Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

zuciyata tana son aikata sabo

tambaya-da-amsa.jpg

Malam zuciyata tanason aikata sa6o, yaya zanyi
na hanata ?

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Salam, malam a cikin zuciya ta ina jin tsoron Allah,kuma ina son bin umarnin Allah, saidai ina yawan sa’bon Allah kuma, malam inaso a taimake ni da shawara akan hakan ?

(Daga sadis Auwal).

AMSA:
-------------------------------------------------

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.To dan uwa, ina fatan zaka karanta wannan ‘kissar
da idon basira, domin zaka sami shawarar da kake bukata gata kamar haka:

Wata rana wani saurayi yaje wajen Ibrahim ‘dan Adhama, (‘daya daga cikin magabata), sai yace
masa zuciyata tana tunkuda ni zuwa sa’bo, kayi min wa’azi. Sai ya ce masa:“Idan ta kirawo ka zuwa sa’bawa Allah to ka saba masa, amma da sharuda guda biyar.
Sai saurayin ya ce fadi mujisu Sai yace:

1. Idan zaka sabawa Allah, to kabuya a wurin da bazai ganka ba, sai saurayin yace:
Tsarki ya tabbata ga Allah, yaya za’ayi na boye masa, alhalin babu abin da yake ‘buya gareshi ???Sai yace:Yanzu bakajin kunya kasa’ba masa alhali kuma yana ganinka.

2. Idan zaka sabawa Allah to karka saba masa acikin kasarsa, sai saurayin yace:
Tsarki ya tabbata ga Allah, ina zanje, alhali duka duniya tasace ???Sai yace masa:
Yanzu bakajin kunya kasa’ba masa alhali kana zaune a saman kasarsa ?

3. Idan zaka sabawa Allah to kadaina cin arzikinsa.Sai saurayin yace:Tsarki ya tabbata ga Allah, ta yaya zan rayu alhali duka ni’imomi daga gareshi suke ?Sai yace masa:
Yanzu ba kajin kunya ka sa’ba masa alhali yana ciyar da kai kuma Yana shayar dakai, Yana baka
karfi.

4. Idan ka sabawa Allah, to idan mala’iku sukazo tafiya dakai Wuta, kace bazaka tafi ba Aljanna za ka.Sai saurayin yace:Tsarki ya tabbata ga Allah ai sunfi ‘karfina, korani
zasuyi.

5. Idan ka karanta zunubanka a takardarka ranar
alkiyama kace ba kaine ka aikata suba.
Sai saurayin yace:
Tsarki ya tabbata ga Allah, ina mala’iku masu kiyayewa, sai yafashe da kuka yatafi yana maimaita
wannan Kalmar ta karshe.IN HAR KANA TUNA ‘DAYA DAGA CIKIN WADANNAN IDAN ZAKA AIKATA ZUNUBI, TO TABBAS ZAKAJI KUNYAR ALLAH.Tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki.
Ya Allah ka tsarkake mana zukatanmu daga sabo.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

shin akwai idda a kaina?

tamabyoyi.jpg

Shin akwai IDDA akaina ?

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Assalamu Alaikum.
Malam mutum ne yanada mata, sun haihu tare da
ita ‘ya’ya hudu sai ya saketa, Sai wani ya aure ta.Suna tare da shi, sai suka sami ‘ya’ya guda biyu
(2).To, wannan mijin na farko, mai ‘ya’ya hudu (4) sai
ya mutu.Sai matar take cewa “Zata fito taje gidan wancan
(mamacin) tayi IDDAH.
Yaya wannan al’amarin yakene ?

(Daga Umar Hafiz)

AMSA:

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

-------------------------------------
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.Babu abin daya hadata da wancan mamacin gameda takaba ko IDDAH. Wadannan ‘ya’yan nasu guda hudu wadanda sune
ainihin ‘ya’yan mamacin zasu tafi domin suci gado.
Amma ita kuwa babu ruwanta da wani abu nasa tunda sun rabu tun kafin ya rasu.
ALLAH SHINE MASANI.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

gyaran zuciya

tunatarwa.jpg

Domin gyaran zuciya

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Assalamun alaikum.
Allah yagafarta malam, wadanne abubuwane zanyi
domin gyara zuciyata da imanina ?Bissalam.

(daga Aminatu Farouk)

AMSA
*********************

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Hakika wannan tambayar tanada muhimmanci
sosai.Kuma tabbas babu wani abinda yake gyara zuciyar Mumini face ambaton Allah (s.w.t).Allah (s.w.t) yana cewa:''KUYI SANI CEWAR DA AMBATON ALLAH NE ZUCIYA TAKE SAMUN NUTSUWA''Zikirin Allah (SWT) shine babban abinda yake raya zuciyar mumini kamar yadda Manzon Allah (s.a.w) yake cewa:"MISALIN WANDA YAKE ZIKIRIN ALLAH DA WANDA
BAYAYI, KAMAR MISALIN RAYAYYE NE DA MATACCE".
(bukhary da Muslim).
Babu abinda yake Katangewa zuciyar Mumini daga sharrin Shaitan face zikirin Allah (swt).Shugaba (s.a.w) yana cewa:
"HAKIKA MISALIN WANNAN (DA YAKE ZIKIRIN ALLAH), KAMAR MISALIN MUTUMIN DA MAQIYA (ABOKAN GABA) SUKA KOROSHI AGUJE, HAR SAI DAYA ISO WATA KATANGA MAI QARFI, YA SHIGA YA TSARE KANSA DAGA GARESU.HAKANAN BAWA BAZAI IYA TSARE KANSA DAGA
SHAITAN BA, SAIDA ZIKIRIN ALLAH"(tirmizy ne ya ruwaitoshi akan hadisi mai lamba 2,863).Sannan babu abinda yafi tseratar da mutum daga azabar Allah, kamar zikirin Allah.Manzon Allah (s.a.w) yana cewa:
"BABU WANI AIKIN DAYAFI TSERATAR DA BIL-ADAMA DAGA AZABAR ALLAH, KAMAR ZIKIRIN
ALLAH (azza wa jalla)."(Imamu Malik ya ruwaitoshi acikin Muwatta' juz'i na 1 shafi na 211 hadisi na 492.Da kuma Imamu Ahmad acikin Musnad juz'i na 5, shafi na 293, hadisi mai lamba 22,132).Babu abinda yake gyara imanin 'Dan Adam kamar ilimi da kuma aiki dashi..
Don haka munemi ilimin addini mai amfani.Kuma muji tsoron Allah. Mu aikata ayyuka na
kwarai.Allah ka shiryar damu akan tafarki madaidaici.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

mace mai ciki

tambaya-da-amsa.jpg

Shin malam ko ya halatta mace mai ciki ta daina sallah ?

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Assalamu Alaikum
Dafatan malam yawuni lafiya.Malam don allah inaso akara mana haske akan
mene hukuncin matar datake zargin mijinta ?
Sannan malam shin ya halasta mace mai juna biyu ta daina sallah ?
Nagode.

(Daga Fateemah Muhammad).

AMSA
---------------------------------------

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.Shi Musulunci addini ne wanda ya gina al'ummarsa abisa kyautata mu'amala da yarda da juna da amincewa da kare mutuncin juna.Don hakane ma Musulunci baya yarda da duk
abinda ya zamto zargi ne, wato babu Qwararan shaidu wadanda suka tabbatar da faruwa ko
kasantuwar abin.Abinda kike zargin mijinki dashi, duk dadai ke zuciyarkita yardar miki cewar yana aikata wannan abin, to amma bakki da Qwakwarar Shaidar da zata tabbatar da zarginda kike yi masa.Yazama wajibi kicire zargi a zamanku na auratayya.

2. AMSAR TAMBAYA TA BIYU.Ba'a daukewa mai ciki sallah yazama wajibi ta kawota.Akwai aiyuka da dama na addini da ake daukewa
dan adam idan larura irin wannan tafaru akansa,amma ita sallah koda kana kwance baka iya tashi
muddin kasan a inda kake saika kawota koda jingina a bango ne.Balantana mace mai ciki wacce har takanyi wanke-wanke shara etc.Saboda haka 'yan uwa mudaina sakaci da sallah.

makomar dan kafiri jinjiri

tamabyoyi.jpg

Malam menene makomar dan kafiri jariri idan ya mutu ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Assalamu Alaikum
Malam menene makomar dan kafiri jariri idan ya
mutu ???Wai da gaske dan Al-jannah ne ???
Allah yakarawa malam lafiya.

(Daga Hafiz Lukhman).

AMSA
-----------------------------------------------

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.To malamai sunyi sabani akan yadda za’ayi da ‘ya’yan kafirai zuwa maganganu:

1. Allah zai sakasu a Aljanna, saboda basuyi aikin da Allah zaiyi musu azaba ba.

2. Akwai malaman da sukace za’ayi musu
jarrabawa ranar alkiyama.

3. Akwai wadanda suka tafi akan mayar da lamarinsu zuwa ga Allah, kada ayi musu shaida da wuta ko Aljanna, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.
“Allah ne ya san abin da sukayi nufin aikatawa”.kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai
lamba ta: 1384.

4. Akwai malaman da suka tafi akan cewa:
‘Yan wuta ne.Sai dai babban malamin nan Ibnul-kayyim ya rinjayar da Magana ta farko, wato suna Aljanna,saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi.
“Kowanne abin haihuwa ana haihiuwarsa ne akan
musulunci, iyayansa ne suke zamar dashi
bayahude ko banasare”Kuduba Sahihul Bukhari hadisi mai lamba ta :1385.
Su kuma gashi sun mutu suna yara kaga suna nan akan musuluncinsu.Sannan Allah yana cewa:“Bamu kasance munayin azaba ba, harsai mun aiko manzo” (Suratul Isra’i aya ta: 15).kaga su kuma basu balaga ba, balle su fahimci
abinda mazanni sukazo dashi, sannan kuma suba azzalumai bane, azabar Allah kuma tana tabbata ne
ga azzalumai.Don neman Karin bayan kuduba:(Darikul hijratain :387).Allah Shine mafi sani.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

zuciyata tana son aikata sabo

tambaya-da-amsa.jpg

Malam zuciyata tanason aikata sa6o, yaya zanyi
na hanata ?

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Salam, malam a cikin zuciya ta ina jin tsoron Allah,kuma ina son bin umarnin Allah, saidai ina yawan sa’bon Allah kuma, malam inaso a taimake ni da shawara akan hakan ?

(Daga sadis Auwal).

AMSA:
-------------------------------------------------

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.To dan uwa, ina fatan zaka karanta wannan ‘kissar
da idon basira, domin zaka sami shawarar da kake bukata gata kamar haka:

Wata rana wani saurayi yaje wajen Ibrahim ‘dan Adhama, (‘daya daga cikin magabata), sai yace
masa zuciyata tana tunkuda ni zuwa sa’bo, kayi min wa’azi. Sai ya ce masa:“Idan ta kirawo ka zuwa sa’bawa Allah to ka saba masa, amma da sharuda guda biyar.
Sai saurayin ya ce fadi mujisu Sai yace:

1. Idan zaka sabawa Allah, to kabuya a wurin da bazai ganka ba, sai saurayin yace:
Tsarki ya tabbata ga Allah, yaya za’ayi na boye masa, alhalin babu abin da yake ‘buya gareshi ???Sai yace:Yanzu bakajin kunya kasa’ba masa alhali kuma yana ganinka.

2. Idan zaka sabawa Allah to karka saba masa acikin kasarsa, sai saurayin yace:
Tsarki ya tabbata ga Allah, ina zanje, alhali duka duniya tasace ???Sai yace masa:
Yanzu bakajin kunya kasa’ba masa alhali kana zaune a saman kasarsa ?

3. Idan zaka sabawa Allah to kadaina cin arzikinsa.Sai saurayin yace:Tsarki ya tabbata ga Allah, ta yaya zan rayu alhali duka ni’imomi daga gareshi suke ?Sai yace masa:
Yanzu ba kajin kunya ka sa’ba masa alhali yana ciyar da kai kuma Yana shayar dakai, Yana baka
karfi.

4. Idan ka sabawa Allah, to idan mala’iku sukazo tafiya dakai Wuta, kace bazaka tafi ba Aljanna za ka.Sai saurayin yace:Tsarki ya tabbata ga Allah ai sunfi ‘karfina, korani
zasuyi.

5. Idan ka karanta zunubanka a takardarka ranar
alkiyama kace ba kaine ka aikata suba.
Sai saurayin yace:
Tsarki ya tabbata ga Allah, ina mala’iku masu kiyayewa, sai yafashe da kuka yatafi yana maimaita
wannan Kalmar ta karshe.IN HAR KANA TUNA ‘DAYA DAGA CIKIN WADANNAN IDAN ZAKA AIKATA ZUNUBI, TO TABBAS ZAKAJI KUNYAR ALLAH.Tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki.
Ya Allah ka tsarkake mana zukatanmu daga sabo.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

tambaya

tamabyoyi.jpg

Shin malam ko ya halatta mace mai ciki ta daina sallah ?

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Assalamu Alaikum
Dafatan malam yawuni lafiya.Malam don allah inaso akara mana haske akan
mene hukuncin matar datake zargin mijinta ?
Sannan malam shin ya halasta mace mai juna biyu ta daina sallah ?
Nagode.

(Daga Fateemah Muhammad).

AMSA
---------------------------------------

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.Shi Musulunci addini ne wanda ya gina al'ummarsa abisa kyautata mu'amala da yarda da juna da amincewa da kare mutuncin juna.Don hakane ma Musulunci baya yarda da duk
abinda ya zamto zargi ne, wato babu Qwararan shaidu wadanda suka tabbatar da faruwa ko
kasantuwar abin.Abinda kike zargin mijinki dashi, duk dadai ke zuciyarkita yardar miki cewar yana aikata wannan abin, to amma bakki da Qwakwarar Shaidar da zata tabbatar da zarginda kike yi masa.Yazama wajibi kicire zargi a zamanku na auratayya.

2. AMSAR TAMBAYA TA BIYU.Ba'a daukewa mai ciki sallah yazama wajibi ta kawota.Akwai aiyuka da dama na addini da ake daukewa
dan adam idan larura irin wannan tafaru akansa,amma ita sallah koda kana kwance baka iya tashi
muddin kasan a inda kake saika kawota koda jingina a bango ne.Balantana mace mai ciki wacce har takanyi wanke-wanke shara etc.Saboda haka 'yan uwa mudaina sakaci da sallah.
ALLAH SHINE MASANI.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

adduoin sabbin ma,aurata

tambaya-da-amsa.jpg

Addu'o'i domin sababbin ma'aurata.

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Assalamu alaikum.
Dan Allah malam wacce addu'ar mutum zai karanta idan yayi sabon aure ?Kuma wacce addu'ar zai karanta idan zai sadu da matarsa ?

(Daga Mukhtar Isyaku B Musawa).

AMSA
--------------------------------

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.Idan mutum yayi sabon Aure anaso yadora hannunsa, akan goshin amaryarsa ya karanta
wannan addu'a kamar haka:''ALLAHUMMA INNY AS'ALUKA MIN KHAIRIHA WA KHAIRI MA JABALTAHA ALAYYA.WA A'UZU BIKA MIN SHARRIHA WA SHARRI MA JABALTAHA ALAYYA.

««FASSARA»»
Ya Allah ina roqonka Alkhairinta, da Alkhairin abin
daka dabi'antar da ita akansa.Sannan ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin abin daka dabi'antar dashi akanta.Addu'ar Saduwa da iyali kuma itace kamar haka:''BISMILLAHI, ALLAHUMMA JANNIB'NASH
SHAIDANA WA JANNIBISH-SHAIDANA MA
RAZAQTANA.
««FASSARA»»
Da sunan Allah, Ya Allah ka nisantar da shaytan daga garemu, sannan ka nisantar da shaidan daga abin daka azurtamu dashi.
Za'a karanta wannan addu'arne kafin afara
saduwar.ALLAH SHINE MASANI.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

mallam koh zan iya sallah da wandon

tamabyoyi.jpg

Malam ko zan iyayin sallah da wandon ?

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Assalamu Alaikum.
Malam Tambayata itace mutum ne yake da wando guda biyu a jikinsa da dan karami da kuma babba to sai mazi ko maniyyi ya zuba shin zai iya sallah dana wajen ??

(Daga Jamilu A Aliyu).
AMSA
-----

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.Eh idan maniyine zai iya sallah dashi babu laifi.Saboda hadisin da nana Aisha (R.A) take cewa:Na kasance ina sanya farcena na kankare
bushashshen maniyyi a jikin tufan Annabi (s.a.w).Kaga da najasane Annabi bazai barshi yabushe
ajikin kayansa ba. Amma idan maziyyine yanada kyau a yayyafa ruwa kafin ayi sallah da tufafin.ALLAH SHINE MASANI.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka

Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate