Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

Digon jinin mai haila a lokacin azumi.

 Digon jinin mai haila a lokacin azumi. by muhammad abba gana

Digon jinin mai haila a lokacin azumi. DAGA ZAUREN 🕋HANYAN***TSIRA🕋 Malam macece taga jini jini a pant dinta kuma tana axumi, amma jinin ba kamar yadda takeyi idan tana haila ba. Wannan yayi fari fari bashi da duhu. Kenan axuminta ya karye ? Dan Allah malam a buye sunana, kuma a taimakamin da addu,a ina yawan mafarkin mace 'yar uwata tana saduwa dani. da chan ban dauka a komai ba sai danaga posting dinku cewa aljannu na shafar mutum. Kenan malm aljana ce ta shafeni ko yaya ? AMSA __________________________ ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
Idan matar da take AZUMI taga wani jini yadigo daga farjinta, to hakika wannan Azumin nata ya karye. Kuma zata ramashi. Shi jinin haila bashida iyakacin karancin lokaci abisa mazhabin Imamu Malik (r.a). Zai iya zuwa nan take, sannan ya dauke nan take. Dangane da Kalarsa kuwa, eh yakan chanza kala awasu lokutan. Musamman ma idan an samu wani chanjin yanayin lafiyar jikin. Ko kuma chanjin abinci, ko kuma yawaitar shekaru. (YA DANGANTA DA HALITTAR JIKIN ITA MAI HAILAN). ***AMSAR TAMBAYARKI TA BIYU: EH Zata iya yuwuwa wata Aljana ko kuma aljani ya shafeki. Musamman ma idan kinajin sauran manyan alamomin kamarsu. FADUWAR GABA, CIWON KAI, FIRGITA, YAWAN BACIN RAI BABU DALILI, QAIKAYIN GABA, etc. *Awasu lokutan ALJANI NAMIJI zai iya zuwa miki da siffar mace yana saduwa dake. ko kuma yazo miki dasiffar mijinki ko saurayinki. wani lokacin kuma yazo miki da siffar wani mutum wanda kikejin kunya, etc. Kuma shima aljanin zai iya haddasa miki RIKICIN JININ AL'ADA. WALLAHU A'ALAM. DA FATAN ALLAH YA BAKI LAFIYA DAKE DA DUKKAN MASU FAMA DA IRIN WANNAN MATSALAR. *✍💖Muhd_Abba_Gana💖* www.hanyantsirah.blogspot.com 📗📘 whatsapp 09039016969 Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like 👇 👇 https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/ وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

NA RISKI LIMAN A RAKA'A TA BIYU, KOZAN IYA YIN ADDU'AR BUDE SALLAH ???

NA RISKI LIMAN A RAKA'A TA BIYU, KOZAN IYA YIN ADDU'AR BUDE SALLAH ???

NA RISKI LIMAN A RAKA'A TA BIYU, KOZAN IYA YIN ADDU'AR BUDE SALLAH ??? DAGA ZAUREN 🕋HANYAN***TSIRA🕋 Assalam Malam inada Tambaya ?. Shin idan an fara sallah kazo zakabi jam'i, zaka karanta addu'ar da ake yine bayan kabbarar harama ??? Amsa: ===== ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ . To dan uwa abin da malamai suka fada shine: Mutukar ya riski liman a mike, to zaiyi addu'ar bude sallah, sannan ya karanta fatiha, koda kuwa a raka'a ta biyu ne. Saidai idan ya riski liman a ruku'u, to zai shiga tare dashi, kuma addu'ar bude sallah zata fadi daga kansa, saboda wurin yinta yawuce. Raka'ar da kafara samu tareda liman, ita ceraka'ar farko a wajenka, wannan yasa zakayi addu'ar bude sallah, koda kuwa shi liman a raka'a ta uku yake kota hudu. Wannan shine zance mafi inganci. Idan ka riski liman a tsaye amma abin daya rage yayi ruku'u, bazai isa ka karanta addu'ar bude sallah ba, sannan ka karanta Fatiha, to zaka karanta fatiha, kabar karanta addu'ar bude sallah, saboda addu'ar bude sallah sunnah ce, karanta fatiha ga mamu kuwa wajibice a wajan wasu malaman. Domin neman Karin bayani sai kuduba Al-majmu'u na Nawawy mujallady na 3/276 da kuma Majmu'ul fataawa 30/150. Allah shine mafi sani. *✍💖Muhd_Abba_Gana💖* www.hanyantsirah.blogspot.com 📗📘 whatsapp 09039016969 Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like 👇 👇 https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/ وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

Ina masu Girman kai toku saurara kuji.🤠

Ina masu Girman kai toku saurara kuji.🤠

🤠Ina masu Girman kai toku saurara kuji.🤠 DAGA ZAUREN 🕋HANYAN***TSIRA🕋 ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ . *DARASI NA 1* KUDUBI IRIN AZABAR DA ALLAH YAKE YIWA MASU GIRMAN KAI: 1. AADAWA (mutanen Annabi Huud a.s.): Yayin da Manzo yaje musu da gargadi daga Ubangijinsu sai sukayi girman kai suke ganin cewar: Su sunfi Qarfin wani mutum yayi musu wa'azi.. WAI DON ME BA ZA'A TURO MUSU MALA'IKU BA!!! Saboda Qarfin jiki da da kuma Girman halittar da Ubangijinsu yayi musu. Sai sukayi jayayya da ayoyinsa, suka Qaryata Manzanninsa, suka bi son zuciyarsu. Daga Qarshe sai Ubangiji ya tura musu wata irin iska daga gareshi MAI QARFIN GASKE, mai tsananin Sanyi. Har tsawon Darare Bakwai da wuni Takwas wannan Masifaffiyar iskar tana bugawa akansu. Ta rurrushe gidajensu da katangun da suka kewaye garin dashi, Sannan ta Tsintsinke Kayuwansu, Tayi rugu-rugu da gangar jikinsu, nan ta barsu ayayyashe tamkar guma-guman bishiyoyin dabinai.. Allah yana bamu labarinsu ne domin mu wa'azantu mu gyara halayenmu karmu aikata irin laifukansu. Tabbas Girman - Kai sutura ce ta ALLAH. Allah ya riga ya rantse cewa duk mutumin daya ara ya yafa, to saiya Qaskantashi ya azabtar dashi. Allah ka rabamu da girman kai. ✍*💖Muhd_Abba_Gana💖* www.hanyantsirah.blogspot.com 📗📘 whatsapp 09039016969 Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like 👇 👇 https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/ وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

INA MATASA MAZA DA MATA MARASA AURE ? TO KUBUDE KUNNE KUJI.

INA MATASA MAZA DA MATA MARASA AURE ? TO KUBUDE KUNNE KUJI.

*INA MATASA MAZA DA MATA MARASA AURE ? TO KUBUDE KUNNE KUJI.* DAGA ZAUREN 🕋HANYAN***TSIRA🕋 ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ . *IN KA KARANTA KA TURAMA DAN UWANKA DAN YA AMFANA* *HATTARA MATASA MU BUDE KUNNE MUJI.* Akwai wani babban Bala'i wanda ya kunno ma al'ummar musulmi kai. Ita wannan musibah tafi afkuwa ga marasa aure. Zaka iske namiji ko mace a duk sa'ar da sha'awarsu ta motsa saisu rika wasa da al'aurarsu har sha'awar tasu ta kwanta (fitar damaniyyi) wannan shi ake kira dasuna Istimna'i ko masturbation a turance. Ganin haka yasa nayi farautar fatawa daga wasu malamai a kan ko menene hukuncin abun a musulunci ??? Sai malam yace: ''Duk maiyin ~ISTIMNA~ wato (MASTURBATION) Mace ko Namiji, Idan har bai tuba ya dainaba, ko idan har bata tuba ta dainaba. Babu mamaki daya daga cikin wadannan cututtukan guda goma (10) ya sameshi koya sameta, ko kumama sama da ciwo daya ya sameta, koya sameshi. ALLAH YA KAREMU. _Ga cututtukan kamar haka_: 1-Yana Rage Qarfin ido. 2-Rage karfin namiji ko mace awajen kwanciyar saduwa, kanaso kabiya bukatar aure amma babu dama. 3-Yana shafar lafiyar jijiyoyin dasuke da ala’ka da fitar maniyyi, ko yasa duk lokacin da mutum zaiyi fitsari sai yaji kamar ana tsira masa allura a cikin gabansa. 4-Yana haifar da wani irin ciwo acikin mutum. 5- Yana shafar lafiyar ‘ya’yan maraina, kuma ya kankantar da gaban namiji yakoma kamar na karamin yaro, idan kuma macece gabanta zai dingayin wari. 6-Yana sanya saurin fitar maniyyi a lokacin saduwa 7-Yana kawo ciwon kashin gadon baya. 8- Yana rage kaurin maniyyi, wanda kuma zai iya shafar lafiyar abin da za a haifa, koma yahana haihuwar gaba daya. 9-Yanasa kuraje ajikin mutum 10-Na karshe kuma Yana rage kaifin kwakwalwa. *MAI NEMAN KARIN BAYANI YADUBA CIKIN LITTAFIN FATAWA NA SHEKH BN BAZ DA SHEKH UTHAIMIN DA KUMA SHEKH BN JUBAIRU, JUZ’INA BIYU SHAFI NA 132-133''* Bayan malam yakare fatawarsa sai muka tuntubi wani mai kulada Lafiya shima yace: ''kasan duk maniyyin dake fita kadan ne, sabili daba ta ainihin saduwane maniyyin ya fitaba, to sauran zai ragowa kuma yayi ta taruwa a mararsa dahaka sai yajawo masa illoli ta fuskar Lafiyar sa. Misali duk maiyin wannan abu zaka iske yana shan wahala ko yayane wajen yin fitsari. To ina amfanin wannan ? 'To yan uwana sai mudage muyi aure komu yawaita azumin nafila da karatun Al-qur'ani da kasancewa da muminan abokai da gujewa fasikan abokanai. Sannan muji tsoron Allah muguji kallace-kallacen banza da wofi. Allah kashiryi masuyi. _Allah ka kiyaye wadanda basayi._ *💖Muhd_Abba_Gana💖*✍ www.hanyantsirah.blogspot.com 📗📘 whatsapp 09039016969 Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like 👇 👇 https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/ وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate