Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

KOZAN IYA QARA GASHI, SABODA MIJINA ???

tamabyoyi.jpgKOZAN IYA QARA GASHI, SABODA MIJINA ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

KOZAN IYA QARA GASHI, SABODA MIJINA ???
Malam nayi rashin lafiya kaina ya kwakuye, mijina
yana bakin ciki, idan yaga kaina.Kozan iya kara gashi, don zaman auranmu ya kara
dadi ??

AMSA.

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
==================
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.To 'yar uwa wata mace taje wajen Annabi (s.a.w)
tabashi labari cewa:
'Yarta tayi rashin lafiya gashin kanta yazube, kuma gashi mijinta ya umarceta data kara mata gashi,shin zata iya Qarawa ???.

Sai Annabi (s.a.w) yace mata:A'a, saboda an la'anci masu Qara gashi"Bukhari ne ya rawaito a hadisi mai lamba ta:4831.
Hadisin yana nuna cewa:Baya halatta mace taqara gashi, koda kuwa mijinta
ne ya umarceta.Saboda hakan zaisa tashiga tsinuwar Allah.
Allah shine mafi sani.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"

وعليكم السلام ورحمة الله وبركاته
Share:

Shin malam ya halatta ayiwa kabari sumunti ?

Shin malam ya halatta ayiwa kabari sumunti ?
tamabyoyi.jpg

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Assalamu alaikum
Malam wai ya halatta asawa kabari sumunti ?

Daga Salihu Kankia.
AMSA:-

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
-----
DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
A’a kasa mai danko kadai ake iya kwa6awa a
sanya, domin kada kasa ta rufeshi.Amma sanya sumunti makarufine.sannan kuma, sanya itatuwa, yafi a sanya tukwane.
Saboda sanya tukwane zai hana wata rana a sanya wani a wurin saboda za ayi ta ganin kushewar kabarin, nasa na farko.
Domin tukunya bata lalacewa da wuri, sai tayi samada shekaru dari.Amma itace nada saurin rubewa, ya lalace (ya6ace
fiye da sauri) akan tukunya.WALLAHU A'ALAM. R's

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

KAYI SHAWARA DA KANKA, SHIMA BA KARAMAR DABARA BACE-

tunatarwa.jpgKAYI SHAWARA DA KANKA, SHIMA BA
KARAMAR DABARA BACE-

01

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Bazan taba mantawa da lokacin da ina dan
shekara 8 a duniya ba, na kanyi tunanin duniya tawace, a lokacin da nakai shekara 15, sai na fara
tunanin ya zan in mulki duniya nima na zama daya daga cikin muhimman mutanenta. Sanda nakai shekaru 20, sai na fara tunanin ya zan zama babban attajiri a duniya na mallaki ababen 'kawa nima kamar kowane mai sukuni. Lokacin dana cika dan shekaru 25, sai na fara tunanin samun soyayyar mutane. Dana kai shekaru 40 a duniya
sai na fra tunanin neman taimakon al'umma.Tabbas nasan akwana atashi wata rana sai na
bukaci mutuwa da kaina muddin shekaru sun ja.Idan zaku lura da kyau, a duk tsawon wadannan shekaru na karar da sune akan son mallakar abubuwa da dama a lokuta maban-banta. Amma
abinda nafiso shine na zamo cikin farin ciki. Amma babu shakka ina tunanin mafi alherin hanyar
cimma buri a rayuwa shine sauraron shawarar
mutane.
Wannan yasa alokacin da zan shiga jami'a naso
ace na karanta fannin koyon malumta wato
(Education) don in son nan gaba na zama
kwararren malamin makaranta, amma a lokaci daya
mutane sukayo mini caaa! Me zanyi da wata
koyarwa, in karanci Engineering ko medicine, sune
kwasa-kwasai na rayuwa masu ci. Na dauki
shawararsu na zabi Engineering. Bayan
kasancewata a jami'a, na kasa samun tallafin
karatu daga kowane daya daga cikinsu, matsalolin
rayuwa suka rufar ma karatu na, dole tasa na gudu
daga jami'a saboda karatun bazai yiwwu ba.
Bayan na bar jami'a...... Mu hadu a 02

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

KAYI SHAWARA DA KANKA, SHIMA BA KARAMAR DABARA BACE-02

KAYI SHAWARA DA KANKA, SHIMA BA KARAMAR DABARA BACE-02
tunatarwa.jpg
DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Bayan na bar jami'a, wadan nan mutane dai suka
sake ce mini ya za ai na gudu na gudu daga
jami'a, ina laifin ace ko malumta na koya
maimakon na barta duka. Ina laifin ace ko malamin
makaranta na zama tunda ban zama engineer ba.
Haka dai har nakai shekaru 28 mutanen nan suka
matsa mini sai nayi.....03

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

KAYI SHAWARA DA KANKA, SHIMA BA KARAMAR DABARA BACE 03

tunatarwa.jpgKAYI SHAWARA DA KANKA, SHIMA BA KARAMAR DABARA BACE

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Haka da nakai shekaru 28, mutanen nan dai suka matsa mini sai nayi aure. Ni nasan halin da nake ciki amma suk takuramini lokacina yayi kar in
zama tuzuru, nasan bani da wata sana'a tsayayya,amma suka addaban dole na kukuta nayi aure,
nabi shawararsu, amma ko da sau daya ba wanda ya taba taimaka maini da komai. Ina ji ina gani
abin cefane da ciyar da iyali na ya gagara dole muka rabu da matar. Haka mutanen nan suka dunga zunde na suna zagi na na kasa rike mata
daya.Lokacin da ina dan shekaru 40 ne na samu wata kwangila, ta sanadiyyar wani abokina ta Naira Milliyan 10. Suna na ya baje gari cewa na samu babbar kwangila mai tsoka. Nan da nan abokai da dangi, wadan nan mutanen dai da suke bani shawara suka yo kaina, kowa da irin tashi matsalar, sunz son rance da buktunsu daban-daban. Cikin mako daya (sati daya) na rabar musu da duka kudin nan da alkawarin zasu biya a cikin dan kankanin lokaci amma suka gaza cika alkawarinsu. Dole tasa kwangila ta bata kammalu ba aka tasa keyata zuwa gidan yarisuna kallo na
sai da na kwashe tsawon shekaru 6 sannan na samu sukunin fitowa. Lokacin dana fito dukkan wadannan mutane ban same su a kusa dani ba duk sun gujeni.Tabbas akwai.....04

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA
Share:

Maganin mai hassada

Maganin mai hassada

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Akaramakallah, inada wani aboki na kud-da-kud,saidai bayaso yaga nafishi da wani abu, idan na samu wani abin alkairi, saiya aibanta abin ta yadda
mutane bazasu kimanta shiba, abin yana damuna,shine nakeso a taimaka min da hanyoyin da zan samu kariya daga mahassada ?
(Daga Salihu Ahmad).

AMSA
--------------------
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

To dan’uwa, ya kamata kasan cewa babu yadda zakayi ka wofantu daga mahassada, domin duk wanda Allah yayi masa ni’ima, dole sai yasamu mahassada, saidai duk da haka akwai hanyoyin da
malamai suka fada wadanda suke hana hassadar yin tasiri gasu kamar haka:

1. Neman tsari awajen Allah daga sharrinsa.

2. Tsoron Allah da kiyaye umarninsa, duk wanda ya kiyaye Allah, to Allah zai kiyaye shi.

3. Yin hakuri akan abokin gabansa, kar yace zai rama mummunan abinda yayi masa, domin inhar bai rama abinda akayi masa ba, to tabbas Allah zai rama masa.

4. Karfin dogaro zuwa ga Allah, Allah yana cewa a cikin (Suratu Addalak Ayah ta 3) cewa:“Duk wanda ya dogara ga Allah, to ya ishe shi”.Idan ka dogara ga Allah sharrin mahassadi bazai cutar da kai ba, ko da kuwa ka ga wani abu da yake na cutarwa ne to karshensa zai zama alkairi.

5. Fuskantar Allah Madaukakin Sarki da tsarkake aiki zuwa gare Shi, da yawan ambatonSa.

6. Tuba daga zunubai, domin ba za’a dora maka wani yadinga cutar da kai ba, sai idan akwai wani
zunubi daka aikata, kasan zunubin ko bakasan shiba.

7. Yin sadaka da kyautatawa iya abinda zai iya,saboda da wuya Allah yadora mai hassada akan wanda yake kyautatawa mutane.

8. Kyautatawa wanda yakeyi maka hassadar, saidai wannan yana da tsananin wahala.Idan har ka kiyaye wadannan Allah zai taimaka maka.
Don neman karin bayani kuduba:
(Bada’iul fawa’id na Ibn Qayyim, 2\463).
Allah ka rabamu da rigar hassada.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

LABARIN WANI MAZINACI

kissa.jpgLABARIN WANI MAZINA CI

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

A daure a karanta akwai darasi babba

ZINA BASHI CE!

'Yan uwana Maza da Mata akwai wata Qissa da zan Bamu, mai matu'kar amfani acikin wannan zamanin namu, ma'abocin Qissar, wanda abin yafaru dashi,shine yake bayar da Labarin yadda al'amarin ya kansace dashi.Labarin yana cikin wata Mujallah (Magazine News
paper) ta 'kasashen Larabawa, kuma cikin harshen Larabcine, amma zanyi 'kokari wajen fassarawa gwargwadon yadda
na fahimta, saboda nima din ba gwani bane a harshen Larabci.gata kamar haka.......

Mutumin yana cewa:
A lokacin da ina saurayina nasami Admission a Jami'a, bayan nafara karatunne sai na had'u da wata Budurwa (Girl-friend) acikin Jami'ar tamu muka 'kulla soyayya da ita tamkar ma'aurata, hardai tasami juna biyu, (yai mata ciki kenan).Da iyayenta suka gane sai suka tambayeta wanda yayi mata ciki sai tace nine nayi mata.Sai yayanta yataho nema na a fusace yana nufin
d'aukar mataki a kaina, yana zuwa saiya tambayeni kaine kayima qanwata ciki ko ???Sai na amsa masa da cewa:
Wace ce, ni banma ta6a ganinta ba a Rayuwata,ban santa ba.Sakamakon rashin hujjar da zasu kamani da ita dole suka 'kyaleni.Bayan tsawon zamani, wata rana nadawo gida saina tarar da Mahaifiyata a dur'kushe tana tana
kuka.Saina dur Qusa na daga ta sai tasake yanke jiki tafad'i 'kasa har sau uku saina tambayeta a karo
na qarshe:"Ya Ummi Man ladzhi haddath (me ya faru mama)?
Sai tace:Qanwarkace gata can wani yayi mata ciki!Yace sai naji kamar an sokeni da mashi, hankalina yatashi na tasa 'keyarta muka tafi wurin wanda tace yai mata cikin.Da mukaje sai yafada min maganar data tayarmin da hankali.
Bawata magana bace face wadda na fadama yayan yarinyar da nayi
ma ciki a baya.(Ban santa ba, banma ta6a ganinta ba)!Bayan zamani yaqara yin nisa sai nayi nufin yin
aure nafara neman aure nasamu matar da nake so kuma akasa lokaci akayi biki, ranar farko dana tare da ita saina sameta ba a matsayin budurwa ba.
Ma'ana tariga tayi zina, tuni hankalina yatashi.Saita fadamin wata magana mai shiga rai."Don Allah karufa min asiri, ka suturta al'amarina
kaima Allah sai ya suturta al'amarinka."
Yace sai nace acikin zuciyata:Ya Rabby yakfy, yakfy.(Ma-ana Ya Mahalliccina ya isa haka ya isa haka).•Ya cigaba da cewa:Bayan mun kwashe shekaru da matata sai muka
haifi 'ya mace kyakkyawa gata da haske kamar
wata.A lokacin da tacika shekaru 6 a duniya sai gata wata rana tashigo gida tana kuka.Me yafaru ?
Ai me gadine yayi mata fyad'e!INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN
Aljazaa'u min jinsil amal!Wallahi duk tsiyar da kake sheqewa idan Allah
ta'ala yaga dama sai ya hada maka zafi kan zafi irin wannan!Yanzu kunga shi ya lalata 'yar mutane guda daya
tak shi kuma an lalata masa guda uku! Yaa Allah ka Qara karemu daga zina, masuyi kuma Allah ka shiryasu.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

Maganin mai hassada

tunatarwa.jpgMaganin mai hassada

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Akaramakallah, inada wani aboki na kud-da-kud,saidai bayaso yaga nafishi da wani abu, idan na samu wani abin alkairi, saiya aibanta abin ta yadda
mutane bazasu kimanta shiba, abin yana damuna,shine nakeso a taimaka min da hanyoyin da zan samu kariya daga mahassada ?
(Daga Salihu Ahmad).

AMSA
--------------------
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

To dan’uwa, ya kamata kasan cewa babu yadda zakayi ka wofantu daga mahassada, domin duk wanda Allah yayi masa ni’ima, dole sai yasamu mahassada, saidai duk da haka akwai hanyoyin da
malamai suka fada wadanda suke hana hassadar yin tasiri gasu kamar haka:

1. Neman tsari awajen Allah daga sharrinsa.

2. Tsoron Allah da kiyaye umarninsa, duk wanda ya kiyaye Allah, to Allah zai kiyaye shi.

3. Yin hakuri akan abokin gabansa, kar yace zai rama mummunan abinda yayi masa, domin inhar bai rama abinda akayi masa ba, to tabbas Allah zai rama masa.

4. Karfin dogaro zuwa ga Allah, Allah yana cewa a cikin (Suratu Addalak Ayah ta 3) cewa:“Duk wanda ya dogara ga Allah, to ya ishe shi”.Idan ka dogara ga Allah sharrin mahassadi bazai cutar da kai ba, ko da kuwa ka ga wani abu da yake na cutarwa ne to karshensa zai zama alkairi.

5. Fuskantar Allah Madaukakin Sarki da tsarkake aiki zuwa gare Shi, da yawan ambatonSa.

6. Tuba daga zunubai, domin ba za’a dora maka wani yadinga cutar da kai ba, sai idan akwai wani
zunubi daka aikata, kasan zunubin ko bakasan shiba.

7. Yin sadaka da kyautatawa iya abinda zai iya,saboda da wuya Allah yadora mai hassada akan wanda yake kyautatawa mutane.

8. Kyautatawa wanda yakeyi maka hassadar, saidai wannan yana da tsananin wahala.Idan har ka kiyaye wadannan Allah zai taimaka maka.
Don neman karin bayani kuduba:
(Bada’iul fawa’id na Ibn Qayyim, 2\463).
Allah ka rabamu da rigar hassada.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

FALALA

tunatarwa.jpgFALALA ASHIRIN (20) TA WATAN RAMADAN

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

FALALA ASHIRIN (20) TA WATAN RAMADAN.

1.-Acikin sa aka saukar da Alkurani mai girma Bakara ayata185.

2.-Dukkan littafan Allah mai girma, acikin sa aka saukar dasu,takardun Annabi Ibrahim a daran farko na watan, Attaurar Annabi Musa a ranar 6 ga watan, Injila ta Annabi Isa 13 ga watan, Alkur'anin Annabi Muhammad (s.a.w) a ranar 24 ga watan,Musnad Ahmad, sheikh Albaniy ya ingantashi.

3.-Ana bude Kofofin Aljannah a cikin watan.

4,-Ana rufe kofofin wuta.

5,;Ana daure kangararrun shedanu.

6,-Ana bude kofofin Rahma.

7.-Ana bude kofofin sama.

8.-Mai kira yana kira, ya mai neman alkhairi
gabato, ya mai neman sharri, kayi nisa.

9.-A kowanne dare, Allah yana yanta bayi daga wuta.

10,-A cikin watan akwai daren lailatul kadri wanda yafi wata dubu.

11.-Ana kankare zunubin shekara, Annabi (s.a.w)yace:Daga Ramadan Zuwa Ramadan ana kankare zanubi duka, mutukar an nisaci kaba'ira.

12.-Ana durmuza hancin, Duk wanda Ramadana yakama harya wuce baiyi aikin da za'ayi masaRahma ba.

13.-Umra acikin watan Ramadan daidai yake da aikin hajji tareda Annabi (s.a.w) a wajen lada.

14.-Watan da akafi shiga I'itikaf, a goman karshe.

15.-Watan da ake amsa Addu'a.

16. Watan da akeson yawaita Karatun Alkur'ani mai girma, akalla sauka hudu a duk sati daya.

17.-Watan Alkhairi da kyauta da ciyarwa, da samun dumbin lada, duk wanda ya ciyar da mai azumi,zai kara samun lada kamar yayi azumi.

18.-Watan da akafi yawan kiyamul laili da tarawih da Tahujjud da Asham, don kara kusanci da Allah.

19.-Watan neman nasara akan makiya, Sahabbai sukanyi amfani da watan Ramadan, wajen addua mai tsanani akan makiya.

20,-watan sada zumunci, da karfafa, yan uwantaka ta musulunci.Allah ka kaimu wani Ramadan, da imani da son Allah da Manzonsa.Sannan ka karbi ibadun mu kayafe mana.Ya Hayyu Ya Qayyum.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

Bushara da watan Ramadan

tunatarwa.jpgtambaya-da-amsa.jpgushara da watan Ramadan

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

TAMBAYA ???

WANE IRIN ALBISHIR MANZON ALLAH (S.A.W) YAKE YIWA SAHABBANSA KAFIN WATAN AZUMIN RAMADAN ???

AMSA
-------------

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Manzon Allah (S.A.W.) ya kasance yana yiwa
sahabbansa bushara zuwan watan Azumin
Ramadan yana basu labarin cewar:Acikin watan Ramadan ana bude kofofin Rahama
da kofofin Aljanna,kuma ana rufe Jahannama,sannan ana daure shaidanu,kamar yadda yazo a hadisin Abi Huraira(Kuduba Sahihul bukhari, hadisi mai lamba1899).

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

MENENE HUKUNCIN WANDA YAHAU JIRGIN SAMA DAGA KASAR SA, RANA TA KUSA FADUWA,AMMA BAYAN YATASHI SAI YARINKA GANIN RANA ???

tambaya-da-amsa.jpgMENENE HUKUNCIN WANDA YAHAU JIRGIN SAMA DAGA KASAR SA, RANA TA KUSA FADUWA,AMMA
BAYAN YATASHI SAI YARINKA GANIN RANA ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

TAMBAYA ???

MENENE HUKUNCIN WANDA YAHAU JIRGIN SAMA
DAGA KASAR SA, RANA TA KUSA FADUWA, AMMA BAYAN YATASHI SAI YARINKA GANIN RANA ???
AMSA
-------------------
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Bazai buda baki ba har sai rana tafadi a idanunsa.Hakama kuma idan yatashi akwai sauran rana a
kasarsa amma sai yashiga wani garin wanda yanayin kasarsu ya sabawa na kasarsa.Ma'ana su a wurinsu rana tafadi, to sai yayi buda baki tare dasu.Domin hadisi ya tabbata daga Abu Umamata Albahiliy yace:Naji manzon Allah (S.A.W) yana cewa:"Naji sauti mai tsanani a bayan wani dutse sai na Tambaya wannan wane irin ihu ne ???Sai akace kukan wadanda ake yiwa azabane a cikin wuta domin suna yin buda baki kafin rana tafadi".
Anan ma'ana tunda yana ganin rana to a wurinsa rana bata fadiba kenan.Kuma Allah (S.W.T) yana cewa:THUMMA ATIMMUS SIYAMA ILAL-LAILI"Ma'ana
Sannan kucika azumi izuwa dare"

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

FALALAR WATAN AZUMIN RAMADAN DA IRIN ROMON DA YAKE CIKINSA.

tamabyoyi.jpgFALALAR WATAN AZUMIN RAMADAN DA IRIN ROMON DA YAKE CIKINSA.

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

FALALAR WATAN AZUMIN RAMADAN DA IRIN ROMON DA YAKE CIKINSA.

TAMBAYA ???

MENENE FALALAR WATAN AZUMIN RAMADAN ???

AMSA
------------------------------------

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Azumin Ramadan yanada falaloli da yawa.Daga cikin falalar azumin sun hada da:-

1. Yana kankare zunubin mutum kamar yadda yazo a hadisin Khuzaifah (R.A.) Yace
Manzon Allah {S.A.W} yace:"Fitinar mutum acikin iyalansa, da dukiyarsa ko makwabcinsa sallah da azumi da sadaka suna kankaresu (Bukhari).

2. Yazo a hadisai da dama cewa:Dukkan aikin Dan Adam nasane Malaikune suke rubuta shi, amma azumi wannan na Allah ne Shi Yake sakawa wanda yayi shi (hadisin ya tabbata
acikin targhib wattarhib, juz'I na farko shafi na 75).

3. Hadisi kuma ya tabbata daga Jabir dan Abdullahi(R.A.) daga Manzon Allah {S.A.W.} cewar:Azumi garkuwane da dan Adam zaiyi garkuwa
dashi daga wuta.

3. Sannan hadisi ya tabbata daga Mu'azu dan Jabal (R.A.) cewa:
Hakika Manzon Allah {S.A.W.} yace dashi shin bazan nuna maka kofofin alheriba ?Sai yace na'am ya Rasulullah.Sai yace azumi garkuwane.

4. Sannan akwai hadisin Abi Umamata (R.A.) yace:"Nacewa Manzon Allah (s.a.w) ka umarceni da wani aiki da Allah Zai amfanar dani dashi sai yace ka lizimci azumi, domin babu kamarsa"
(dukkan wadanna hadisai sun tabbata a targhib, tahakikin Sheikh Albani juzu'I na farko shafi na 578).

6. Azumi kuma shine sababin tsoron Allah.

7. A lokacin azumin Ramadan ana bude kofofin Aljanna, kuma ana kulle kofofin Jahannama sannan
a daure shaidanu kamar yadda ya tabbata a hadisin Abi Huraira.(Kuduba Sahihul Bukhari 1899).

8. Hadisi ya tabbata wanda Imam Tirmizi ya ruwaito cewar Manzon Allah {S.A.W.} yace:"Warin bakin mai azumi yafi kamshi fiye da turaren Al-miski a wurin Allah.Hadisine sahihi.

9. Sannan wani hadisin ya tabbata daga Sahl bin Sa'ad (R.A) daga Manzon Allah {S.A.W.) yace:
Acikin Aljanna akwai wata kofa ana kiranta
Rayyanu, masu azumi zasu shigeta ranar tashin kiyama, babu wanda zai shigeta sai su.Idan sun shiga sai a kulleta babu wanda zai sake shiga(Kuduba Sahihul Bukhari 1896).
Tirmizi yakara bayani a cikin riwayarsa cewar wanda ya shigeta bazaiji kishin ruwaba (Qishirwa
ba) har abada.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

AZUMI A SHARI A

tambaya-da-amsa.jpgMENENE MAANAR AZUMI A SHARI'A ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

TAMBAYA ???
MENENE MAANAR AZUMI A SHARI'A ???

AMSA
-----------------------------------------

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Maanar azumi a Sharia shine kamewa daga dukkan abubuwan da suke bata azumi kamar ci da sha, jimaI da sauransu daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana da niyyar bautawa Allah.

TAMBAYA ???
MENENE DALILIN WAJIBCIN AZUMI ?
AMSA
-----
Daliln wajibcin azumi shine fadin Allah Madaukakir Sarki cewa:Yaku wadanda kukayi imani an wajabta muku yin
azumi kamar yadda aka wajabtawa wadanda suka
gabaceku ko kunji tsoron Allah."Kwanakine kididdigaggu.Kuma hadisin daya gabata na Abi Huraira ya nuna
wajibcin Azumi, domin Manzon Allah (S.A.W.)
yace:Kuyi azumi idan kun ganshi.Wannan kuwa umarni ne.ALLAH SHINE MAFI SANI..

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

SU WANENE AZUMI YA WAJABTA A GARESU ???

tambaya-da-amsa.jpgSU WANENE AZUMI YA WAJABTA A GARESU ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

TAMBAYA ???
SU WANENE AZUMI YA WAJABTA A GARESU ???

AMSA
-----------------------------
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Azumin Ramadan ya wajabta akan dukkan Musulmi baligi mai hankali kuma wanda yake da ikon yi,sannan mazaunin gida ba matafiyaba.Amma azumi baya wajaba akan wadannan mutane kamar haka:

Kafiri:
Azumi baya wajaba akansa, hakanan ramuwa bata wajaba a kansa idan ya musulunta a gaba.

Karamin Yaro wanda bai balagaba.
Amma za'a umarceshi domin ya saba kamar yadda magabata suke yiwa yayansu.

Mahaukaci:
Azumi bai wajaba a kansa ba.Dalili kuwa shine:Manzon Allah yace an dauke alkalami akan mutum
uku wanda mahaukaci da yaro na cikin mutum
ukun daya ambata, saboda haka idan mahaukaci sai yarama azumi to yaro ma kenan zai rama
azumin da yasha idan ya balaga.Hakanan mai bacci da yayi jimaI saboda haka
malaman da sukace mahaukaci yarama azumi basu da wata madogara daga Alkuani ko maganar
Manzon Allah (S.A.W.).

Wanda ya gaza yin azumi saboda tsufa zai sha azumi kuma bazai rama ba sai dai zai ciyar.

Mara lafiya wanda bazai iya azumi ba to shi zai rama bayan ya warke.Amma cutar da ake tabbatar bazata warke ba, to wannan ma zai rika ciyarwa.

Matafiyi:Azumi bai wajaba a kansa ba amma zai rama.

Mai haila ko jinin biki:Baza suyi azumi ba, amma zasu rama.
Allah shine mafi sani.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

tambaya ta 1

tambaya-da-amsa.jpgTambaya ta 1.

Malam mace ce taga jini jini a pant dinta kuma tana axumi, amma jini ba kamar yadda takeyi idan
tana haila ba.Wannan yayi fari-fari ne bashi da duhu.Kenan axuminta ya karye?
Dan Allah malam a buye sunana.Kuma a taimakamin da addu,a ina yawan mafarkin
mace 'yar uwata tana saduwa dani.Da chan ban dauka a komai ba sai danaga posting
dinku cewa aljannu na shafar mutum.Ke nan malm aljana ce ta shafeni ko ko yaya?

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

AMSA
******************
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Idan matar da take AZUMI taga wani jini ya digo daga farjinta, to hakika wannan Azumin nata ya karye.
Kuma zata ramashi.
Shi jinin haila bashida iyakacin karancin lokaci abisa mazhabin Imamu Malik (rta).
Zai iya zuwa nan take, sannan ya dauke nan take.Dangane da Kalarsa kuwa, eh yakan chanza kala
awasu lokutan.Musamman ma idan an samu wani chanjin yanayin lafiyar jiki.Ko kuma chanjin abinci, ko kuma yawaitar shekaru.
(YA DANGANTA DA HALITTAR JIKIN ITA MAI HAILAR).AMSAR TAMBAYARKI TA BIYU:
EH Zata iya yuwuwa wata Aljana ko kuma aljani ya shafeki.
Musamman ma idan kina jin sauran manyan alamomin kamarsu FADUWAR GABA, CIWON KAI, FIRGITA, YAWAN
BACIN RAI BABU DALILI, QAIKAYIN GABA, etc.Awasu lokutan ALJANI NAMIJI zai iya zuwa miki da siffar mace yana saduwa dake.Ko kuma yazo miki dasiffar mijinki ko saurayinki.Wani lokacin kuma yazo miki da siffar wani mutum wanda kike jin kunya, etc.Kuma shima aljanin zai iya haddasa miki RIKICIN
JININ AL'ADA.WALLAHU A'ALAM
DA FATAN ALLAH YABAKI LAFIYA DAKE DA DUKKAN MASU FAMA DA IRIN WANNAN MATSALAR.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

YAUSHE NE AKE DAUKAR NIYYAR AZUMI ?

tamabyoyi.jpgYAUSHE NE AKE DAUKAR NIYYAR AZUMI ?

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

YAUSHE NE AKE DAUKAR NIYYAR AZUMI ?

AMSA

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

----- Ana daukar niyyar azumine kafin ketowar
alfijir idan ya kasance azumin farillane, domin fadar Manzon Allah (S.A.W.) wanda bai dauki niyyar azumi da dare ba (kafin ketowar alfijir) bashi da azumi" Nana Hafsa ta ruwaitoshi (R.A.) Sheikh Albani yayi tahakikinsa. Kuduba sahihu jamiu Sagir
hadisi mai lamba ta 6535 ko kuma sahihin Nasa'I,tahakikin Sheikh Albani lamba 2199).

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

YAUSHE NE LOKACIN BUDA BAKI (SHAN RUWA).

tamabyoyi.jpgtambaya-da-amsa.jpgAUSHE NE LOKACIN BUDA BAKI (SHAN RUWA).

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

YAUSHE NE LOKACIN BUDA BAKI (SHAN RUWA).

AMSA
-------------------------------------

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Buda baki yana tabbatane da zarar anga rana tafadi koda mutum yayi buda baki ko bai yiba.Dalili kuwa shine:Hadisin Abdullahi Ibn Awfa yace:Mun kasance cikin tafiya tareda Manzon Allah {S.A.W} alhalin cewa yana azumi.Yayin da rana tafadi sai yacewa wani daga cikin sashen sahabbansa yakai wane ka tashi ka shirya mana abin buda baki (farau-farau) sai yace:Ya Manzon Allah inama ace mun kara yammata (shi yana kokwanton faduwar rana ne).Sai yace ka sauka ka shirya mana abin buda baki.Sai yace ya Manzon Allah ina ma mun kara
yammata.Sai yace ka sauka ka shirya mana abin buda baki.Sai yace ya Manzon Allah ai akwai sauran rana sai yace ka sauka ka shirya mana abin buda baki.Sai ya sauka ya shirya musu sai Annabi {S.A.W.}
yasha ruwa sannan yace:Idan kuka ga dare ya gabato daganan hakika mai azumi yabude baki (ana nufin ko yasha ruwa, ko bai shaba).(Bukhari 1958 Kitabus-siyam)kuma ya tabbata acikin Bukhari daga Sahal ibn
Sa'ad Yace:Hakika Manzon Allah (S.A.W.) yace:Mutane baza su gushe cikin Alkhairi ba, matukar suna gaggauta bude baki.
Amma abin mamaki a yanzu sai kaga mutane
sunyi salla basu sha ruwa ba.ko kuma su bari harsai taurari sun bayyana,sannan suyi buda baki, tsammanin su yin haka shine dai-dai, alhali yin hakan ya sabama sunna kamar yadda ya tabbata a hadisin daya gabata.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

YAUSHENE YAFI DACEWA AYI SAHUR ???

tamabyoyi.jpgYAUSHENE YAFI DACEWA AYI SAHUR ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

YAUSHENE YAFI DACEWA AYI SAHUR ???
AMSA
------------------------------------

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

A sunnace anaso a Jinkirta yin sahur zuwa kusan ketowar Alfijir.Hadisi ya tabbata daga Anas dan Malik, daga Zaid
Bn Thabit (R.A.) yace:"Munyi Sahur tare da manzon Allah (S.A.W.) bayan wannan sai manzon Allah (S.A.W.) ya tashi zuwa sallah.Sai Anas ya tambayi Zaid bin Thabit cewa:Menene tsakanin cin sahur dayin sallar Asuba ?
Sai yace:Gwargwadon Aya 50 (watau mutum ya karanta Aya 50)".(Kuduba Sahihul Bukhari, 1921)(Ko sahihu muslim 1097).
Akwai kuma hadisin Sahl ibn Sa'ad yace:-
"Na kasance inayin sahur cikin iyalina bayan wannan sai inyi gaggawa domin samun Sujada (Sallah) da manzon Allah (S.A.W.)".Wannan yanuna cewa ana yin sahur ne dab da ketowar Alfijir.(Kuduba Sahihul Bukhari, 1920).

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

YAN UWA MUSULMI DUBI HIMMAR MAGABATA (NAGARI) WURIN KARATUN ALQUR‘ANI LOKACIN RAMADAN DOMIN KOYI DASU.

tunatarwa.jpg

'YAN UWA MUSULMI DUBI HIMMAR MAGABATA (NAGARI) WURIN KARATUN ALQUR‘ANI LOKACIN RAMADAN DOMIN KOYI DASU.

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

DAN UWA MUSULMI DUBI HIMMAR MAGABATA
(NAGARI) WURIN KARATUN ALQUR‘ANI LOKACIN RAMADAN DOMIN KOYI DASU.

Imam Al-nawawiy yafada acikin littafinsa (hilyatul-abraar:116) yace:Dan abiy dawud yarawaito da sanadi ingantacce cewa:
Hakika MUJAHID (cikin tabi‘ai) Allah ya
rahamsheshi ya kasance yana saukar Al-qur‘ani tsakanin sallar magriba zuwa isha'i cikin ramadan
(domin suna jinkirta sallar ishah).UTHMAN DAN AFFAN (R.A) TAMIM AD- DARIY
(R.A), DA SA‘EED BN JUBAIR ALLAH
YAKARA MUSU YARDA DUK SUKAN SAUKI ALQUR‘ANI ACIKIN RAKA‘A GUDA!!!.Wannan baya cikin hanin da mazo Allah (s.a.w)yayi na karance Al-qur‘ani cikin kasa ga kwanaki
uku.Domin Karin bayani kuduba littafin da muka fada asama.
ALLAH YA BAMU IKON KWATANTAWA.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

FALALAR YIN SAHUR

tambaya-da-amsa.jpgmamatan-kwarai.jpgtambaya-da-amsa.jpg5.jpgtambaya-da-amsa.jpg

MENENE FALALAR YIN SAHUR ?

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

MENENE FALALAR YIN SAHUR ?

AMSA
----------------
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Hadisi ya tabbata daga Anas dan Malik (R.A.)yace:-Hakika manzon Allah (S.A.W.) yace:Kuyi sahur, hakika yin sahur akwai albarka acikinsa.(Kuduba Sahihul Bukhari 1923).Saboda haka duk abinda Manzon Allah ya ambace
shi da Albarka kuna ganin mutum zaiyi wasa dashi kuwa ?Yin azumin dore ba sunnah bace, akwai lada mai tarin yawa acikin yin sahur, anaso koda mutum bazaici abinci ba to yasha ruwa.ALLAH YASA MU DACE

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

GASKIYA DA 'DACI YAKE, AMMA SAI NA FA'DA

GASKIYA DA 'DACI YAKE, AMMA SAI NA FA'DA

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Kayi abota da wanda ke rike sirrinka ya rufe
aibunka, ya fadi alkhairinka. Idan baka sameshi ba to kazama kaine abokin kanka.
Idan kana son kaji dadin zama da mutane ka nisanci mugun zato da yawan ikirari da leken asirin mutane.
Abokin kwarai yana da wuyar samu, yana da wuyar bari,kuma ba a mantashi.Alamomin wadanda suka auri duniya suka saki
lahira guda biyar ne;

1* Basu jiran sallah kafin atayar da ita.

2* Basu karanta Alkur'ani sai lokacin bukata.

3* Ba karbar nasiha ballantana suyi amfani da ita.

4* Basu zuwa wurin wa'azi ballantana su saurareshi.

5* Basu neman sanin addini ballantana suyishi yadda ya kamata.

Ababuwa ukku suna hana arziki;

* Yawan bacci
* Yanke zumunta
* Cin amana.

‪‎Bebe‬ yana sha'awar karanta Alkur'ani, ‪#Kurma‬ yana son saurarenshi
‪‎Makaho‬ yana son ya kalle shi.Kai da Allh ya baka ji da gani da magana, sau nawa kake karantashi?
Mutanen kirki kamar iccen mangwaro suke; mutane na jifar su da dutse su kuma suna sako musu nunannun'ya'ya masu dadi.Allah yasa mu dace Ameen.
Naku; Muh'd Abba Gana

www.hanyantsira.mywapblog.com

Share:

DAME AKAFI SO MUTUM YA FARA BUDA BAKI ?

tambaya-da-amsa.jpg

DAME AKAFI SO MUTUM YA FARA BUDA BAKI ?

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

DAME AKAFI SO MUTUM YA FARA BUDA BAKI ?

AMSA
-----------------

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

An fiso yafara buda baki da danyen dabino, idan har bai samu ba sai yayi da busasshe, idan bai samu ba sai yasha ruwa.Dukkan wannan zai zama kafin yayi sallah ne,
kuma an fiso yaci guda (1 ko 3 ko 5 ko 7 ko 9).Domin hadisi ya tabbata daga Anas dan Malik (R.A)yace:Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana bude baki da danyen dabino kafin yayi sallah, idan bai samu danye ba, ya kanyi da busasshe,idan kuma bai samu busasshe ba sai ya kamfaci ruwa yasha.(Abi Dauda, Babin Bude Baki hadith mai lamba
2065).Hadisi ne ingatacce.Allah yasa mu dace

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
Share:

MENENE HUKUNCIN AZUMIN MUTUMIN DA YAYI ALLURA, KO AKASA MASA MAGANI A CIKIN CIWONSA ???

MENENE HUKUNCIN AZUMIN MUTUMIN DA YAYI ALLURA, KO AKASA MASA MAGANI A CIKIN
CIWONSA ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

MENENE HUKUNCIN AZUMIN MUTUMIN DA YAYI ALLURA, KO AKASA MASA MAGANI A CIKIN
CIWONSA ???

AMSA

-----
Azuminsa yananan bai karye ba, saidai idan Allurar ta kasance akwai abinci acikinta.
Domin Hasnul basri yace babu laifi mutum yasa Magani a cikinsa, wanda hakan ya kunshi allura ne, saidai idan tana da abinci a cikinta.
____________________________________
Bukshari, Muslim
Kuba Athar na Husnul Basri (Bukhari, babi na 25, kitabus siyam).

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
Share:

MENENE HUKUNCIN MATAR DA JININ AL'ADA KO JININ BIKI YADAUKE MATA KO WANKAN JANABA YA SAMETA KAFIN KETOWAR ALFIJIR, ZATA IYA DAUKAR AZUMI KO KUWA ???

MENENE HUKUNCIN MATAR DA JININ AL'ADA KO JININ BIKI YADAUKE MATA KO WANKAN JANABA YA SAMETA KAFIN KETOWAR ALFIJIR, ZATA IYA DAUKAR AZUMI KO KUWA ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

MENENE HUKUNCINt MATAR DA JININ AL'ADA KO JININ BIKI YADAUKE MATA KO WANKAN JANABA
YA SAMETA KAFIN KETOWAR ALFIJIR, ZATA IYA DAUKAR AZUMI KO KUWA ???

AMSA
-----

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Zata tashi da azumi, daga baya sai tayi wanka.Saboda hadisi ya tabbata daga nana Aisha (RA)tace:"Manzon Allah (S.A.W) yakan wayi gari da janaba a
jikinsa a sababin jima'I da yayi, ba mafarki ba
acikin ramadhan,kuma sai yaci gaba dayin
azuminsa.Ma'ana zai iya samun janaba da dare, ya wayi gari
da ita kuma yaci gaba da azuminsa babu komai".WALLAHU A ALAM

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
Share:

SHIN MAI AZUMI ZAI IYA SHAFA MAI KO TURARE ???

SHIN MAI AZUMI ZAI IYA SHAFA MAI KO TURARE ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

SHIN MAI AZUMI ZAI IYA SHAFA MAI KO TURARE ???

AMSA
-----

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Na'am, zai iya, saboda fatawar Abdullahi dan
Mas'ud wadda yace:
Idan "Dayanku yana azumi zai iya wayar gari yana mai shafa mai kuma yana taje kansa".Domin jin kamshi bacin abinci bane kuma ba sha
bane.Haka kuma katadah yace:Mustahabbi ne mutum yashafa mai domin ya kauda kura daga jikinsa.A cikin malaman mazhaba akwai mutrafi, da Abdult Hakam, da Asbagu duk sunce ya hallata a shafa mai, kuma basu bambanta ba tsakanin me kamshi
ko mara kamshi.
________________________________________
Domin karin bayani kuduba maganar ibn Mas'ud(Sahihu Bukhari babi na 25, Kitabus siyam).Hakanan sanya kwalli shima baya karya azumi.
Ibn majshun yace babu laifi yin haka, domin baya cikin abubuwan da suke karya azumi.Hakanan mutraf da Asbagu, da laithu da ibn Habib,
da Imam Zuhri suka tafi akai.Dukkansu kuma manya manyan malaman mazhaba
ne. Allah yasa mu dace

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww)yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

WACE ADDU'A MUTUM ZAIYI A DAREN DA AKESA RAI DA LAILATUL QADARI???

WACE ADDU'A MUTUM ZAIYI A DAREN DA AKESA RAI DA LAILATUL QADARI???

TAMBAYA ???
WACE ADDU'A MUTUM ZAIYI A DAREN DA AKESA
RAI DA LAILATUL QADARI ???
AMSA
-----

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Hadisi ya tabbata daga nana Aisha (R.A) ta tambayi Manzon Allah (SAW) cewa:"Idan naga daren Lailatul kadari me zance ?Sai Annabi (SAW) yace mata kice:-"ALLAHUMMA INNAKA AFUWUN TUHIBBUL AFWA
FA'AFU ANNA"Ma'ana
"Ya bangiji,hakika kaine mai afuwa, kuma kana son afuwa, kayi min afuwa".
______________________________
Domin Qarin bayani Kuduba Sahihu Muslim,(Sharhin Qhadi iyad, 762)Ko Sahihu Muslim hadisi mai lamba (1170).Abu Dauda, Tirmiji da Hakim suka ruwaito shi.Tirmizi ya ingantashi.Allah ya Azurtamu da ganin wannan dare.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

MENENE MAFIFICIN AIKIN DA MAI AZUMI ZAI DINGA YI ???

MENENE MAFIFICIN AIKIN DA MAI AZUMI ZAI
DINGA YI ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

MENENE MAFIFICIN AIKIN DA MAI AZUMI ZAI DINGA YI ???

AMSA
-----
Aikin da yafi falala ga mai azumi shine

1. Karatun Al'Qurani.
Ma'ana ya lazimce shi dare da rana, kuma yadinga izna da abin da yake karantawa.
Amma idan bazai iya karatun Al-Qurani ba, to sai ya rinka lazimtar inda ake karatun Al-qur'anin ko fassarashi domin hadisi ya tabbata daga nana
Fadima 'yar Manzon Allah da Abu Huraira yardar Allah ta tabbata a garesu sunce: "Mala'ika Jibrilu ya kasance yana bijirowa da Annabi (S.A.W) Al'Kurani sau daya a kowace shekara, sai ya bijiro masa dashi sau biyu a shekarar da zaiyi wafati.Bukhari da Muslim ne suka ruwaito (1).
____________________________________
(1) Bukhari K=66, Book=7, Hadith=4998 da Muslim
K=44,
B= 15, Hadith=2450.
Wannan yana nuna cewa karatun Al-qur'ani shine
mafificin ibada a cikin watan Ramadhan.
Allah madaukakin Sarki yace:
"Lallai mun saukar dashi a daren Lailatul Kadari.
2. Kyauta:
Ya kamata mai Azumi ya yawaita kyauta wajen
ciyar da jama'a, da sadaka, da taimakon gajiyayyu
da makusanta.
Kamar yadda ya tabbata a hadisin ibn Abbas cewa:"Annabi (S.A.W.) yafi kowa kyauta, kuma mafi
alkhairinsa yana yinsa ne a ramadhan yayin da yake saduwa da Jibrilu.Kuma ibn Abbas (R.A) yace:
Alkhairin Manzon Allah (S.A.W) yafi sakakkiyar
iska".Bukhari ne ya ruwaito shi (2).
(1) Suratul Kadari Aya1 (2) Bukhari K = 1, B = 5, da
Muslim K = 43, B = 12, H = 2308.
Nafil-fili:
Anaso mai Azumi ya yawaita Nafil Fili musamman
kiyamul laili
Saboda hadisin Abu Hurairah yardar Allah ta kara
tabbata a gareshi yace:Manzon Allah (S.A.W) yace:
"Duk wanda yatsaya kiyamulaili yana mai imani, da neman lada; an gafarta masa zunubansa da suka
gabata".
Bukhari ne ya ruwaito shi(1).
Haka kuma Manzon Allah (S.A.W) yace:
Wanda yayi sallah dare tare da liman har yagama
za'a rubuta masa ladan kiyamullaili.h
Kuma anfison duk wanda zaiyi kiyamullaili ya
tsawaita tsayuwar saboda hadisin Khuzaifa (R.A)
Targib Wattarhib wanda Albani yayiwa tahkiki lambar (1078).
"Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana tsawaita
karatu a sallar dare a watan Ramadhan fiye da sauran sallolin dare, yace:Manzon Allah (S.A.W) yakan karanta Suratul Bakarah da Nisa'I da Ali'Imran a raka'a daya, kuma
baya wuce ayar da akayi tsoratarwa a cikin ta sai ya tsaya ya roki Ubangiji tsari.
Kuma bai gama raka'a biyu ba sai ga Bilalu (R.A)yazo yana neman izni ayi sallar Asuba.
Ahmad ya ruwaito wannan hadisin kuma ya ingantashi.
4. Yawan Zikiri da Salatin Annabi (S.A.W):
Abune mai matukar falala mutum ya yawaita Zikiri
da Salati ga Shugaban Halitta irin wanda ya
tabbata daga bakin Manzon Allah (S.A.W).
5. Ciyar da mai Azumi abin Buda baki:
Yana daga cikin mafificiyar ibada mutum yayi
kokari wajen bawa dan uwansa abin Bude baki
saboda hadisin da Annabi
(S.A. W) yake cewa:
"Duk wanda yaciyar da mai Azumi abinda zaiyi bude baki yana da kwatan kwacin ladan wanda ya ciyar batare da an rage ladan wanda ya ciyar ba".Tirmizi yace wannan hadisine hasanun sahih.
6. Umrah:
Yin umrah acikin watan ramadhan ga wanda Allah
ya bashi iko yana daga cikin Aiyukan da ake
kwadaitar da mai Azumi yayi.
Amma duk da haka bai kamata mutum yatafi
umrah yabar makwabtansa da danginsa da sauran
mabukata a cikin yunwa da halin kakani kayi ba.
Kuma ya kamata mu fahimci cewa, ciyarwa itace abinda Annabi (S.A.W) yafi bawa muhimmanci
acikin watan Ramadhan.To kunjifa Annabi yake daukar dogon zango idan
yana sallar nafila da azumi.Ya Allah kasa muna daga cikin wadanda zaka
'yanta acikin wannan wata, domin darajar Annabi Muhammad (s.a.w).

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

ABUBUWAN DA SUKA HALATTA GAME AZUMI

ABUBUWAN DA SUKA HALATTA GAME AZUMI.

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

ABUBUWAN DA SUKA HALATTA GAME AZUMI.

1.Shiga cikin Ruwa dayin nitso aciki domin sanyaya jiki saboda tsananin zafi.
Domin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam, ya
kasance:"Yana zuba ruwa akansa, yana me Azumi saboda kishirwa ko saboda Zafi"(Ahmad da Abu Dawud).

2. Yawayi gari yanada janaba a jikinsa, ya halatta,Saboda fadin Nana A'isha Allah yakara mata yarda
tace:"Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.Ya kasance yana wayar gari da janba yana mai Azumi sannan yayi wanka"Bukhari da muslim).Wato acikin Azumin Ramadan.

3. Ci da Sha da Jima'i cikin dare har zuwa lakacin fitowar alfijir.
Saboda fadin Ma'aiki Sallallahu AlaihiWasallam:
"Lallai Bilal yana kiran Sallah da dare, to kuci
kusha harsai dan umm maktum yayi kiran sallah"Bukhari da muslim).Wato bilal nayin kira na farko shikuma yanayin kira
na biyu.

4. Me jinin Haila da me jinin Biki.Idan jinin ya yanke mata cikin dare ya halatta su jinkirta wankan har zuwa Asubahi, kuma su wayi
gari da Azuminsu sannan suyi wanka kafin suyi Sallah.

5. Yin Aswaki a farkon Yini da karshensa. Saboda cin Aswaki mustabbine kuma babu wani dalili da yanuna cewa za'ayi shi a wani lokaci banda wani, wannan shine mazhabin mafi yawan malamai.

6. Yin magani kowane Iri matukar bazai tafi cikinsa ba kamar yin allura wacce bata abinci bace.

8. Tauna abinci da dandanashi da sharadin babu abinda zewuce ciki.

9. Yin amfani da turare da Shakar kamshi mai
dadi.
Allah yasa mu daxe

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969y
07038774163

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww)yace:"WALLAHI IDAN ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

SHIN GASKIYANE ACIKIN DAREN LAILATUL QADARI ANA GANIN KOMAI YANA YIN SUJADA, KAMAR BISHIYOYI DA GIDAJE HARMA MUTUM YA RINKA HANGO KA'ABA DAGA DUK INDA YAKE ???

SHIN GASKIYANE ACIKIN DAREN LAILATUL
QADARI ANA GANIN KOMAI YANA YIN SUJADA,
KAMAR BISHIYOYI DA GIDAJE HARMA MUTUM YA
RINKA HANGO KA'ABA DAGA DUK INDA YAKE ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

TAMBAYA ???
SHIN GASKIYANE ACIKIN DAREN LAILATUL QADARI
ANA GANIN KOMA YANA YIN SUJADA, KAMAR
BISHIYOYI DA GIDAJE HARMA MUTUM YA RINKA
HANGO KA'ABA DAGA DUK INDA YAKE ???
AMSA
-----

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Wannan bai tabbata ba daga manzon Allah (S.A.W)ko magabata na kwarai.Ijtihadin wasu mutane ne ba tareda wani dalili na
sharia ba.Amma ya tabbata wasu daga cikin sahabbai "An
nuna masu a mafarki cewar daren lailatul Qadari yana cikin bakwai na karshe"
Wannan hadisin yanuna cewar an nuna masu ranar ne amma ba wani abu suka gani ba.Amma ana ganin alamomin daren lailatul Qadari
kamar yadda Annabi (S.A.W) ya bada labari cewa:"Ranar daren lailatul Qadari takan fita batayin zafi.Muslim (Sharhin khadi iyad, 1165)
Kuma Manzon Allah (S.A.W) yace:"A cikinku wa zai tuna daren da wata ya fito kamar rabin akushi? Ana fadin daren lailatul kadari sait Annabi (S.A.W)yafadi haka.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969
07038774163

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

YAUSHE AKESA RAI DA DAREN LAILATUL KADARI ???

YAUSHE AKESA RAI DA DAREN LAILATUL
KADARI ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

TAMBAYA ???
YAUSHE AKESA RAI DA DAREN LAILATUL
KADARI ???
AMSA
-----

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
Anasa rai da daren lailatul Qadari a dararen 21, 23,
25, 27 da 29.
Domin hadisi ya tabbata daga Abdullahi bin Umar
(RA) yace:Manzon Allah (S.A.W) yace:
"Kunemi daren lailatul Qadari a wutiri na goman karshe"Amma hadisai dayawa sun karfafa daren 27.An karbo wani hadisin daga Abdullahi bin Umar(R.A) yace:
Manzon Allah (S.A.W) yace:"Kuyi kirga don lailatul Qadari a bakwai na karshe".
__________________________________
Domin Qarin bayani kuduba Sahih Muslim (206).
Allah ka azurtamu da ganin wannan dare.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969
07038774163

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

DALILAN SHAN AZUMI GUDA GOMA SHA BIYU {12}.

DALILAN SHAN AZUMI GUDA GOMA SHA BIYU {12}.

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

DALILAN SHAN AZUMI GUDA GOMA SHA BIYU.
Sharia ta Amincewa masu larura, susha azumi.Wasu zasu Rama Wasu, su ciyar.
Wasu baza, su ramaba, kuma bazasu ciyar ba.Gasu kamar haka:

1. Na farko:Mara lafiya, zaisha azumi, idan ya warke sai yarama.

2. Na biyu:Matafiyi, zaisha azumi saboda tafiya, saiya Rama
daga baya.

3. Na uku:
Mace mai jinin al'ada zatasha azumi idan tayitsarki, saita Rama.

4. Na hudu:Mai jinin haihuwa, idan jini yadauke sai tarama.

5. Na biyar.
Mai ciki, wacce Taji tsoron, wani Abu zai sameta,koya sami dan cikinta.

6. Na shida.Mai shayarwa, wacce Taji tsoron cutuwa gareta ko dan da take shayarwa.

7 Na bakwai.Tsoho, ko tsohuwa, wadanda, tsufa ya hanasu yin
azumi, sai su ciyar kawai babu ramuwa akansu.

8. Na takwas:
Mahaukaci, idan ya warke, sai ya Rama idan kuwa,babu waraka ya sauka akansa babu ramuwa babuciyarwa.

9. Na tara:Qaramin Yaro, azumi ba wajibi bane akansa, sai dan sabawa.

10. Na goma.
Mai farfadiya, idan farfadiya, tazowa mutum, yana azumi, bazai ramaba idan ya farfado.

11 Na sha daya:
Mai ciwon Qishirwa, wanda bazai iya azumi ba, sai ya Dinga ciyarwa kawai.

12 Na sha biyu:
Mai ciwan yinwa Ulcer (olsa) wanda, baya iya
daukar lokaci mai tsawo sai yaci abinci, shima sai ya Dinga ciyarwa.SHARHI
-------------------------------------
Mai ciki da mai shayarwa, suna matsayin marasa
lafiya idan sun sami dama sai su Rama.
Amma, wasu malamai suna ganin idan ciyarwa ma sukayi yayi dai-dai.
WALLAHU A'ALAM.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969
07038774163

Muh'd Abba Gana

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

ABUBUWAN DA AKA HARAMTA GA MAI JININ HAILA

ABUBUWAN DA AKA HARAMTA GA MAI JININ HAILA

(2)

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

ABUBUWAN DA AKA HARAMTA GA MAI JININ HAILA kahina 2

5. Azumi:Bai halatta mai jinin Haila tayi azumi na farilla ko
na nafila, idan tayi kuma bai yiba, saboda haka zata lissafa azumin da tasha bayan watan ya wuce
saita ramasu.Ba'a ajiye azumi domin tsammanin gobe al'ada zatazo, amma dazarar tazo to ba azumi, dazarar bata zoba to akwai azumi, koda kinji tafiyarjinin a
jikinki amma bai fitoba to biki fara al'adaba, sai ya fitane za'a fara lissafi.

6. TABA ALQUR'ANI MAI GIRMA:
Mai jinin Haila bata taba kasantuwarsa littafi mai tsarki sannan kuma ita bata da tsarki, amma wannan baya hana idan ta ganshi zai fadi ta daukeshi ta gyara masa wuri.

7. Karatun Alkur'ani:
Mai al'ada bata karanta Alkur'ani, duk dacewa wadansu malamai suna ganin ya halatta ta karantashi daka domin kada ta manta sabanin
dauka.

8. Saduwa:
Baya halatta saduwa da mace tana al'ada, idan taqi yadda da mijinta ya sadu da ita domin tana Haila ba za'ace ta sabawaAllah ba hasalima tayi
biyayyane gareshi.
Bai halatta a sadu da mace tana al'adaba harsai al'adar ta dauke kuma tayi wankan tsarki, koda al'adar ta dauke amma batayi wankaba to bai halatta a sadu da itaba harsai tayi wanka.Ya halatta miji ya taba duk inda yakeso a jikin matarsa alokacin da take al'ada bayan tayi kunzugu inbanda daga cikbiyarta zuwa gwiwarta wannan kan bai halattaba harsai jinin yadauke kuma tayi wanka.Hakanan itama ya halatta ta taba ko ina a jikinsa
duk da tana al'ada.

9. Tabbatar Da Rashin Tsarki:Al'ada tana tabbatar da wacce take da ita bata datsarki.

10. Wajabta Wanka:
Al'ada tana wajabta wanka, wato dukkan matar datayi al'ada kuma al'adar ta dauke to wankan tsarki ya wajaba akanta.Shi kuma bayani akan abinda ya shafi wankan tsarki tuni ya gabata, da fatan Allah yayi mana jagora ya karba mana ayyukammu.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969
07038774163

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER,y
BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

ABUBUWAN DA AKA HARAMTA GA MAI JININ HAILA

ABUBUWAN DA AKA HARAMTA GA MAI JININ HAILA

(1)

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Abubuwan Da Basu Halattaba Ga Mai jinin Haila (1)

Anan zan lissafa abubuwan da basu halatta mai al'ada tayisu ba ko ayi mata.
Wadannan abubuwa ne guda goma zan kawo guda 5 darasi mai zuwa zan kawo ragowar:

1. Sallah
Baya halatta mai al'ada tayi sallar farilla ko nafila,idan kuma tayi baza'a karba ba sannan kuma tayi laifi, sannan bayan ta kammala al'adar bazata rama sallolinba.

2. SAKI:
Baya halatta matar da take al'ada a saketa, wannan ya sabawa karantarwar musulunci, saboda haka koda yanason ya saketa to yabari saita kammala al'ada kafin yasadu da ita sai ya saketa.Amma idan ya saketa tana jinin Hailar to sakin yayi amma za'a tilasta shi ya mayar da ita idan sakin bai kai uku ba.

3. Dawafi:
Baya halatta mai al'ada tayi dawafin Ka'abah,amma zatayi sauran dukkan abinda maniyyaci yakeyi, kamar tsaiwar Arafah da kwanan mina dana
muzdalifa da jifa da Labbaika, da daidai sauransu.

4. ZAMA A MASALLACI:
Mace mai Haila bazata zauna a cikin masallaciba,domin sauraron karatu ko karantarwa ko taro dadai sauransu.Darasi mai zuwa zanci gaba daga yadda muka tsaya.Insha Allah.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969
07038774163

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

MALAM MENENE HUKUNCIN WANDA YAKALLI BLUE FILM DA RANA YANA AZUMI HAR YA FITAR DA MANIYYI KUMA BAIYI WANKABA HAR SALLOLIN AZAHAR DA LA'ASAR SUKA WUCESHI ???

MALAM MENENE HUKUNCIN WANDA YAKALLI BLUE FILM DA RANA YANA AZUMI HAR YA FITAR DA MANIYYI KUMA BAIYI WANKABA HAR SALLOLIN AZAHAR DA LA'ASAR SUKA
WUCESHI ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

MALAM MENENE HUKUNCIN WANDA YAKALLI BLUE
FILM DA RANA YANA AZUMI HAR YA FITAR DA MANIYYI KUMA BAIYI WANKABA HAR SALLOLINAZAHAR DA LA'ASAR SUKA WUCESHI ???

Domin naji kace wanda yayi mafarki da rana yafitar da maniyyi azuminsa yananan.
Shima wannan kenen azuminsa yananan ?
(Dan Allah ka6oye sunana).
AMSA
-----

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN.
Lallai wannan kayi babbar ta6argaza.
Bakada azumi sannan sai kayi kaffarar guda sittin duk da wanda kakarya zakayi 61 kenan babu hutu.
Domin wannan ba uxury bane a wajen Ubangiji gangancine kayi.Koda mai matar aure ta sunnah an haramta masa ya sadu da ita da rana acikin watan azumi, sai yayi
kaffara.Balantana kai daka tafka sa6on Allah kana kallon kafirai maqiya Annabi Muhammad (s.a.w) suna tafka Masha'a har kafitar da maniyyi, sannan kake taqama da wanda yayi mafarkib da rana.HUJJA ANAN ITACE:Duk wanda yakev bacci baisan a inda yakeba,hankalinsa baya tare dashi, sannan koda wani abu
zai sameshi acikin baccin nasa bashida ikon kare kansa kamar yadda zai iya a zahiri.
Kamar yadda yazo a hadisai cewa:An dauke alqalamin rubutun zunubi akan mutum
uku.
1. Qaramin yaro.
2. Mahaukaci.
3. Maiyin bacci har saiya farka.
Wadannan mutanen dukansu hankalinsu baya tare dasu.
Amma banda wanda yasha giya yafita daga
hayyacinsa, domin wannan shine yajawa kansa.Saboda haka zaka rama azumi guda 61 bayan sallah.
Sannan inajan kunnen matasa maza da mata
suguji yin Chating acikin watan azumi saboda gudun afkawa fitina irin wannan.
Allah kashiryi matasanmu maza dav mata ka aurar dasu ga ma'aurata nagari.ALLAH YASA MU DACE.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969
07038774163

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

MATSAYIN ZAKKAR FIDDA KAI A QARSHEN AZUMI.

MATSAYIN ZAKKAR FIDDA KAI A QARSHEN AZUMI.

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

TAMBAYA ???
MENENE MATSAYIN ZAKKAR FIDDA KAI ???

AMSA
-----
Zakkar fidda kai sunnah ce daga cikin sunnar Manzon Allah (S.A.W).Manzon Allah da kansa ya aikata ta, hakama sahabbansa sun aikakata.Za'a iya fidda ita kafin ganin wata, domin sahabbai sun aikata haka.Ana fitar da zakkar fidda kai ga kowane musulmi,yaro da babba, mace da namiji, 'Da ko kuma bawa, kowane mutum mudun nabi hudu.
Amma abin mamaki mafi yawan mutane basu damu da fitar da itaba, saboda da'awar talauci.HAKIMAR ZAKKAR FIDDA KAI
TSARKAKE MAI AZUMI:Tana tsarkake mai azumi daga kuskuren daya aikata acikin azuminsa na ramadan kamar zantukan banza, zagi, kallon haram da sauransu.SANYA WALWALA AZUKATAN 'YAN UWA MUSULMI:Zakkar fidda kai tana sanya walwala a zukatan 'yan
uwa musulmai ta yadda babu wani dan uwa da zai nemi abinci da zaici a ranar farin cikin sallah yarasa, da sauransu.SUWA YA KAMATA SUYI ZAKKAR FIDDA KAI ???Hakika zakkar fidda kai ta rataya akan dukkan musulmi mai 'yanci ko bawa, babba ko yaro,
namiji ko mace.

TAMBAYA ???
SHIN YA TABBATA WANDA BAI FITAR DA ZAKKAR FIDDA KAIBA, ZA'A RATAYE AZUMINSA, BA ZA'A KARBA BA HARSAI RANAR DA YA BAYAR ???

AMSA

A'a Wannan hadisin bai tabbata daga bakin
manzon Allah ba.
Hadisi ne mai rauni, kuma duk mutumin daya bari aka sauka daga idi, hukuncin zakkarsa kamar sauran sadaka ne ba zakkar fidda kai bace.WALLAHU A'ALAM
YA ALLAH KADATAR DAMU.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969
07038774163

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

MENENE HUKUNCIN WANDA YACI ABINCI KO YASHA RUWA ABISA MANTUWA ALHALI YANA AZUMIN RAMADAN ???

MENENE HUKUNCIN WANDA YACI ABINCI KO YASHA RUWA ABISA MANTUWA ALHALI YANA
AZUMIN RAMADAN ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

AMSA
-----
Sai yaci gaba da azuminsa yana nan bai karye ba,domin Allah ne yaciyar dashi ya shayar dashi.Daili kuwa ya tabbata daga Abi Hurairata (R.A)
daga Manzon Allah (S.A.W) yace:"Idan mutum ya manta, yaci ko yasha, to sai yaci
gaba da azuminsa, domin Allah ne ya ciyar dashi ya shayar dashi.
____________________________________
Kuduba Attarghib wattarhib na munzuri lahakikin sheikh Albany Juzu'I na farko shafi na (2).Suratul Baqarah, ayata183.
Sahihul Bukhari hadisi mai lamba ta (1933).

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969
07038774163

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Zaku iya turo tambayanku kai tsaye zuwa ga wannan number: 09039016969

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

KARIYA DAGA SIHIRI, TSAFI KO MUGUN BAKI.

KARIYA DAGA SIHIRI, TSAFI KO MUGUN BAKI.

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

KARIYA DAGA SIHIRI, TSAFI KO MUGUN BAKI.

1. Ka karanta:
"Laa ilaaha illallahu, wahdahu laa shareeka lah,lahul-mulku, wa lahul-hamdu, wa Huwa alaa kulli shai'in qadeer"kafa 100 bayan sallar asuba.

2. Idan kazo kwanciya, Ka karanta Suratul Ikhlas(Sura ta 112), Falaq (Sura ta 113), Nas (Sura ta114), ka tofa a hannu, sannan, ka shafe a jikinka gaba daya.Ka yi haka sau 3.

3. Ka karanta:
Hasbiyallaahu laa ilaaha illaa Huwa alaihi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-Arshil Azeem"Kafa 7, da safe da kuma yamma.

4. Ka Karanta:
"Bismillaahil lazee laa yadurru ma'asmihi shai'un fil-ardi walaa fis-samaa'i wa Huwas samee'ul Aleem."Kafa 3 da safe da kuma yamma.

5. Ka rinka cin Dabino guda 7 (irin wanda ake
cema ajwa na madina) kullum da safe.

6. Ka karanta:
"A'uzu bi kalimaatil-lahit taammaat min sharri maa khalaqa."Kafa uku da safe da yamma.

7. Ka karanta Amanar rasulu zuwa karshe lokacinda zaka kwanta barci.(Suratul Baqara ayata 285 zuwa ta 286).

8. Ka rinka kwanciya da alwala.Allah kabamu kariya da kariyarka, sannan ka rabamu daga sharrin azzalumai.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969
07038774163

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

MUHIMMIYAR FADAKARWA GA MATA MASUYIN CIKIN SHEGE.

MUHIMMIYAR FADAKARWA GA MATA MASUYIN CIKIN SHEGE.

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

MUHIMMIYAR FADAKARWA GA MATA MASUYIN
CIKIN SHEGE.
Yin ZINA Babban Laifi ne, amma KISAN KAI ya fishi laifi, duk Matar da ta yi ZINA, Kuma har tasamu CIKI na ZINA, wannan laifi ne tsakanin ta da Allah,
kada ta KASHE Abin da ta haifa, idan har ta haihu,ta yi wa abin da ta Haifa tarbiyya, tayi "ISTIGFARI"Tsakaninta da Allah, ta yi Addu'a ga abin da ta Haifa Allah Ya yi masa albarka, domin shi ba shi da laifi, idan Allah Mai girma da daukaka ya so, sai ya kar6i tuban ta, kuma ya sanya abin da ta Haifa
ya zama nagari.Amma duk wanda yayi KISAN KAI da gangan. Idan
ba wata rahamar Allah ba, tozai dawwama a WUTA,KASHE JINJIRI kamar KASHE BABBAN MUTUM ne.
Saboda fadin Ubangiji inda yake cewa:"WA MAN YAKTUL MU'UMINAN MUTA'AMMIDAN FA
JAZA'UHU JAHANNAMA".
Ma'ana DUK WANDA YA KASHE RAI DA GANGAN SAKAMAKONSA WUTAR JAHANNAMA.
ALLAH YA KARE MU, AMEEEEN Hakama shan GIYA, Haka LUWADI, Haka CACA,
haka rantsuwar KARYA,Duka wadannan laifuka ne tsakanin Bawa da
Ubangiji, idan Mutum ya TUBA Allah zai yafe masa.Amma hakkin tsakanin Mutum da Mutum, lallai Mutum ya nemi GAFARA wajen Mutum Daya
zalunta, sannan Allah Ya yafe Masa.KUMA BA'A SAMUN SHEGE A GIDA, IDAN MUTUM
YANA MATA 2 KO 3 KO 4 YA DAUKIV KWANAN WATA YA BAWA WATA, KOTA SAMU CIKI A WANNAN SADUWAR BA SHEGE BANE, SAIDAI KAWAI ACE YA ZALUNCI MAI WANNAN KWANAN.
SAI YA NEMI AFUWA TA YAFE MASA.KUMA YIN ZINA DA MACE BAYA HANAWA A AURETA, KODA TAYI CIKIN SHEGE TARE DA WANDA YAYI NIYYA ZAI AURE TA, SUN AIKATA ABIN DA ALLAH BAYA SO, YANZU KUMA ZA SUYI WANDA ALLAH YAKE SO, SAI SU TUBA, TARIKE DANTA TA GAJE SHI YA GAJE TA KO 'YAR,AMMA SHIDAN BAZAI GAJI WANDA AKE ZATO SHI YAYI MATA CIKIN BA, IDAN HAR ZA A YI AURE,BAYAN HANKALI YA DAWO MUSU SAI TAYI
"ISTIBRA'I".{WATO JINI UKU}TANA DANA SANI MIYAGUN AYYUKAN DA TAYI
TANA ROKON ALLAH YA GAFARTA MATA,TAZAMA
CIKAKKIYAR BAZAWARA, SAI YASHIGA CIKIN
ZAWARAWA, KOTA AURE SHI, KOTA AURI WANI".ALLAH YASA MU DACE

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969
07038774163

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon tab hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

ILLOLIN YIN ZINA KAFIN AURE

ILLOLIN YIN ZINA KAFIN AURE

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

ILLOLIN YIN ZINA KAFIN AURE
=================
Duk yadda kika kai ga son saurayinki, kada kibari shaidan yafi karfin zuciyarki harki bashi kanki.Kai kuma kaji tsoron ALLAH, kada ka kusanceta
harsai tazama halak a gareka, saboda su mata sunada karancin hankali da tunani.
Amma hakan yakan faru a lokuta da dama
Domin a aure goma idan aka daura, zai wahala ba a samu irin wannan barnar ba a guda uku...BELOW ARE SOME OF ITS PROBLEMS!
1. We don't have our lives in our hands. If the young man dies before the wedding the girl is the one who is spoiled and must face life as a degraded "virgin".
{2}. She may become pregnant and he may turn his back onher.
3. Statistics show that many a girl has lost her boy friend after having had sex with
him, because his interest in her changed.
4. Some marriages are unhappy and often lead to divorce because the couple had sex before
marriage.They start their marriage which could be an exciting experience, with a feeling of guilt which
leads to stress and strife.
5. It's just soo haram and Allah punishes those who commit zina (sex before marriage and sex
with another person besides your marriage
partner)..The last Prophet may peace be upon him said that
poeple who commit zina will be punished in hell''Premarital or extramarital sex known as Zina is a
major sin in Islam!
Allah (S.W.T) warns Muslims not to even come near it and describes it as “An abomination and an
evil way.” (17: 32)
According to a Hadith it is also considered one of the worst sins inthe eyes of Allah (S.W.T).
6. The Holy Prophet related a dream in which he saw a number of sinners were being punished. The Prophet said:
We proceeded until wecame across a hole in the ground that resembled a baking pit, narrow at the top and wide at the bottom.
Babbling and voices were issuing from it.
We looked in and saw naked men and women.Underneath the pit was a raging fire whenever it flared up, the men and women screamed and rose
with it until they almost fell out of the pit. As it subsided, they returned (to the bottom). I said:
‘Who are these?’ They said: ‘…The naked men and women who
were in the pit, they aren men and women who indulge in Zina” (Bukhari).So please be obedient to God, who knows people better than they know themselves and who has a very good reason to say:
"I give you a very beautiful gift of sex, but please use it only
when you are married!" It is not a physical unity only, but a very complex psychological experience which has its roots inthe whole personality of the
man and woman.
The girl, especially, must remember that sex for her is not the same as what it means for her
boyfriend. It is possible for him to degrade it to a mere
fleshly connection only.For his girl it is a part of her whole emotional set-
up.Please wait until you are married, god will reward you.He always knows best.
If you have trespassed this law of God,remember that if you truly repent and want to live as a real Muslim you can go to the Lord and ask His forgiveness.''Innallaha Gafurur Rahim''.ALLAH KAQARA SHIRYAMU SHIRIN ADDINI.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969
07038774163

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"ALLAH BAMU IKON YI
Share:

step upp

You can stand for 2hours expecting ladies, but
you run away for 40minutes tarawih prayer
Keep wasting your strength on foolish things
A man of 60+ old is leading the prayer in the
mosque, you keep complaining he stay longer
in
prayer
Shame on you
You walk down to where you want to watch
football (you will still pay), but you said tafsir
is
too far
Please check your foot your brain is under it
You can use money to download latest music
on
naijaloaded, but you can't use your MB to
download just suratul Fatiah
Keep wasting your resources
You listen to music 9hours in a day and
Qur'an
20minut in a Day
You are walking on your brain
You delay your sleeping time because you
want
to watch football, but you can't even stand up
to
observe salat at midnight
Your productivity time is going
You are free to add yours... Be careful please
my
Brothers and sisters Ramadan is here change
before Ur Life Time is Off. May Allah accept
our
Ibadat
Share:

ALAMOMIN DA SUKE NUNA CEWA MUTUM YANADA ALJANU.

ALAMOMIN DA SUKE NUNA CEWA MUTUM YANADA ALJANU.

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

ALAMOMIN DA SUKE NUNA CEWA MUTUM
YANADA ALJANU.
ALAMOMI NA FILI
********
1. Ciwon kai marar jin magani.
2. Gujewa ambaton Allah, kamar zikiri da karatun Alqur'ani.
3. Rikicewa acikin Sallah. Ko kuma Qin yin sallar ma kwata-kwata.
4. Jiri, da kasala ayawancin lokuta.
5. Ciwon wani bangare na jiki, amma ko anje
asibiti an auna ba za'aga komaiba.
6. Fa'duwa, da kuma yin Ihu da maganganu irin na aljanu.
7. Faduwar gaba mai tsanani.
8. Rikicewar Jinin al'ada.
9. Matsananciyar mantuwa da shirita akan harkokin rayuwa.

ALAMOMI NA BOYE
********
1. Firgita da jin tsoro, musamman ma idan mutum yana zaune, ko yana tafiya shi kadai.
2. Rashin yin barci na tsawon lokaci.
3. Yawan farkawa cikin tsoro.
4. Dannau.. Wato mutum zai ga wani BAQIN ABU yazo ya danneshi. Kuma ko kayi Ihu ba za'a ji ba.
5. Namijin dare. Mace zata ga aljani yazo yana saduwa da ita..
Acikin siffar mijinta, ko kuma wani mutum wanda ta sani. Ko kuma namiji ya rika ganin aljana tana zuwa tana saduwa dashi koyaushe. Sannan zaiji ya tsani yayi aure.
6. Mummunan mafarki. Kamar karika ganin kana fa'da da Macizai da karnuka, etc.
7. Yawan fushi da 'bacin rai ba tare da dalili ba.
8. Yin dariya, kuka, ko Eehu a mafarki.
9. Mafarkin ruwa, jini, ko makabarta, ko mayanka,etc. Bayan wadannan ma akwai wasu alamomin masu
yawa.Saboda kurewar lokaci anan zamu takaita.Muna fatan Allah (s.w.t) yayi mana tsari dasu.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969
07038774163

Muh'd Abba Gana

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allahb (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

The SHORTEST but POWERFUL dua?! Do you know it?

The SHORTEST but POWERFUL dua?! Do you know it?

Daily reminder from

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Al-'Abbās, the uncle of the Prophet , came to the Prophet (peace be pon him) and said:
“Ya Rasūlullāh, teach me a du'ā'.” .
The Prophet (peace be upon him) said:
“O my uncle, say:

Allāhumma inni asaluka al-'āfiyah
(O Allāh, I ask you for 'āfiyah).”

What is 'āfiyah?
'Āfiyah means “to save me from any afflictions.
To be healthy, you are in 'āfiyah.
To have enough money
To live, you are in 'āfiyah.
To have your children protected,
you are in 'āfiyah.
And if you are forgiven and not punished, you are in 'āfiyah".
'Āfiyah means:
“O Allāh, protect me from any pain and suffering.”
This includes dunya and ākhirah.

Al-'Abbās thought about this for a while, and then he came back after a few days and said (paraphrased):
“Ya Rasūlullāh, this du'ā' seems a little short. I want something big.”
The Prophet (peace be upon him) said, “My dear uncle, ask Allāh for 'āfiyah for wallāhi, you cannot be given anything better than 'āfiyah.”
It is a simple du'ā'.
Sincerely mean what you say.
“O Allāh, I ask You to be saved from any distress, grief, hardship, harm. Don't test me.”
All of this is included in
“Allāhumma inni asaluka al-'āfiyah”

Riyadh As Saliheen,
Sunan At-Tirmidhi

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969
Share:

KA TABAYIN ZINA ???

KA TABAYIN ZINA ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

KA TABAYIN ZINA ???
Tsaya kuji irin mummunan Bala'in da zina ke haifarwa.
Zina tana cikin manyan laifuffuka, wanda dukkan shariun da Allah ta'ala ya saukar sun hadu akan
haramcin zina.Al kur'ani mai girma da Sunnar Annabi (s.a.w) da dukkan Malamai sun hadu akan haramcin zina.Qofofin zina guda biyar ne kamar haka:

1- Kallo zuwaga Abinda Allah ya Haramta.
2- Shigar batsa
3- Kalaman Batsa
4- kebancewa da matar daba muharrama ba,
5- Sha'awa Mai karfi babu aure Allah taala yace: "kada ku kusanci zina"Manzon Allah (s.a.w) yace:
Mai zina ba zaiyi zina ba, yayin da yake zina, sai an cire masa imani.Abdulllah Dan Mas'ud Ra yace:Duk Al'ummar da take zina, ta jawo wa kanta
fushin Allah, da halaka.Musulunci yayi umarni da tsare abubuwa guda shida sune kamar haka:
1-Addini.
2-Dukiya
3-Rayuka
4-Hankali
5-Mutunci
6-Nasaba
Amma zina ita kadai, tana rusa wadannan duka. Hukuncin mazinaci, mai aure kisa ta hanyar jifa.
Saurayi mara aure Bulala dari da daurin shekara.Ana tabbatar da zina ta hanya uku.

1-Shaidu guda hudu.
2-Mutun yayi ikirari da kansa.r
3-Samun mace da ciki, babu aure, ko shubha.
Bisa sharudda da aka sanyawa ko wanne.
Zina wata babbar musiface da bala'i da dukkan sharri, datake ruguza al'umma, take wargaza iyali, take tarwatsa gari, take rushe mutunci, take jawo karayar tattalin arziki, da fatara, da tsiya, dabannoba, acikin rayuwar dai dai ku, da gidaje, da
unguwanni, da gururuwa, da kasashe, da duniya baki daya.Zina itace cikakkiyar fitsara, a cikin zina ake
samun dukkan sharri kamar haka:
1- Raunin Addini
2- Raunin Akida
3-Karancin Imani
4- Rashin kunya
5- Rashin kishi
6- Rashin mutunci
7- Rashin kwarjini
8- Rashin hasken fuska
9- Duhun zuciya
10- Rashin kima
11- Rashin Nagarta
12-Rashin Nutsuwa
13- Rashin Amana
14- Fushin Allah
15- cikawa babu imani
16- Azabar Allah
Allah ya tsare mu da zuriyar mu, da dukkan
al'ummar musulmi daga afkawa bala'in zina.Wadanda sukeyi Allah ya shiryesu.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969
07038774163

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

Falalar Suratul kahfi

Falalar Suratul kahfi

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Manzon Allah (S.A.W) yana cewa:Duk wanda ya karanta SURATUL KAHFI ranar Jumu'a. Allah zai Haskaka masa da haske, har zuwa wata jumu'ar mai zuwa yana cikin haske, yana mai farin
ciki da Annashuwa cike dajin dadi.Wannan Hadisi yazo acikin Sahihu Jami'us sageer.

Allah ka jiyar damu dadinka.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969
07038774163

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Share:

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka

Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate

Blog Archive