Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

yadda ake warware sihiri a musulunci

YADDA AKE WARWARE SIHIRI


TAMBAYA:

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Assalamu alaikum.
Dan Allah malam a fitar dani daga cikin duhu gameda abin da yake damuna. Mahaifiya tace taje gurin Boka ayi mata maganin ciwon mara da yake damunta, tace tana da ciki yakai shekara guda da rabi, amma likitoci sunyi scanning sunce ba komai tosai Bokan yace mata asiri akayi mata, kuma zaiyi mata magani nan take ta haife abinda yake cikinta amma zata kawo tunkiya da dubu bakwai, sai take min magana in kawo kudi a sayi tunkiyar kuma akai masa dubu bakwan, to gaskiya malam zuciyata bata aminta da Bokan bane. Shiyasa Nakeso kabani fatawa shin irin wannan hanyar ta magani ta halatta a addini ? Idan bata halatta ba wacce hanya zanbi wajen qin biyan kudin da kuma sanar da ita ? Wassalam nagode malam Allah yaqara basira.

(Daga Binta Umar).

AMSA
------------------------------------------

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To ‘yar uwa, tabbas ba'a warware sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin
Alqur’ani. Wasu malaman sunyi bayani cewa:Ana iya warware sihiri ta hanyar karanta wadannan ayoyi kamar haka:

1- Ayatul-Kursiyyu.
2- Quliya.
3- Ikhlas.
4- Falaki da Nasi.
5- Sai kuma ayah ta: 117 zuwata 122, cikin Suratul
A’araf.
6- Sai kuma Ayah ta: 79-81 cikin Suratu Yunus.
7- Sannan sai Ayah ta: 65-70 cikin Suratu Dhaha.Za’a karanta su, sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya guda bakwai, sannan ayi wanka dashi a waje mai tsafta.Haka ake magance sihiri cikin yardar Allah. Bai halatta ki taimaka mataba, wajan bada
wadannan kayan da boka yanema duk da cewa mahaifiyarkice.
Saboda ba’a yiwa iyaye biyayya a wajen sabon Allah.Ya wajabta gareki kayi mata nasiha cikin hikima,kisanar da ita cewa:Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa:“Duk wanda yaje wajan boka, ya tambaye shi wani
abu, Allah bazai amshi sallarsa ba, ta kawana
arba’in”Muslim ya rawaito acikin hadisi mai lamba ta:2230. Kinga idan mutum ya mutu acikin wadannan
kwanaki akwai matsala, musamman ma tun da akwai hanyar da shari’a ta yarda da ita.Sannan awani hadisin kuma yana cewa:“Duk wanda yaje wajan boka ya gaskata abin daya fada, to tabbas ya kafurce da abinda Annabi Muhammad yazo dashi”Kuduba Sunanu-Abi-Dawud hadisi mai lamba ta:
3904, kuma Albani ya inganta shi.INA GANIN DA IRIN WADANNAN HADISAN ZAKI IYA
GANAR DA ITA, TA DAWO KAN HANYA. Allah Shine mafi sani.

www.hanyantsira.mywapblog.com


whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate