DAGA ZAUREN
HANYAN***TSIRA
TAMBAYA ???
SU WANENE AZUMI YA WAJABTA A GARESU ???
AMSA
-----------------------------
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
Azumin Ramadan ya wajabta akan dukkan Musulmi baligi mai hankali kuma wanda yake da ikon yi,sannan mazaunin gida ba matafiyaba.Amma azumi baya wajaba akan wadannan mutane kamar haka:
Kafiri:
Azumi baya wajaba akansa, hakanan ramuwa bata wajaba a kansa idan ya musulunta a gaba.
Karamin Yaro wanda bai balagaba.
Amma za'a umarceshi domin ya saba kamar yadda magabata suke yiwa yayansu.
Mahaukaci:
Azumi bai wajaba a kansa ba.Dalili kuwa shine:Manzon Allah yace an dauke alkalami akan mutum
uku wanda mahaukaci da yaro na cikin mutum
ukun daya ambata, saboda haka idan mahaukaci sai yarama azumi to yaro ma kenan zai rama
azumin da yasha idan ya balaga.Hakanan mai bacci da yayi jimaI saboda haka
malaman da sukace mahaukaci yarama azumi basu da wata madogara daga Alkuani ko maganar
Manzon Allah (S.A.W.).
Wanda ya gaza yin azumi saboda tsufa zai sha azumi kuma bazai rama ba sai dai zai ciyar.
Mara lafiya wanda bazai iya azumi ba to shi zai rama bayan ya warke.Amma cutar da ake tabbatar bazata warke ba, to wannan ma zai rika ciyarwa.
Matafiyi:Azumi bai wajaba a kansa ba amma zai rama.
Mai haila ko jinin biki:Baza suyi azumi ba, amma zasu rama.
Allah shine mafi sani.
www.hanyantsira.mywapblog.com
09039016969
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
No comments:
Post a Comment