Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

LABARIN WANI MAZINACI

kissa.jpgLABARIN WANI MAZINA CI

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

A daure a karanta akwai darasi babba


ZINA BASHI CE!'Yan uwana Maza da Mata akwai wata Qissa da zan Bamu, mai matu'kar amfani acikin wannan zamanin namu, ma'abocin Qissar, wanda abin yafaru dashi,shine yake bayar da Labarin yadda al'amarin ya kansace dashi.Labarin yana cikin wata Mujallah (Magazine News
paper) ta 'kasashen Larabawa, kuma cikin harshen Larabcine, amma zanyi 'kokari wajen fassarawa gwargwadon yadda
na fahimta, saboda nima din ba gwani bane a harshen Larabci.gata kamar haka.......

Mutumin yana cewa:
A lokacin da ina saurayina nasami Admission a Jami'a, bayan nafara karatunne sai na had'u da wata Budurwa (Girl-friend) acikin Jami'ar tamu muka 'kulla soyayya da ita tamkar ma'aurata, hardai tasami juna biyu, (yai mata ciki kenan).Da iyayenta suka gane sai suka tambayeta wanda yayi mata ciki sai tace nine nayi mata.Sai yayanta yataho nema na a fusace yana nufin
d'aukar mataki a kaina, yana zuwa saiya tambayeni kaine kayima qanwata ciki ko ???Sai na amsa masa da cewa:
Wace ce, ni banma ta6a ganinta ba a Rayuwata,ban santa ba.Sakamakon rashin hujjar da zasu kamani da ita dole suka 'kyaleni.Bayan tsawon zamani, wata rana nadawo gida saina tarar da Mahaifiyata a dur'kushe tana tana
kuka.Saina dur Qusa na daga ta sai tasake yanke jiki tafad'i 'kasa har sau uku saina tambayeta a karo
na qarshe:"Ya Ummi Man ladzhi haddath (me ya faru mama)?
Sai tace:Qanwarkace gata can wani yayi mata ciki!Yace sai naji kamar an sokeni da mashi, hankalina yatashi na tasa 'keyarta muka tafi wurin wanda tace yai mata cikin.Da mukaje sai yafada min maganar data tayarmin da hankali.
Bawata magana bace face wadda na fadama yayan yarinyar da nayi
ma ciki a baya.(Ban santa ba, banma ta6a ganinta ba)!Bayan zamani yaqara yin nisa sai nayi nufin yin
aure nafara neman aure nasamu matar da nake so kuma akasa lokaci akayi biki, ranar farko dana tare da ita saina sameta ba a matsayin budurwa ba.
Ma'ana tariga tayi zina, tuni hankalina yatashi.Saita fadamin wata magana mai shiga rai."Don Allah karufa min asiri, ka suturta al'amarina
kaima Allah sai ya suturta al'amarinka."
Yace sai nace acikin zuciyata:Ya Rabby yakfy, yakfy.(Ma-ana Ya Mahalliccina ya isa haka ya isa haka).•Ya cigaba da cewa:Bayan mun kwashe shekaru da matata sai muka
haifi 'ya mace kyakkyawa gata da haske kamar
wata.A lokacin da tacika shekaru 6 a duniya sai gata wata rana tashigo gida tana kuka.Me yafaru ?
Ai me gadine yayi mata fyad'e!INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN
Aljazaa'u min jinsil amal!Wallahi duk tsiyar da kake sheqewa idan Allah
ta'ala yaga dama sai ya hada maka zafi kan zafi irin wannan!Yanzu kunga shi ya lalata 'yar mutane guda daya
tak shi kuma an lalata masa guda uku! Yaa Allah ka Qara karemu daga zina, masuyi kuma Allah ka shiryasu.

www.hanyantsira.mywapblog.com


whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate

Blog Archive