Home »
HUKUNCIN TSARKI
» Fitar da maniyyi batare da wanka ba.
Fitar da maniyyi batare da wanka ba.
ASHE AKWAI YANAYIN DA WANI ZAI FITAR DA MANIYYI AMMA BABU WANKA AKANSA SAI DAI YAYI TSARKI KAWAI ??? ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠ Assalamu Alaikum. Yau ina dauke da wani jawabi mai ban mamaki. Kamar yadda kowa dai yasani ita janaba duk wanda ya tsinci kansa acikinta to ya wajaba a gareshi da yayi wanka. HANYOYIN DA MUTUM IDAN YA SAMU JANABA ZAI WANKA SUNE KAMAR HAKA: ♦Duk wanda ya sadu da iyalinsa, ko kuma boyewar hashafa [kan kaciya] a cikin farjin mace, to ya wajaba yayi wanka koda kuwa bai fitar da maniyyi ba. ♦ Duk Wanda yayi mafarki kuma yatashi yaga Maniyyi a jikinsa, to ya wajaba akansa yayi wanka, koda kuwa ya bushe. Amma idan ya tashi ya tabbatar bai ga maniyyi ba, to babu wanka akansa. - Wasu kuma zakuga Allah yayi musu karfin sha'awa, mace idan suka gani ko suka shafi jikinta, to zaku ga sun fitar da maniyyi. To shima wannan yanayi wanka za ayi. - A Takaice Wanda duk ya fitar da maniyyi ta hanyar jin dadi kamar tunani, kallo, ko a lokaci da yake waya da budurwarsa [mafi akasari anfi fitar da maziyyi a wannan lokaci, to tsarki kawai za ayi]. Amma idan maniyyi ne to wanka za a yi. HANYOYIN DA ZA'A FITAR DA MANIYYI AMMA MAIMAKON AI WANKA SAI KAWAI AYI TSARKI IRIN NA ALWALA BA WANKA BA. Akwai hanyoyi da dama wadanda idan wani ya tsinci kansa a ciki har yafitar da maniyyi, to wanka bai wajaba akansa ba, sai dai kawai yayi tsarki ya canja tufafi koya wanke wajan janabar. Wadanne hanyoyi ne wadannan ? Sune kamar haka: HAWA KAN DOKI: Duk wanda yahau kan doki, walau yana kilisane ko yana sassarfa koma dai me yake, inda wannan hawa kan dokin ne silar da tasa ya zubar da maniyyi to tsarki kawai zai yi. Babu wanka a kansa. WAHALA: Wanda wahala tasa yazubar da maniyyi shima babu wanka akansa. Misali: Idan mutum yana cikin wani mawuyacin hali ko bashi da lfy wannan radadin wahalar yasa ya zubar da maniyyi, to shima babu wanka akansa, tsarki kawai zaiyi. Haka ma wanda yake dakin jarrabawa sai kawai yaji ya kawo, watakila chajin kwakwalwa ne yai masa yawa harya fitar, to babu wanka akansa. (Zanci Gaba Idan Allah Yaso ya yarda...) TUNATARWA: Bawai dole saita hanyar jin dadi kawai ake zubar da maniyyi ba. Akwai hanyoyi da dama. Domin wahala ma tanasa mutum ya kawo. WALLAHU A'ALAM.
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
No comments:
Post a Comment