Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

ABUBUWAN DA SUKA HALATTA GAME AZUMI

ABUBUWAN DA SUKA HALATTA GAME AZUMI.


DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .


ABUBUWAN DA SUKA HALATTA GAME AZUMI.

1.Shiga cikin Ruwa dayin nitso aciki domin sanyaya jiki saboda tsananin zafi.
Domin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam, ya
kasance:"Yana zuba ruwa akansa, yana me Azumi saboda kishirwa ko saboda Zafi"(Ahmad da Abu Dawud).

2. Yawayi gari yanada janaba a jikinsa, ya halatta,Saboda fadin Nana A'isha Allah yakara mata yarda
tace:"Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.Ya kasance yana wayar gari da janba yana mai Azumi sannan yayi wanka"Bukhari da muslim).Wato acikin Azumin Ramadan.

3. Ci da Sha da Jima'i cikin dare har zuwa lakacin fitowar alfijir.
Saboda fadin Ma'aiki Sallallahu AlaihiWasallam:
"Lallai Bilal yana kiran Sallah da dare, to kuci
kusha harsai dan umm maktum yayi kiran sallah"Bukhari da muslim).Wato bilal nayin kira na farko shikuma yanayin kira
na biyu.

4. Me jinin Haila da me jinin Biki.Idan jinin ya yanke mata cikin dare ya halatta su jinkirta wankan har zuwa Asubahi, kuma su wayi
gari da Azuminsu sannan suyi wanka kafin suyi Sallah.

5. Yin Aswaki a farkon Yini da karshensa. Saboda cin Aswaki mustabbine kuma babu wani dalili da yanuna cewa za'ayi shi a wani lokaci banda wani, wannan shine mazhabin mafi yawan malamai.

6. Yin magani kowane Iri matukar bazai tafi cikinsa ba kamar yin allura wacce bata abinci bace.

8. Tauna abinci da dandanashi da sharadin babu abinda zewuce ciki.

9. Yin amfani da turare da Shakar kamshi mai
dadi.
Allah yasa mu daxe



www.hanyantsira.mywapblog.com


whatsapp
09039016969y
07038774163


Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA


Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww)yace:"WALLAHI IDAN ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate

Blog Archive