Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

KA TABAYIN ZINA ???

KA TABAYIN ZINA ???


DAGA ZAUREN


HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .KA TABAYIN ZINA ???
Tsaya kuji irin mummunan Bala'in da zina ke haifarwa.
Zina tana cikin manyan laifuffuka, wanda dukkan shariun da Allah ta'ala ya saukar sun hadu akan
haramcin zina.Al kur'ani mai girma da Sunnar Annabi (s.a.w) da dukkan Malamai sun hadu akan haramcin zina.Qofofin zina guda biyar ne kamar haka:

1- Kallo zuwaga Abinda Allah ya Haramta.
2- Shigar batsa
3- Kalaman Batsa
4- kebancewa da matar daba muharrama ba,
5- Sha'awa Mai karfi babu aure Allah taala yace: "kada ku kusanci zina"Manzon Allah (s.a.w) yace:
Mai zina ba zaiyi zina ba, yayin da yake zina, sai an cire masa imani.Abdulllah Dan Mas'ud Ra yace:Duk Al'ummar da take zina, ta jawo wa kanta
fushin Allah, da halaka.Musulunci yayi umarni da tsare abubuwa guda shida sune kamar haka:
1-Addini.
2-Dukiya
3-Rayuka
4-Hankali
5-Mutunci
6-Nasaba
Amma zina ita kadai, tana rusa wadannan duka. Hukuncin mazinaci, mai aure kisa ta hanyar jifa.
Saurayi mara aure Bulala dari da daurin shekara.Ana tabbatar da zina ta hanya uku.

1-Shaidu guda hudu.
2-Mutun yayi ikirari da kansa.r
3-Samun mace da ciki, babu aure, ko shubha.
Bisa sharudda da aka sanyawa ko wanne.
Zina wata babbar musiface da bala'i da dukkan sharri, datake ruguza al'umma, take wargaza iyali, take tarwatsa gari, take rushe mutunci, take jawo karayar tattalin arziki, da fatara, da tsiya, dabannoba, acikin rayuwar dai dai ku, da gidaje, da
unguwanni, da gururuwa, da kasashe, da duniya baki daya.Zina itace cikakkiyar fitsara, a cikin zina ake
samun dukkan sharri kamar haka:
1- Raunin Addini
2- Raunin Akida
3-Karancin Imani
4- Rashin kunya
5- Rashin kishi
6- Rashin mutunci
7- Rashin kwarjini
8- Rashin hasken fuska
9- Duhun zuciya
10- Rashin kima
11- Rashin Nagarta
12-Rashin Nutsuwa
13- Rashin Amana
14- Fushin Allah
15- cikawa babu imani
16- Azabar Allah
Allah ya tsare mu da zuriyar mu, da dukkan
al'ummar musulmi daga afkawa bala'in zina.Wadanda sukeyi Allah ya shiryesu.


www.hanyantsira.mywapblog.com


whatsapp
09039016969
07038774163


Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA


Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate

Blog Archive