Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

Abubuwa uku

ABUBUWA GUDA UKU KADA KA RISKESU HAR SAI
KAYI TAMBAYA AKANSU.

by muhd abba gana

1- IBADA
2- MATA
3- AIKI.
Abubuwa Uku Baka Samun Sakat Har Sai Sun
Rabu Dakai
1- WAS-WASI
2- BASHI
3- MUGUN ABOKI.
Abubuwa Uku Da Baikamata A Jinkirta Su Ba.
1- WALIMA
2- TA'AZIYYA
3- SALLAR MAGARIBA.
Abubuwa Uku Allah Ka Tsaare Mu Dasu.
1- DAN HARAM wato dan cikin (Shege).
2- MAI YANKE ZUMUNTA
3- CIN DUKIYAR MARAYU.
Mutane Uku Karka Kuskura
Kayi Abota Dasu
1- WAWA
2- MAI KARANCIN HIMMA WAJEN IBADA.
3- MAI KARANCIN MUTUNCI.
Mutum Uku Kada Ka Saurari
Maganar Su.
1- MAKARYACI
2- MAGULMACI
3-MAI BAYAR DA SHAIDAR ZURR.
Mutum Uku Kar Kayi Abota Dasu
1- MAI HASSADA
2- MAI SA'IDO
3- MAI FUSHI DA MAHAIFANSA.
ALLAH YASA MU DACE KA DATAR DAMU GA
RAHAMARKA.
Wanda yakeda nasa abubuwa 3 shima zai iya
rubutawa saboda tunatar da yan uwa.

www.hanyantsira.mywapblog.com
Share:

SIRRIN ZAMA DA MIJI 9B

mamatan-kwarai.jpg

SIRRIN ZAMA DA MIJI

{KASHINA 9}

(IYA MAGANA 2)


BY

MUHD*ABBA*GANA
09039016969

manzon Allah yana cewa mafi alherin aure shine auren da aka samu sauki a cikinsa koba komai dukkan iyayen da suke bukatar nemawa yayansu girma a idon mazajensu to sai ku kyautatawa mijinta tare da nuna mishi ai shima dansune don haka dole ne su kyautata masa. to amma abin haushi kuma abin takaici sai ya zama mafi mafi akasarin hankalin iyaye ya tafi a cikin sai an yiwa yayansh abinda zasuyi alfahari da shi kuma su burge koda kuma shi mijin zai shiga halin damuwa da takaici, wanda idan muka dubi koyarwar manzon Allah ya nuna cewa koda a cikin harkar saye da sayarwa Allah yana yin rahama da jin kai a gurin dan kasuwar da yake saukaka kayan siyarwarsa to ballantana ma a cikin sha,anin aure wanda yake duk wanda yace yana son yarka tofa baka da kamarsa a cikin masoyanka don haka shine mafi cancanta da a taimaka masa tare da yin agaji da tausayi a gare shi to amma abin mamaki sai yazo a halin da muke ciki yanzu babu abinda ake jira face sai wanda za,a dorawa nauyi. to jama a ya kamata mu riki koyarwar manzon Allah da kuma abinda zai janyo mana farin ciki da zaman lafiya da sukuni a tsakanin junanmu wannan shine zai taimaka izuwa dorewar zamantakewar aure. kuma ya kamata mu sani cewa shifa auren nan ibada ne bai dace ba a ce muna shigar da son zuciyarmu a cikin abin da Allah ne ya tsara ga yanda yake so aiwatar dashi. in da ace tsadar aure ko kuma tsadar tsadaki wani abin alherine ko kuma wata daraja ce a gurin Allah madaukakin sarki to da mafi cancantar wadanda ya kamata suyi hakan, to amma saiya zama a tsakaninsu bbu tsanantawa sai fa jin kai da tausayi da rahama a tsakaninsu. don haka idan har ba za mu iya yin yanda sukayi ba to sai mu kamanta domin mu samu kadan daga darajojin da suka samu. muna rokon Allah ya hadamu da mata ba gari wadanda zasu taimake mu domin cikar addinin mu ya Allah kayi a gaji ga dukkan matan da suke yin biyayya a gurin mazajensu da kuma wadanda suke taimakon mazajensu kafin na kammala wannan littafi ina sanar da dukkan madmsu sha'awar karanta littafina cewa ina masu albishir da fitowar sabon littafina mai suna "UWA TA GARI" muna rokn Aah yayi mana ludufi da kuma mafita a cikin dukkan al,amuranmu 'amin. NI MARUBUCIN WANNAN LITTAFI INA DADA YIWA ALLAH GODIYA DAYA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFI WANDA YA TATTARO MUHIMMAN DARUSA DA SUKA SHAFI RAYUWAR MA,AURATA MUSAMMAN YANDA YA KAMATA AMARYA TAYI MU'AMMALA DA MIJINTA A MUSULUNCI INA ROKON ALLAH YAYI MANA JAGORANCI A CIKIN DUKKAN AL,AMURANMU'AMEEN SUMMA AMEEN DAN UWANKU MUHD ABBA GANA
09039016969

hanyantsira.mywapblog.com
Share:

SIRRIN ZAMA DA MIJI 9

mamatan-kwarai.jpg

SIRRIN ZAMA DA MIJI

{KASHINA 9}

(IYA MAGANA)


BY

MUHD*ABBA*GANA
09039016969

yana daga cikin ladubban zamantakewa wadanda yake amta mace ta kiyaye shine ta iya magana a lokacin da take hira da mijinta ma'ana ya kamata tun farkon ta sani cewa ita fa macece kuma Allah madaukakin sarki ya san ya nutsuwarta a wajen mijinta don haka yana da kyau maganarta ta zama mai farantawa maigidanta. yana da kyau mace ta zama mai tausasa muryarta a lokacin da take hira da mijinta wato ta zama kamar wata karamar yarinya mai nuna shagwaba wannan shi zai dada sa mijinta ya yarda da ita kuma harta kallo idan zaki kalli mijinki to ya kasance kallone na girmamawa da mutuntawa kuma ya zama kallone da zai tabbatarwa mijin cewa kina kaunarsa kuma kin yarda dashi har a cikin zuciyarki, kuma yana da kyau ko a fagen tafiya kada mace ta zama kamar namiji musamman idan tana a gaban mijinta don haka ya kamata tafiyarta ta zama a bisa tsari da kuma nutsuwa amma idan tafiyarta ta zama ta hauka wato irin ta masu jin karfi to wannan zai iya rage kimarta a cikin zuciyar mijinta. haka kuma yana da kyau a musulunce mace tayi shagwaba a gurin mijinta domin nana aisha (RTA) ta kasance yar lelen manzon Allah (SAW) hasalima an samu lokacin data cewa manzon Allah (SAW) sai ya dauketa haka kuma yazo a cikin wani hadisi cewa manzon Allah (SAW) yana yin tseren gudu shida matarsa wato sayyidatu Aysha (RTA) don haka wannan yana nuna mana muhimmancin kyautata mu'amalla a tsakanin mace da mijinta domin a samu jin dadi nutsuwa da kwanciyar hankali sabanin yanda harkar aure take gudana a tsakanin al'ummar wannan zamani wanda zaka mafi akasarin jama'a wato ma'auratan sun saki ka'idojin zamantakewa shi yasa ake ta fuskantar matsaloli a tsakaninsu wannan yasa saika ga hartakai suga rabuwa wanda shine mafi zama abin ki a gurin Allah (SWT) a cikin harkar aure.mafi akasarin abinda ya sa ma aurata suke samun matsaloli a cikin harkar aure shine son zuciya da suke sa a gabansu wato ya zama an daina binciken abinda Allah yace ko abinda manzon Allah (SAW) yace sai ya zama su kuma mata sun maida aure kamar wata hanyar neman wadata da kuma arziki wato kamar kasuwanci tun a farkon neman auren ba a tausassawa mai neman sai a dinga dora masa abubuwa daban daban tun yana ganin kimar matar har ma ya daina ganin girmanta dana iyayenta, kuma sai a zo ayi auren shi kuma idan ya kalli wahalar daya sha kafin ayi auren shi yasa ba zai ji tausayin matar ba. kuma a karshe dai ita ma sai tace mijin ba zai juyata ba to haka dai lamarin zai ci gaba da kasancewa a tsakaninsu a karshe sai kaga an rabu domin kuma tun daga farkon auren an sabawa koyarwan manzon Allah. zan cigaba gobe insha Allah.
Share:

SIRRIN ZAMA DA MIJI 8

SIRRIN ZAMA DA MIJI {KASHINA 8} (KIYAYE SIRRIN MAI-GIDA) BY MUHD*ABBA*GANA 09039016969 Dukkan mace ta gari bazata so ta yada sirrin maigidanta ba ko kuma ta fadawa wasu sirrin maigidanta musamman a cikin sha'anin abin daya shafi harkar kwanciyarsa aikata wannan laifi ne mai girma a gurin Allah domin manzon Allah (SAW) ya tsawatar da kada miji ya bawa mutane labarin abin da yake aikatawa da matarsa haka itama matar kada ta bada labarin abinda yake faruwa a tsakaninta da mijinta a cikin sha'anin kwanciya. haka kuma baya halarta a gurin mace ta hana kanta a gurin mijinta wato idan ya nemeta domin kwanciyar aure yin haka sabawa Allah ne da kuma manzon Allah (SAW) hasalima jinkiri a lokacin da miji ya bukaci saduwa da matarsa shima laifine domin manzon Allah (SAW) yace Allah ya tsinewa matan da suke cewa mazajensu sai an jima har barci ya rinjayi idanun mijin. wato su kuma wadannan in matan baza su cewa mazajensu su ba sa son jima'i ba to amma sai su dinga jan aji har sai mijin yayi barci to yin haka laifine babba don haka sai a kiyaye domin samun zaman lafiya da kuma cikar samun ladan zamantakewa a gurin Allah madaukakin sarki. abinda ya sawwaka kenan sai mun hadu a babi na gaba
Share:

SIRRIN ZAMA DA MIJI 7

SIRRIN ZAMA DA MIJI {KASHINA 7} (KIYAYE DUKIYARSA) BY MUHD*ABBA*GANA 09039016969 yazo a cikin siffofin salihar mace cewa manzon Allah (SAW) yake cewa: ita ce matar da take kiyaye kanta kuma ta kiyaye dukiyar mijinta a lokacin da yake a gida da kuma lokacin da baya gida. don haka dukkan mace ta gari itace wacce take kiyayewa tare da taimakawa mijinta a cikin sha'anin tattalin arzikinsa. bayan haka yana da kyau mace ta kare kanta daga barin yawaita tambayar mijinta domin aikata haka yana janyo mata zubewar kwarjininta a idon mijinta don haka yana da kyau mace ta kiyaye wadannan abubuwa domin samun kyakkyawar zamantakewa mai aminci a tsakaninta da mijinta. Allah ya baku ikon gyarawa, naku har kullum jikan marubuta muhd abba gana
Share:

SIRRIN ZAMA DA MIJI 6

SIRRIN ZAMA DA MIJI
{KASHINA 6}
(KIYAYE GANINSA)
BY
MUHD*ABBA*GANA 09039016969
yana da kyau mace ta kiyaye ganin mijinta ma'ana
tayi kokarin kawar da duk wani abu da zai bata
masa rai koda a dakine ko kuma a gidan kodai a
jikinta. ko kuma a sutura ne yin haka shine zai sa
miji ya kara sakin jikinsa da matarsa kuma ta
zama wacce ta san halin da mijinta yake ciki na
bacin rai ko farin ciki har izuwa biyan bukatarsa
da ita.
Comments
Share:

SIRRIN ZAMA DA MIJI 5

SIRRIN ZAMA DA MIJI
{KASHINA 5}
(KAUNAR MIJI)
BY
MUHD*ABBA*GANA 09039016969
yazo a cikin hadisi cewa "matayen ku wadanda
suke matukar kaunarku anan duniya sune matayen
da zaku zauna dasu a cikin aljannah (mallam
ammafa sai aiki mai kyau) kuma a nan soyyaya
sifface ta yan matan aljannah don haka ko anan
duniy managartan mata ne kawai zaka ga suna
nuna w mazansu soyayya domin mafi akasarin
wasu matan suna ganin idan wai suka nuna wa
mazansu kauna ai sun zubar da ajinsu, kuma wai
sai na miji ya raina su. wannan wani rashin
tunanine da kuma rashin ilimi ne da yayi wa wasu
matan yawa, domin yazo a cikin wani hadisi cewa:
idan miji ya kalli matarsa yayi farin ciki da wannan
kallon to wannan matar zata kasance a cikin
mafifitan mata a lahira" to yaya kuma a matsayin
ita matar da take nunawa mijinta kauna tare da
faranta masa? amusulun ci ana so mace ta dauke
hankalin mijinta ta hanyar dadada masa domin kar
ya fita waje matan banza su dauke hankalinsa.
abin da ya sawwaka kenan Allah baku ikon
gyarawa, ameen naku har kullum har abada jikan
marubuta muhd abba gana
Share:

SIRRIN ZAMA DA MIJI 4

SIRRIN ZAMA DA MIJI
{KASHINA 4}
(TSAFTA)
BY
MUHD*ABBA*GANA 09039016969
Tsaftarki itace mafi amfani a cikin tsarin
mu'amalarki da mijinki,dukkan biyayyar da zakiyi
masa to ki sanifa tsafta itama wata muhimmin yar
abace da zata taimaka domin kammalar jin dadi a
tsakaninku, yazo a cikin hadisi cewa manzon Allah
(SAW) yace mafi alheri mace itace wacce ake
samun farin cikiyayin da aka kalleta, wato itace
wacce take farantawa mijinta yayin da yake
kallonta, ko ba komai ita tsafta itace cikar imanin
mutum don haka ba daidai bane a gurin matar
aure a sameta cikin kazanta, tsaftan ya kunshi
gurin kwanciya, yayanta, dakinta,abinci, jikinta,
gashin kanta, hakoranta,farcenta dukka wayannan
abubuwa ya kamata a ce mata sun kiyaye. yazo
acikin wani hadisin manxon Allah (SAW) yana
cewa: mafi alherin mace itace wacce idan aka
kusanceta sai aji kamshi yana tashi a tare da ita
( ba wani warin albasa albasa ba) don haka ashe
ya isa abin kuna a gurin mace aji wari da doyi
yana tashi a jikinta,domin ita kan tama bazata ji
dadin kanta ba ballantana shi wanda yake tare da
ita wato mijinta. toh abin da ya sawwaka kenan
Allah bamu ikon gyarawa baki daya.Ameen.
Share:

INA MASU MATSALAR SAURIN KAWOWA A LOKACIN JIMA'I ???

INA MASU MATSALAR SAURIN KAWOWA A
LOKACIN JIMA'I ???
To ku karanta wannan.
Maigida bai kamata kafara tunanin biyan buqatarka
ba kafin ta iyalinka.
Kasani wannan iyalinka ce, biya mata buqata wajibi
ne a kanka, ba wace ka daukoce domin zina ba.
Wannan tunanin zaisa nan da nan kayi saurin
kawowa kafin ita.
Galibi wannan tafi faruwa ga auren fari wajen maza,
tareda rashin samun wannan ilimin, to wannan
damuwar takan taru a zuciyar matarka har ya
zamana bata iya kawowa, sai tayi ta haihuwa ba
tare dajin dadin saduwar ba.
Hakanan dadewa ba a sadu ba yakan janyo
wannan matsalar ta saurin kawowa.
Hanyoyin magance wannan babbar matsala su ne
kamar haka:-
1) Kayi qoqarin shafa gabanka in kaji zaka kawo
sai ka bari, ka sakeyi har kamar uku a kwana uku
cikin mako guda.
2) Kanemi tsawaita lokacin kawowar, in kaji kafara
sama sai kazare sai hankalinka ya kwanta saika
mayar, wannan yana da kyau sosai.
3) Idan sha'awarka tafara sama sai kazaro ka
wanke da ruwan sanyi, kashare da tsumman da
yasha ruwan sanyi, sannan ka mayar. (Ban da mai
sanyin qanqara yakan cutar).
4) Idan iyalinka ce aqasa, tabbas akwai saurin
kawowa da wuri saboda saurin zuwan jini gabanka,
amma in itace a sama bazaka sami wannan qarfin
ba (amma shima da 'yar matsala kamar yadda Ibn
Qayyim ya fadi).
5) Amfani da condom albashi a dan huda gaban
yadda ruwanka zai fita, kana iya hada biyu in har
kana jin susarta.
6) Idan sha'awarka tafara motsawa saika zarota,
matarka tadora babban yatsarta a bisa kan
ta6aryarka manuniyarta a qasa saita matse da dan
qarfi ta ci gaba da matsewa, zaka danji zafi, nan
take sha'awar za ta kintse, dan anjima kadan saika
mayar, to amma fa kasani duk bayanan kar kabari
sai sha'awarka tagama haduwa, a wannan lokacin
ba wani abu da zai iya taimakonka, wadannan
hanyoyi sukan taimaka da kashi 95/100, sai yin
amfani da maganin dagawar sha'awa wato (Prozac)
likitoci sun sanshi, amma magungunan da ake
yawan sayarwar nan gaskiya suna rage jin dadi.
Idan kai mai saurin kawowa ne, kuma daka kawo
gabanka zai kwanta (sabo da irinka kenan), to kada
kasauka, kaci gaba da qoqari, wannan yauqin ba
zai jima ba zai daskare, hakan zai taimake ka
kasake miqewa ko kuwa ita uwargidan ta sami
abin da take buqata.
KA NISANCI SON KAWOWA A ZUCIYARKA YIN
HAKAN ZAI TAIMAKA SOSAI.
Kuyi hakury kada kuga na zafafa harkar addini
saida gyara, wadansunku suna fama da wannan
matsalar amma kunya takan hanasu.
Allah kayi mana maganin abinda yafi Qarfinmu.
Share:

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate