Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

LOKUTAN AMSA ADDU'A.

LOKUTAN AMSA ADDU'A.

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .


LOKUTAN AMSA ADDU'A.
~~~~~~~~~~~~~~
Kowanne lokaci mutum yayi addu'a dai -dai ne,
Allah mai iko ne ya amsa masa.
Sannan akwai lokutan da Manzon Allah (s.a.w)
yayi bayani suna da falala, idan mutum yayi addu'a
cikinsu Allah yana amsawa.
Ga lokutan kamar haka:
1 -DAREN LAILATUL QADRI, idan Allah yayiwa
mutum muwafaka ya ganshi.
2 -Yin Addu'a bayan mutum ya idar da Sallar
farilla, ko nafila
3 -Yin Addu'a tsakanin kiran Sallah da tayar da
Ikama.
4 -Yin Addu'a a lokacin da ruwan sama yake
sawka (anso mutum yayi sallah raka'a 2) idan
akwai halin yi.
5 -kowacce awa ta ranar Juma'a domin Manxan
Allah (s.a.w) yace:
Akwai wata awa a ranar Juma'a, da mutum zai
dace yayi addu'a da Allah ya amsa masa
6 -Lokacin da mutum yayi SUJJADA acikin Sallah.
7 -Yin Addu'a lokacin da mutum ya sami ruwan
ZAM-ZAM zai sha
8-Lokacin da mutum yatashi TSAKADDARE yayi
Nafil-fuli Allah ya taimakemu duniya da lahira
yakuma amsa addu'o'in mu na alkhairi.


www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969


Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA
Share:

ALAMOMIN TASHIN ALQIYAMA. Kashi na 1

Alamomi 001-030
1. Aiko Annabi (sallallahu-alaihi-wasallam) {ranar
litinin, 21/Ramadan/0013bh daidai da 10/
August/610m} yana shekara arba'in 40 da wata
shida 6 da kwana goma sha biyu 12 lissafin wata/
shekara talatin da tara 39 wata uku 3 da kwana
ishirin 20.
2. Wafatin Manzon Allah (sallallahu-alaihi-
wasallam) ranar litinin 12/rabi'ul-Auwal/11ah yana
da shekara sittin da uku da kwana hu'du
3. Tsagewar wata
4. 'Karewar Sahabbai
5. Bu'de Baitil-Maqdis.
6. 'Barkewar Annoba;- mai kama da ciwon
dabbobi.
7. Bayyanar fitintunu masu yawa.
8. Bayyanar tashoshin tauraron 'Dan Adam.
9. Yaqin Siffaini.
10. Bayyanar khawarij.
11. Masu da'awar Annabta ta qarya
12. Yalwatar Arzi'ki.
Arzi'ki zai yalwata
13. Bayyanar wuta a Hijaz, dutse mai aman wuta.
14. Ya'ki da turkawa.
15. Bayyanar Azzalumai masu duka babu dalili.
16. Yawan zubar da jini da kashe-kashe
17. 'Dauke Amana;- ma su Amana zasuyi 'karanci.
18. Koyi da Yahudu da Nasara.
19. Baiwa zata haifi uwargijiyar ta.
20. Bayyanar masu tsirara-tsirara(basa shiga ta
addini)
21. Matsiya ta, Matasa masu kiwon awaki zasuyi
yin dogayen gine-gine.
22. Yin Sallama ga wanda aka sani kawai;- mutane
za su daina yiwa mutum Sallama sai sun sanshi.
23. Ya'duwar kasuwanci;- ko ina zai zama
kasuwa.
24. Mata zasuyi tarayya da mazansu a kasuwanci.
25. Wasu tsirarun 'yan kasuwa zasu mamaye
kasuwanci;- ya zama ba ayi dakai sai da yardarsu.
26. Shaidar Zur.
27. 'Boye shaidar gaskiya.
28. Yawan Rowa;- mutane zasu zama marowata.
29. Yanke zumunta.
30. Munana maqotaka.
Allah kasa mucika da imani.
Zamuci gaba Insha Allah.
Share:

Alamomin Tashin Alqiyama 2

ALAMOMIN TASHIN ALQIYAMA.
Kashi na (2).
Alamomi 31 zuwa 61
31. Ya'duwar laifuffuka.
32. Bayyanar jahilci.
33. Amincewa maha'inci, da tuhumar mai Amana.
34. Mutuwar Mutanen 'kwarai da Ya'duwar
lalatattu.
35. Yaki Halal Yaki Haram.
36. Rubda ciki akan Baitil-Mali (Asusun-
gwamnati).
37. Mayar da dukiyar Amana ganimah.
38. Rashin fitar da Zakkah da dadin rai;- mutum ya
ga zakka kamar Asara Ce yayi.
39. Yin Karatu dan Neman Abun duniya.
40. Yiwa mata biyayya da sabawa Uwa.
41. Fifita Abokai ko Kawaye akan iyaye.
42. Hayaniya a masallatai.
43. Mafi yawan shuwagabannin Al'ummah zasu
zama fasiqai.
44. 'Kas'kantattu zasu zama manyan gari.
45. Girmama mutum don tsoron sharrin sa.
46. Za'a halatta Zina.
47. Halatta Alhariri ga Maza (sa Alhariri ga maza
haramun ne, amma za ayi zamanin da za'a halatta
shi.
48. Ya'duwar Kayan maye.
49. Ka'de ka'de da raye-raye zasu mamaye
Al'ummah.
50. Masifa da Bala'i zasu yawa Har mutum ya
dinga fatan mutuwa.
51. Wani Zamani da mutum zai kwana Mumini
yawuni kafiri;- saboda mafi yawan maganganu da
aiyuka da basa kan Shari'ah.
52. 'Kawata Masallatai dayin gasar Hakan (kaji ana
cewa Masallacin mu yafi naku kyau).
53. 'Kawata gidaje dayi musu kwalliya.
54. Yawan Saukar Kwarankwatsa da Aradu.
55. Yawan Rubuce-Rubuce;- Ya'duwar Rubutuce-
Rubucemarasa amfani.
(jaridu da mujallu, da littafai da internet) ba a
tunanin amfanin rubutun kawai da an rubuta.
56. Wanda suka 'kware a roko da ziga, su suka fi
samun kudi.
57. Za shagala da karanta wasu abubuwa a bar
Al'qur'ani.
58. 'Karancin Malaman fiqhu da yawan Gardawa.
59. Neman Ilimi a wajen 'kananan mutane;-
'karamin Mutum wanda baya aiki da ilimin sa.
60. Yawan mutuwar bazata.
Allah kasa mucika da imani.
Saimun hadu Darasi nagaba.
Insha Allah.
Share:

Alamomin tashin Alqiyama 3.

ALAMOMIN TASHI ALQIYAMA.
Kashi na (3).
61. Shugabancin Wawaye (kuma suna ganin kansu
wayaiyu).
62. Lokaci zai dinga sauri.
63. Banzaye zasu mamaye kafafan ya'da labarai;-
Mutumin daba kowa ba, kuma bai zan komai ba,
zai dinga magana kan abubuwan da suka shafi
Al'ummah.
64. Madaukaki a duniya shine banza 'dan banza;-
kaga ana ta rububin wani wanda baida amfanin
komai saboda wani shirme da yake Misali;- 'Yan
Bal da Mawaka.
65. Maida cikin masallatai Hanyoyi.
66. Sadakin Aure zaiyi tsada, sai kuma yazo yai
araha.
67. Dawakai zasuyi tsada sai kuma suzo suyi
araha.
68. Kasuwanci zaiyi sauki (ta yadda zaka sai Abu
ko ka sayar daga dakin ka, batare da kaje ko ina
ba)
Misali;- yanar gizo
69. Kafiran duniya zasuyi taron dangi akan
musulmi.
70. Mutane zasu dinga gudun limanci acikin Sallah
(saboda ba cikakken Albashi).
71. Aukuwar Mafarkin Mumini (in Mumini yai
mafarki sai Abu yafaru.
72. Yawan karya.
73. yawan gaba.
74. Girgizar 'kasa.
75. Yawan Mata.
76. 'Karancin Maza.
77. Aikata Sa6o a fili.
78. Maida karatun Al'qur'ani hanyar Neman kudi.
79. 'Kiba, mutane zasuyi ta kiba maiyawa.
80. Bayyanar mutane masu yin shaida tun ba a
tambaye suba.
81. Masu Bakance basa cikawa.
82. Masu 'karfi zasu danne raunana.
83.'Rashin Hukunci da Alqur'ani.
84. Yawan rumawa da 'karancin larabawa.
85. Yaduwar kudi.
86. 'Kasa zata fitar da taskokinta.
87. Za a dinga shafe halittar wasu mutane suna
komawa wata Halitta daban.
89. Tsagewar 'kasa, ta hadiye mutane.
90. Wasu kwarangwazai, duwatsun da ba aSan
suba zasu dinga fa'dowa mutane aka.
92. Yawan ambaliyar ruwa.
93. Ruwan 'bala'i;- wanda baya fidda shuka ko
tsiro.
93.wata fitina zata 'barke tsakanin larabawa Har
takusa 'karar dasu.
94. Bishiya zatayi magana don taimakawa
musulmi.
95. Dutse zai magana don taimakawa musulmi.
96. Ya'kin Musulmi da Yahudu.
97. Kogin furat zai 'kafe, a hango Dutsen Gwal a
ciki.
98. Zamanin da za a yiwa masu addini kallon ba
wayayyu ba.
99. 'Kasashen larabawa zasu samu cigaba mai
yawa.
100.Bayyanar wata Babbar fitina da zata shafi
kowa
Mu ha'du a darasi na gaba.
Allah ya karemu sharrin fitintunu
Share:

Alamomin tashin Alqiyama 4.

ALAMOMIN TASHIN ALKIYAMA (4).
Mun tsaya akan alama ta 100, zamuci gaba.
101 Bayyanar bakar fitina gama gari sai ta shafi
kowa.
102 masifu za suyi yawa birni da kauye.
103 Wani zamani zaizo sujjada daya tafi duniya da
abinda yake cikin ta, saboda karancin masu ibada.
104 Rigima akan ganin wata, saboda wata zai
kumbura, ya dinka fiyowa babba.
105 za a dinga kaura ana komawa yankin Sham
wato Syria.
106 Yakin duniya tsakanin musulmi da Rumawa
(Turawa).
107 Zaa bude yankin Qusdunsuniyya, karo na biyu,
bayan na zamanin daular Usmaniyya.
108 Zaa dena rabon gado, (masu karfi su cinye na
kanana).
109 Zaa dena farin ciki da samun ganima (saboda
wadata tayi yawa)
110 Zaa koma amfani da makamai na gargajiya,
saboda na zamani zasu dena amfani.
111 Zaa raya baitul Maqdis, bayan karbo shi daga
hannun yahudawa.
112 Mutane zasu kauracewa Madina, idan shagala
tayi yawa.
113 Madina zata kore ashararai daga cikin ta, babu
mai jin dadin zaman madina sai mumini.
114 Duwatsu zasu gushe daga gurinsu, saboda
gine-gine naci gaba.
115 Wani mutum zai fito daga yankin Qahdan na
larabawa kuma mutane zasu bishi.
116 Bayyanar wani mutum mai suna Jah,Jah.
117 Dabbobin dawa zasuyi magana irin ta mutane,
kamar zaki da kura da makaman tansu.
118 Tsumagiya ma zatayi magana,(Bulala)
119 Hancin takalmi zaiyi magana.
120 Jikin mutum zaiyi magana (kamar cinyarsa)
tabashi labarin abin da iyalansa suke aikayawa
idan bayanan.
Allah kasa mucika da imani.
Zamuci gaba darasi mai zuwa.
Insha Allah.
Share:

Alamomin Tashin Alkiyama 5.

ALAMOMIN TASHIN ALQIYAMA.
Kashi na 5.
121 Alkiyama bazata tashiba sai anyi watsi da
musulunci, ba karatu ba aiki.
122 Alkiyama bazata tashi ba sai an dauke
Alkur'ani mai girma daga cikin takardu, da kirjin
mahaddata,
123 Wata bataliyar mayaka zasu tunkari macca da
niyar yaki, amma kasa zata hadiye su a hanya.
124 Zaa kauracewa zuwa aikin hajji.
125 Kabilar kuraishawa zasuyi kadan a duniya.
126 Rushe kaabah ta hannun wani mutum daga
yankin Habasha.
127 Wata iska mai dadi zata dinka dauke ran
muminai idan musifa tayi yawa.
128 Zaa dinka yin ginai- ginai masu tsawo a
Macca.
129 Wasu tsinannun mutane, zasu dinka laantar
magabata, (Annabawa).
130 Zaa sami kayan hawa na zamani,
131 Bayyanar Ma'hadi,
Zamu ci gaba a darasi na 6, kuma insha Allahu
zamu dauki daya bayan daya domin sharhi da
karin bayani, duka wadananan alamomi wadanda
suka zone acikin ingatattun hadisai, na sunnah
(Allah yasa mucika da imani)
Share:

Alamomin tashin kiyama 6

ALAMOMIN TASHIN ALKIYAMA (6).
Manyan alamomi na tashin alkiyama wadanda
suke kusa daf da tashin alkiyama Sune kamar
haka:
132 : Bayyanar Dujal (babban balain da ake jira).
133: Saukowar Annabi Isah.
134 : Fitowar Yajuj da Majuj.
135 Girgizar kasa (manya manya sau uku a
duniya).
136 : Hayakin dazai rufe duniya baki daya.
137 : Bayyanar wata dabba (amfadi kamaninta a
hadisai).
138 : Rana zata fito ta yamma.
139: Wata wuta zata fito takora mutane, zuwa filin
Mahshar.
Wadannan sune, alamomi na tashin alkiyama.
Kamar yadda suka zo ahadisai lngatattu, idan mun
sami lokaci zamuyi sharhi akansu.
Insha Allahu.
Share:

Wannan Rana akwaita da firgici.

WANNAN RANA ITACE MAI CIKE DA BAN TSORO
DA FIRGICI A CIKINTA:
Sahihin Hadisi Daga Cikin SAHIHU MUSLIM.
Daga Sahabi Abu Zarril Giffari YaCe:-
"Watarana Muna Zaune Tare Da Manzon ALLAH
(S.A.W) Da Yamma.
Sai Rana Ta Tafi Zata Fadi Sai ANNABI (S.A.W)
YaCe:
'Ya Abu Zarr Ko Kasan Inda Ranar Nan Zata
Fadi???'
Sai Abu Zarr YaCe: ALLAH Da Manzonsa Ne Sukafi
Sani,
Sai ANNABI(S.A.W) YaCe:
Ai Ba Faduwa Takeyi Ba, Tana Zuwa Gaban ALLAH
(S.W.T) Ne, Sai Ta Fadi Tayi Sujjada Ga ALLAH
(S.W.T) Idan Tayi Sujjadar Sai ALLAH Ya Bata
Dama Sai Ta Wuce.
Shine Sai Ta Bullo Ta Gabas Idan Gari Ya Waye To
Ana Nan Watarana Zata Je Tayi Sujjada Gaban
ALLAH Sai ALLAH YaCe:-
'An Karbi Sujjadarki Amma Yau Ba Za'a Baki Hanya
Ba, Ki Koma Ta Inda Kika Fito.
Idan Ta Koma Kuma Gari Ya Waye Sai Ta Bullo Ta
Yamma.
To a Wannan Lokacin Ne Fa Da Zaran Rana Ta
Bullo Ta Yamma To An Rufe Kofar Karbar Tuba
Babu Wani Wanda Zai Tuba Allah ya kar6a.
Kuma a Wannan
Rana Ne Ko Da Kafiri YaCe:
LA'ILAHA ILLALLAH MUHAMMADUR RASULULLAH
(S.A.W).
To ALLAH BaZai Karbi Wannan Shahadar Ba.
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN.
Ya ALLAH! Kasa Bamu Cikin Wadanda Zaka Rufe
Kofar Tuba Ba Tare Da Mun Tuba Ba.
Share:

INDAI KAGA WADANNAN ABUBUWAN SUNA FARUWA A TSAKANIN AL'UMMA TO SUJIRA AKWAI HORO KO AZABA DA ZATA BIYO BAYA DAGA ALLAH (S.W.T).

MANZON ALLAH (S.A.W) YACE:
INDAI KAGA WADANNAN ABUBUWAN SUNA
FARUWA A TSAKANIN AL'UMMA TO SUJIRA AKWAI
HORO KO AZABA DA ZATA BIYO BAYA DAGA
ALLAH (S.W.T).
1- Karancin ruwan sama a doran kasa.
2- Dukiyar kasa tazama ta wadansu mutane daban
da al'umma kasa baki daya.
3- Amana tazama ganima a tsakanin
al'umma.
4- Zakka tazama biyan bashi a cikin
al'ummar musulmai.
5- Miji yadinga bin maganar matarsa duk abinda
tace yayi watsi da maganar mahaifiyarsa.
6- Ya amince da maganar abokansa amma yayi
watsi da ta babansa.
7- mutane sudinga mayar da malamai jahilai
kaskantattu a cikin addini.
8- A dinga girmama mutun ba dan Allah ba.
9- Sannan mutane zasu dinga tsoran wani badan
komaiba sai dan gudin sharrinsa.
10- Mutane zasu yawaita shan giya (shaye-shaye
zai yawaita).
11- Mutane zasu saki karatun Al-qur'ani surike
wakoki ababan more rayuwa dajin nishadi.
12- Ababan kide-kide zasu yawaita a cikin
al'umma.
13- Mutanen karshen zamani zasu dinga tsinewa
na farkon zamani da kaskantar dasu.
14- mutane zasuyi saki da Sunnah ta suyi ruko da
bidi'a.
15- mutane zasu mayar da karatun kur'ani abin
neman kudi.
TO ''YAN UWANA A HALIN YANZU ACIKIN WANNAN
ABUBUWA DA ANNABI MUHAMMADU (S.A.W)
YAFADA MENENE BAI FARUBA ???
SANNAN KUMA MENENE BA'A AIKATAWA A DORAN
KASARNAN ???.
Dan haka 'yan uwa.
Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!!
Mukoma ga Allah mu yawaita neman
gafara a wajen SA.
Ya ALLAH KASA ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) YA
CECEMU RANAR SAKAMAKO.
Share:

Halin da duniyar Musulunci take ciki a yanzu.

MANZON ALLAH KENAN SARKIN GASKIYA !
MANZON ALLAH (S.A.W) Yace:
Akwai wani zamani zai zoma al'ummata (acikinsu)
duk wanda yariqe addininsa zai zama kamar wanda
yariqe garwashin wuta.
MANZON ALLAH (S.A.W) yace:
Nan gaba kad'an al'ummomi zasu zagayeku (ku
musulmai) kamar yadda jama'a ke zagaye kwanon
abinci.
Sai sahabbai suka tambayi manzo cewd:
Shin bamuda yawane a lokacin ?
Sai yace kunada yawa amma yawanku taron
tsintsiyane babu shara kuma nan gaba kad'an Allah
(s.w.t) zai cire kwarjinin da kuke dashi acikin
zukatan abokan ga'barku (kafirai) kuma yasanya
muku rauni.
Sai yace son duniya da qin mutuwa.
MANZON ALLAH (S.A.W) yace:
Wasu shekaru masu yaudara zasuzo wayanda
acikinsu zakaga ana qaryata mai gaskiya kuma ana
gasgata mai karya.
Mai ha'inci zaiyi zamansa cikin kwanciyar hankali,
amma za'a riga cutar mutumin kirki.
'Yan uwa yanzu a wane irin yanayi muke ciki ???
ALLAH YASA MUGAMA DA DUNIYA LAFIYA.
Share:

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate