(b)Kan hanya:
Akwai rashin mutunci mutum yazo kan hanya ya
gicciya bayangida, wannan dabi'a musulunci bai
yarda da ita ba.
(c) Mashayar ruwa:
Hakanan baya cikin karantarwar musulunci mutum
yazo inda al'umma suke diban ruwa rafine ko wani
gulbi ko gindin fanfo koma dai inane ya aikata
wannan ta'asa.
Wadannan wurare uku musulunci ya hana a aikata
wannan danyan aiki a wurin, domin mutum yana
jawa kansa tsinuwa.
Allah ya tsaremu.
Sai darasi mai zuwa zanci gaba daga yadda muka
tsaya.
Insha Allah.
Share:

Ladabin shiga bandaki (2).

(4) Tabbatuwa ACikin Sutura:
Ana bukatar kada mutum ya yaye al'aurar sa tun
yana tsaye, sai ya tsugunna yayi dab da kasa saiya
daga suturarsa, domin ba'a yarda wani yaga
al'aurar waniba, idan ba miji da mataba, amma
halin ko inkula da wasu ke nunawa na bayyanar
da al'aurarsu ga kowa muddin jinsi gudane
wannan bai daceba, sai kaji wani yace' Ai duka
mazane, abinda kake dashi ina dashi, wannan ba
koyarwar musulunci bace.
Hakanan mata, wannan zai kaika kaga maza sun
tube suna wanka lokaci guda a dakin wanka guda,
haka namma mata, wai sun dauka abinda yake
haram shine namiji yaga al'aurar mace ko mace
taga al'aurar namiji.
Kai wani lokaci kana tafiya a cikin mota sai kayi
arba da wani gabjejen kato yana wanka a rafi, wani
kuma a gefan titi yakafe mashin ko ya ajiye kayan
tallansa.
Duk wadannan ba kyawawan halaye bane, mutum
musulmi ya nisance su.
(5) Yafi Bada Karfi A Kafarsa Ta Hagu:
Abinda a kafiso shine mutum yafi bayar da karfinsa
akan kafarsa ta hagu.
(6) Sannan Yabude Tsakanin Cinyoyinsa:
Kada ya matse, ballantana yasa matsattsiyar tufa
wacce idan yana fitsari na gaban ne kawai zai fita,
sannan idan ya mayar cikin wando sauran ya
gangaro.
Allah ya sawwake.
(7) Ya Nisanci Inda Ruwa Yake:
Musulunci bai yadda mutun yayi fitsari ko bayan
gida a inda ruwa yakeba ko kusa dashi, dan
wannan zai haifar da cututtuka.
Darasi mai zuwa zanci gaba daga yadda muka
tsaya.
Insha Allah.
Allah yasa muna aiki da abinda muke karantawa.
Share:

Ladabin shiga bandaki (1).

Ladubban Shiga Bandaki (Fitsari Ko Bayangida):
Akwai tsari na ladubba da musulunci yake dasu a
lokacin da mutum yake niyyar kewayawa.
Wannan zai nuna maka cewa addinin musulunci ya
karade komai:
(1) Anbaton Allah:
Ana bukatar kafin kashiga ka ambaci Allah domin
ba'a anbaton Allah a makewayi, kuma kanemi Allah
ya tsareka daga sharrin aljanu, domin irin
wadannan wurare matattarace tasu.
Sai ya karanta wannan addu'a yace:
ﺑِﺴْﻢِ ﺍَﻟﻠﻪِ، ﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻲ ﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﻚَ ﻣِﻦَ ﺍَﻟْﺨُﺒُﺚِ ﻭَﺍﻟْﺨَﺒَﺎﺋِﺚِ
Ma'ana
Da sunan Allah, Ya Allah lalle ni ina neman
tsarinka (Daka tsareni) daga aljanu maza da kuma
aljanu mata.
Idan kuma zaka fito sai kace:
ﻏُﻔْﺮَﺍﻧَﻚَ، ﺍَﻟْﺤَﻤْﺪُ ﻟﻠﻪِ ﺍَﻟَّﺬِﻱ ﺃَﺫْﻫَﺐَ ﻋَﻨِّﻲ ﺍَﻷَﺫَﻯ ﻭَﻋَﺎﻓَﺎﻧِﻲ
Ma'ana:
Ina neman) gafararka Allah, Dukkan godiya ta
tabbata gareka, wanda ya rabani da wannan
kazantar kuma ya bani lafiya.
Kusani ba'a shiga bayi da dukkan wani abu da
yake dauke da sunan Allah, kamar zobe, ko carbi.
Hakanan kuma ba'a katse bayangida da dukkan
wani abu da yake da sunan Allah.
(2) Fara Gabatar Da Kafar Hagu A Lokacin Shiga.
kafar dama kuma lokacin fitowa.
(3) Ayi A Tsugunne:
kada mutum yayi fitsari ko bayan gida a tsaye, sai
dai idan wurin kangone ko yana tsoron fitsarin ya
fallatso masa, sannan ba wanda zai ganshi.
Darasi mai zuwa zanci gaba daga yadda muka
tsaya.
Insha Allah.
Share:

About MUHAMMAD ABBA GANA

Placeholder for About Me page of MUHAMMAD ABBA GANA
Share:

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate