Malam zuciyata tanason aikata sa6o, yaya zanyi
na hanata ?
DAGA ZAUREN
HANYAN***TSIRA
Salam, malam a cikin zuciya ta ina jin tsoron Allah,kuma ina son bin umarnin Allah, saidai ina yawan sa’bon Allah kuma, malam inaso a taimake ni da shawara akan hakan ?
(Daga sadis Auwal).
AMSA:
-------------------------------------------------
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.To dan uwa, ina fatan zaka karanta wannan ‘kissar
da idon basira, domin zaka sami shawarar da kake bukata gata kamar haka:
Wata rana wani saurayi yaje wajen Ibrahim ‘dan Adhama, (‘daya daga cikin magabata), sai yace
masa zuciyata tana tunkuda ni zuwa sa’bo, kayi min wa’azi. Sai ya ce masa:“Idan ta kirawo ka zuwa sa’bawa Allah to ka saba masa, amma da sharuda guda biyar.
Sai saurayin ya ce fadi mujisu Sai yace:
1. Idan zaka sabawa Allah, to kabuya a wurin da bazai ganka ba, sai saurayin yace:
Tsarki ya tabbata ga Allah, yaya za’ayi na boye masa, alhalin babu abin da yake ‘buya gareshi ???Sai yace:Yanzu bakajin kunya kasa’ba masa alhali kuma yana ganinka.
2. Idan zaka sabawa Allah to karka saba masa acikin kasarsa, sai saurayin yace:
Tsarki ya tabbata ga Allah, ina zanje, alhali duka duniya tasace ???Sai yace masa:
Yanzu bakajin kunya kasa’ba masa alhali kana zaune a saman kasarsa ?
3. Idan zaka sabawa Allah to kadaina cin arzikinsa.Sai saurayin yace:Tsarki ya tabbata ga Allah, ta yaya zan rayu alhali duka ni’imomi daga gareshi suke ?Sai yace masa:
Yanzu ba kajin kunya ka sa’ba masa alhali yana ciyar da kai kuma Yana shayar dakai, Yana baka
karfi.
4. Idan ka sabawa Allah, to idan mala’iku sukazo tafiya dakai Wuta, kace bazaka tafi ba Aljanna za ka.Sai saurayin yace:Tsarki ya tabbata ga Allah ai sunfi ‘karfina, korani
zasuyi.
5. Idan ka karanta zunubanka a takardarka ranar
alkiyama kace ba kaine ka aikata suba.
Sai saurayin yace:
Tsarki ya tabbata ga Allah, ina mala’iku masu kiyayewa, sai yafashe da kuka yatafi yana maimaita
wannan Kalmar ta karshe.IN HAR KANA TUNA ‘DAYA DAGA CIKIN WADANNAN IDAN ZAKA AIKATA ZUNUBI, TO TABBAS ZAKAJI KUNYAR ALLAH.Tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki.
Ya Allah ka tsarkake mana zukatanmu daga sabo.
www.hanyantsira.mywapblog.com
09039016969
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته