Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

kallon film ga ma,aurata

kallon film ga ma,aurata

 Kallon Blue film ga ma'aurata DAGA ZAUREN HANYAN***TSIRA Slm Malam dan.ALLAH yahalatta mutumin da yake da aure yaringa kallon BLUE FILM shida matarsa ? AMSA ========================== ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ . A'a bai halattaba, yin hakan haramunne, Allah (s.w.t) ya tsinewa mai kallon tsiraici da wanda yake nunuwa. Akwai zunubi mai tarin girma, domin gudun kada mutum yafada zina yasa yayi aure, idan akace mutum yayi aure baya samun biyan bukata da matarsa ta sunnah dole saiya kalli kafirai maqiya Allah da Manzonsa suna tafka masha'a suna aikata zuna a fili yazama auren nasa bai katangeshi daga zina ba kenan. Duk ma'auratan da suka sabarwa kansu da irin wannan muguwar dabi'ar tunda wuri sudaina. Bazasu ta6a samun biyan bukata ta wannan hanyar ba. ABIN DAYA KAMATA SUYI SHINE: ================= matsayinsu na ma'aurata su cire kunya su zauna su tattauna tsakaninsu, akan shi mai gidan ko ita uwar gidan wanne abu yafiso ko wanne abu tafiso tayi masa ko yayi mata a lokacin kwanciyarsu ta aure ??? Wannan shine matakin daza su dauka amma maganar kallon B.f haramunne Allah (s.w.t) yana fushi da ma'auratan da basa kishin junansu. Da fatan ma'aurata zasu kiyaye. Allah ka aurar da matasanmu maza da mata su huta da wannan bala'in albarkacin Muhammadu Rasulullah (s.a.w). Dan Allah kudinga yin share dinsa ta facebook da kuma whatsapp domin 'yan uwanku su amfana. www.hanyantsira.blogspot.com whatsapp 09039016969 Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/ وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

darasi na 9

darasi na 9

Darasi na 9 DAGA ZAUREN HANYAN***TSIRA ***{Darasi na 9}*** Hukunce Hukuncen Azumi. Malam yace: ........... ﻭﺍﻟﺼﻴﺎ ﻡ .......... Ma'ana: Da (sanin hukunce hukuncen) Azumi. BAYANI: Wajibine akan duk wani mukallaf mai hankali yasan hukuncin Azumi, wadannan kuwa sune: 1- Sharudan Azumi. 2- Rukunan Azumi. 3- Abubuwan da suke vata Azumi. 4- Abubuwan da aka karhantawa mai Azumi. 5- Sunnonin Azumi. Duk wadan nan ya kamata mai azumi yasansu. kuma Insha Allah zamuyi bayaninsu daya bayan daya. Musani Azumi yana daga cikin manya-manyan ayyukan da ake bautawa Allah (S.W.T). Saboda girmansa nema Ubangiji madaukakin sarki yake cewa: Azumi nawa ne acikin hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito cewa: "DUK WANI AIKIN DA DAN ADAM YA AIKATA WANNAN NASANE SAI DAI AZUMI SHI WANNAN NAWANE, NINE KUMA NAKE YIN SAKAYYA IDAN ANYISHI". Saboda girmansa da Albarkar dake cikinsa ne yasa Sahabbai idan yakusa qarewa suke kuka kuma suke fatan Allah ya nuna musu wani. Allah yanuna mana wannan wata lafiya yabamu ikon azumtarsa. Yasa muna cikin wadanda za'a 'yanta a cikinsa. Darasi nagaba zanci gaba. INSHA ALLAH. www.hanyantsira.blogspot.com whatsapp 09039016969 Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/ Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

tambaya


MENENE HUKUNCIN MACEN DA TAYI AURE KAFIN TAYI ISTIBRA'I ??? DAGA ZAUREN HANYAN***TSIRA Salam Malam Ya kamata ace nayi istibra’i kafin nayi aure, amma banyiba, har nayi aure, yanzu haka ina jini na farko banyi tsarki ba, amma bada wanda na aikata laifin cikin nayi aure ba. Yaya ingancin aure na? Gani nake kamar babu auren ko ? (Dan Allah ka6oye sunana) AMSA ========================== ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ . DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI. Da farko dai inayi miki wasici da tsoron Allah, saboda zunubin da kika aikata na zina, amma gameda aure, shi aurenki yayi, saidai yinsa bayan istibra’i shine yafi alkhairy, sannan ya wajaba mutukar kinsan kinada ciki to bai halatta kibawa sabon mijinki dama ya take kiba ma'ana ya sadu dake. Saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi: “Duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa”. (Abu-Dawud: hadisi mai lamba 1847). Don haka, ya wajabta a gareki kiyi stibra’i kafin mijinki yasadu dake, sannan istibra’i jini dayane, idan kuma har kin dauki ciki, kafin kiyi istibra’i, in kin haihu kafin wata shida to ba ‘dansa bane, amma in har kin haihu bayan wata shida (6) daga fara saduwarku, to ‘dansa ne, mutukar ba’a samu shaidar da take nuna kinada ciki ba, tun kafinku fara saduwar. WALLAHU A'ALAM DoMIn neman Karin bayani kuduba: (Al-mugny na Ibnu Qudaamah, mujallady na 8\79). www.hanyantsira.blogspot.com whatsapp 09039016969 Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/ Domin samun shafinmu a whatsapp seku dannah wannan, https://chat.whatsapp.com/2AKME7ArAoc5mbmV0dDkWe وسلم عليكم ورحمت وبركاته
Share:

hakkin wanda yaki amsa sallama

hakkin wanda yaki amsa sallama

Hukuncin wanda yaki amsa sallama. DAGA ZAUREN HANYAN***TSIRA Menene hukuncin wanda akayi masa sallama amma yaqi amsawa, kodai saboda girman kai ko kuma saboda wani dalili ??? (Daga Hafiz Ibrahim). AMSA: ===================== ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ . DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI. kada kadamu kaida kayi masa sallamar bakayi asara ba. Aduk lokacin da kayiwa mutum sallama, idan ya amsa kana da lada yana da lada, idan kuwa yaqi amsawa wadanda suka fishi daraja da mutunci (mala'ikun rahama) sun amsa maka. Akwai wanda za'a yiwa gaisuwa 'Assalamu Alaikum'. Yaqi amsawa, saboda shi (yana ganin) ba dama ne, yana jijji da kansa, ko kuma wanda za'a gaishe shi saboda wani banbanci na aqida, shi bai yarda da imanin kaba. Don haka sai yaqi amsawa. Kaga wannan kuwa jahilci ne yake kawo haka. Wannan ba dabi'a bace ta "Ahlus Sunnah". Don haka idan kayi masa sallama ya amsa kai dashi kunyi tarayya cikin lada, in yaqi amsawa kuwa to, wannan shine yayi asara, kai kam bakayi asara ba. Sannan mala'ikun rahma sun amsa maka, Kamar yadda hadisai da sunnah suka koyar. WALLAHU A'ALAM. Allah yabamu ikon gyarawa. www.hanyantsira.blogspot.com whatsapp 09039016969 Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/ وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

tambaya

tambaya

Malam wai da gaskene kowane musulmi sai yashiga wuta ?

DAGA  ZAUREN

HANYAN***TSIRA

                      tambaya

Malam wai da gaskene cewar, kowa sai ya dandana wutar lahira, banda Annabi Muhammad (S.A.W.) ?

(Daga Dahiru Adam).

AMSA:
*******************************

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI. A’a cewa akayi “WADDUHA” ba cewa akayi “MUTHEEQUHA”ba.
Watau kowa sai yabi takan wuta sannan ya wuce. Domin Siradi, akan wuta aka dorashi, mutanen da aka yiwa hisabi zuwa Aljanna sai sunbi takan Siradin. Wanda yake a kan wuta. Shine (acikin Alkur’ani) akace: “WA-IN-MINKUM-ILLA-WARIDUHA KAN-
ALARABBUKA HATMAN MANKIYYA.
Suratul Maryam. Amma kuma jin zafinta (wutar) sai wanda Allah ya nufa da yaji zafin nata, sannan yaji zafin.
Allah ka tseratar damu daga azabar wuta.
WALLAHU A'ALAM.

www.hanyantsira.blogspot.com


whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

Darasi na 8


Darasi na 8

DAGA  ZAUREN

HANYAN***TSIRA


*****{Darasi na 8}*****

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

MUHIMMANCIN TSARKI.

MALAM YACE:
... ﻭﺍﻟﻄﻬﺎﺭﺓ ...
WAD-DAHARATU
Ma'ana: Da (hukunce hukuncen) tsarki".
BAYANI: Yazama wajibi wato dolene duk wani baligi mai hankali yasan hukuncin tsarki gaba daya, domin tsarki dashi akeyin.

♣Sallah.
♣Azumi
♣Dawafi da sauransu.

Allah madaukakin sarki yana cewa a suratu Baqra ayata 221 wato:
ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺤﺐ ﺍﻟﺘﻮﺍﺑﻴﻦ ﻭﻳﺤﺐ ﺍﻟﻤﺘﻄﻬﺮﻳﻦ
Ma'ana:
"HAQIQA ALLAH YANA SON MASU YAWAN TUBA,SANNANYANA SON MASU YAWAN TSARKI"
Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: "Allah bazai karvi sallar da ba'ayi tsarkiba. Awani hadisin kuma yace:
Babu sallah ga wanda bashi da Alwala.
Awani hadisin kuma yace: Wanda yayi sallah batare da Alwalaba, kuma ya gasgata hakan to shi kafirine. Kunga sallah bata yiwuwa saida tsarki abin tsoratarwar kuma shine: Manzon Allah (S.A.W) yace:
"Banbancin Musulmi da kafiri sallah" Wani hadisin kuma yace:
"Sallah itace ginshiqin Addini, wanda ya tsayar da ita, to ya tsayar da addininsa.
Wanda kuma yabarta to yabar addininsa.
Wani hadisin yace:
Farkon abinda za'a fara tambayar mutum bayan mutuwa shine sallah. Idan ta gyaru komai ya gyaru. Idan kuma ta 6aci komai ya 6aci.Gashi ita kuma Sallar ba'a karvarta saida tsarki. Ya Allah ka tsarkakemu da imaninmu. Sai gobe kuma idan Allah yakaimu lokaci kamar
wannan zamuci gaba.
Insha Allah.

www.hanyantsira.blogspot.com


whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate