Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

MENENE MAFIFICIN AIKIN DA MAI AZUMI ZAI DINGA YI ???

MENENE MAFIFICIN AIKIN DA MAI AZUMI ZAI
DINGA YI ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .


MENENE MAFIFICIN AIKIN DA MAI AZUMI ZAI DINGA YI ???

AMSA
-----
Aikin da yafi falala ga mai azumi shine

1. Karatun Al'Qurani.
Ma'ana ya lazimce shi dare da rana, kuma yadinga izna da abin da yake karantawa.
Amma idan bazai iya karatun Al-Qurani ba, to sai ya rinka lazimtar inda ake karatun Al-qur'anin ko fassarashi domin hadisi ya tabbata daga nana
Fadima 'yar Manzon Allah da Abu Huraira yardar Allah ta tabbata a garesu sunce: "Mala'ika Jibrilu ya kasance yana bijirowa da Annabi (S.A.W) Al'Kurani sau daya a kowace shekara, sai ya bijiro masa dashi sau biyu a shekarar da zaiyi wafati.Bukhari da Muslim ne suka ruwaito (1).
____________________________________
(1) Bukhari K=66, Book=7, Hadith=4998 da Muslim
K=44,
B= 15, Hadith=2450.
Wannan yana nuna cewa karatun Al-qur'ani shine
mafificin ibada a cikin watan Ramadhan.
Allah madaukakin Sarki yace:
"Lallai mun saukar dashi a daren Lailatul Kadari.
2. Kyauta:
Ya kamata mai Azumi ya yawaita kyauta wajen
ciyar da jama'a, da sadaka, da taimakon gajiyayyu
da makusanta.
Kamar yadda ya tabbata a hadisin ibn Abbas cewa:"Annabi (S.A.W.) yafi kowa kyauta, kuma mafi
alkhairinsa yana yinsa ne a ramadhan yayin da yake saduwa da Jibrilu.Kuma ibn Abbas (R.A) yace:
Alkhairin Manzon Allah (S.A.W) yafi sakakkiyar
iska".Bukhari ne ya ruwaito shi (2).
(1) Suratul Kadari Aya1 (2) Bukhari K = 1, B = 5, da
Muslim K = 43, B = 12, H = 2308.
Nafil-fili:
Anaso mai Azumi ya yawaita Nafil Fili musamman
kiyamul laili
Saboda hadisin Abu Hurairah yardar Allah ta kara
tabbata a gareshi yace:Manzon Allah (S.A.W) yace:
"Duk wanda yatsaya kiyamulaili yana mai imani, da neman lada; an gafarta masa zunubansa da suka
gabata".
Bukhari ne ya ruwaito shi(1).
Haka kuma Manzon Allah (S.A.W) yace:
Wanda yayi sallah dare tare da liman har yagama
za'a rubuta masa ladan kiyamullaili.h
Kuma anfison duk wanda zaiyi kiyamullaili ya
tsawaita tsayuwar saboda hadisin Khuzaifa (R.A)
Targib Wattarhib wanda Albani yayiwa tahkiki lambar (1078).
"Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana tsawaita
karatu a sallar dare a watan Ramadhan fiye da sauran sallolin dare, yace:Manzon Allah (S.A.W) yakan karanta Suratul Bakarah da Nisa'I da Ali'Imran a raka'a daya, kuma
baya wuce ayar da akayi tsoratarwa a cikin ta sai ya tsaya ya roki Ubangiji tsari.
Kuma bai gama raka'a biyu ba sai ga Bilalu (R.A)yazo yana neman izni ayi sallar Asuba.
Ahmad ya ruwaito wannan hadisin kuma ya ingantashi.
4. Yawan Zikiri da Salatin Annabi (S.A.W):
Abune mai matukar falala mutum ya yawaita Zikiri
da Salati ga Shugaban Halitta irin wanda ya
tabbata daga bakin Manzon Allah (S.A.W).
5. Ciyar da mai Azumi abin Buda baki:
Yana daga cikin mafificiyar ibada mutum yayi
kokari wajen bawa dan uwansa abin Bude baki
saboda hadisin da Annabi
(S.A. W) yake cewa:
"Duk wanda yaciyar da mai Azumi abinda zaiyi bude baki yana da kwatan kwacin ladan wanda ya ciyar batare da an rage ladan wanda ya ciyar ba".Tirmizi yace wannan hadisine hasanun sahih.
6. Umrah:
Yin umrah acikin watan ramadhan ga wanda Allah
ya bashi iko yana daga cikin Aiyukan da ake
kwadaitar da mai Azumi yayi.
Amma duk da haka bai kamata mutum yatafi
umrah yabar makwabtansa da danginsa da sauran
mabukata a cikin yunwa da halin kakani kayi ba.
Kuma ya kamata mu fahimci cewa, ciyarwa itace abinda Annabi (S.A.W) yafi bawa muhimmanci
acikin watan Ramadhan.To kunjifa Annabi yake daukar dogon zango idan
yana sallar nafila da azumi.Ya Allah kasa muna daga cikin wadanda zaka
'yanta acikin wannan wata, domin darajar Annabi Muhammad (s.a.w).


www.hanyantsira.mywapblog.com


whatsapp
09039016969



Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA


Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate

Blog Archive