Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

KAYI SHAWARA DA KANKA, SHIMA BA KARAMAR DABARA BACE-

tunatarwa.jpgKAYI SHAWARA DA KANKA, SHIMA BA
KARAMAR DABARA BACE-

01


DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .


Bazan taba mantawa da lokacin da ina dan
shekara 8 a duniya ba, na kanyi tunanin duniya tawace, a lokacin da nakai shekara 15, sai na fara
tunanin ya zan in mulki duniya nima na zama daya daga cikin muhimman mutanenta. Sanda nakai shekaru 20, sai na fara tunanin ya zan zama babban attajiri a duniya na mallaki ababen 'kawa nima kamar kowane mai sukuni. Lokacin dana cika dan shekaru 25, sai na fara tunanin samun soyayyar mutane. Dana kai shekaru 40 a duniya
sai na fra tunanin neman taimakon al'umma.Tabbas nasan akwana atashi wata rana sai na
bukaci mutuwa da kaina muddin shekaru sun ja.Idan zaku lura da kyau, a duk tsawon wadannan shekaru na karar da sune akan son mallakar abubuwa da dama a lokuta maban-banta. Amma
abinda nafiso shine na zamo cikin farin ciki. Amma babu shakka ina tunanin mafi alherin hanyar
cimma buri a rayuwa shine sauraron shawarar
mutane.
Wannan yasa alokacin da zan shiga jami'a naso
ace na karanta fannin koyon malumta wato
(Education) don in son nan gaba na zama
kwararren malamin makaranta, amma a lokaci daya
mutane sukayo mini caaa! Me zanyi da wata
koyarwa, in karanci Engineering ko medicine, sune
kwasa-kwasai na rayuwa masu ci. Na dauki
shawararsu na zabi Engineering. Bayan
kasancewata a jami'a, na kasa samun tallafin
karatu daga kowane daya daga cikinsu, matsalolin
rayuwa suka rufar ma karatu na, dole tasa na gudu
daga jami'a saboda karatun bazai yiwwu ba.
Bayan na bar jami'a...... Mu hadu a 02

www.hanyantsira.mywapblog.com


whatsapp
09039016969



Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate

Blog Archive