Maganin mai hassada
DAGA ZAUREN
HANYAN***TSIRA
Akaramakallah, inada wani aboki na kud-da-kud,saidai bayaso yaga nafishi da wani abu, idan na samu wani abin alkairi, saiya aibanta abin ta yadda
mutane bazasu kimanta shiba, abin yana damuna,shine nakeso a taimaka min da hanyoyin da zan samu kariya daga mahassada ?
(Daga Salihu Ahmad).
AMSA
--------------------
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
To dan’uwa, ya kamata kasan cewa babu yadda zakayi ka wofantu daga mahassada, domin duk wanda Allah yayi masa ni’ima, dole sai yasamu mahassada, saidai duk da haka akwai hanyoyin da
malamai suka fada wadanda suke hana hassadar yin tasiri gasu kamar haka:
1. Neman tsari awajen Allah daga sharrinsa.
2. Tsoron Allah da kiyaye umarninsa, duk wanda ya kiyaye Allah, to Allah zai kiyaye shi.
3. Yin hakuri akan abokin gabansa, kar yace zai rama mummunan abinda yayi masa, domin inhar bai rama abinda akayi masa ba, to tabbas Allah zai rama masa.
4. Karfin dogaro zuwa ga Allah, Allah yana cewa a cikin (Suratu Addalak Ayah ta 3) cewa:“Duk wanda ya dogara ga Allah, to ya ishe shi”.Idan ka dogara ga Allah sharrin mahassadi bazai cutar da kai ba, ko da kuwa ka ga wani abu da yake na cutarwa ne to karshensa zai zama alkairi.
5. Fuskantar Allah Madaukakin Sarki da tsarkake aiki zuwa gare Shi, da yawan ambatonSa.
6. Tuba daga zunubai, domin ba za’a dora maka wani yadinga cutar da kai ba, sai idan akwai wani
zunubi daka aikata, kasan zunubin ko bakasan shiba.
7. Yin sadaka da kyautatawa iya abinda zai iya,saboda da wuya Allah yadora mai hassada akan wanda yake kyautatawa mutane.
8. Kyautatawa wanda yakeyi maka hassadar, saidai wannan yana da tsananin wahala.Idan har ka kiyaye wadannan Allah zai taimaka maka.
Don neman karin bayani kuduba:
(Bada’iul fawa’id na Ibn Qayyim, 2\463).
Allah ka rabamu da rigar hassada.
www.hanyantsira.mywapblog.com
whatsapp
09039016969
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Home »
» Maganin mai hassada
No comments:
Post a Comment