DAGA ZAUREN
HANYAN***TSIRA
YAUSHE NE LOKACIN BUDA BAKI (SHAN RUWA).
AMSA
-------------------------------------
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
Buda baki yana tabbatane da zarar anga rana tafadi koda mutum yayi buda baki ko bai yiba.Dalili kuwa shine:Hadisin Abdullahi Ibn Awfa yace:Mun kasance cikin tafiya tareda Manzon Allah {S.A.W} alhalin cewa yana azumi.Yayin da rana tafadi sai yacewa wani daga cikin sashen sahabbansa yakai wane ka tashi ka shirya mana abin buda baki (farau-farau) sai yace:Ya Manzon Allah inama ace mun kara yammata (shi yana kokwanton faduwar rana ne).Sai yace ka sauka ka shirya mana abin buda baki.Sai yace ya Manzon Allah ina ma mun kara
yammata.Sai yace ka sauka ka shirya mana abin buda baki.Sai yace ya Manzon Allah ai akwai sauran rana sai yace ka sauka ka shirya mana abin buda baki.Sai ya sauka ya shirya musu sai Annabi {S.A.W.}
yasha ruwa sannan yace:Idan kuka ga dare ya gabato daganan hakika mai azumi yabude baki (ana nufin ko yasha ruwa, ko bai shaba).(Bukhari 1958 Kitabus-siyam)kuma ya tabbata acikin Bukhari daga Sahal ibn
Sa'ad Yace:Hakika Manzon Allah (S.A.W.) yace:Mutane baza su gushe cikin Alkhairi ba, matukar suna gaggauta bude baki.
Amma abin mamaki a yanzu sai kaga mutane
sunyi salla basu sha ruwa ba.ko kuma su bari harsai taurari sun bayyana,sannan suyi buda baki, tsammanin su yin haka shine dai-dai, alhali yin hakan ya sabama sunna kamar yadda ya tabbata a hadisin daya gabata.
www.hanyantsira.mywapblog.com
09039016969
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
No comments:
Post a Comment