ABUBUWAN DA AKA HARAMTA GA MAI JININ HAILA
(2)
DAGA ZAUREN
HANYAN***TSIRA
ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
ABUBUWAN DA AKA HARAMTA GA MAI JININ HAILA kahina 2
5. Azumi:Bai halatta mai jinin Haila tayi azumi na farilla ko
na nafila, idan tayi kuma bai yiba, saboda haka zata lissafa azumin da tasha bayan watan ya wuce
saita ramasu.Ba'a ajiye azumi domin tsammanin gobe al'ada zatazo, amma dazarar tazo to ba azumi, dazarar bata zoba to akwai azumi, koda kinji tafiyarjinin a
jikinki amma bai fitoba to biki fara al'adaba, sai ya fitane za'a fara lissafi.
6. TABA ALQUR'ANI MAI GIRMA:
Mai jinin Haila bata taba kasantuwarsa littafi mai tsarki sannan kuma ita bata da tsarki, amma wannan baya hana idan ta ganshi zai fadi ta daukeshi ta gyara masa wuri.
7. Karatun Alkur'ani:
Mai al'ada bata karanta Alkur'ani, duk dacewa wadansu malamai suna ganin ya halatta ta karantashi daka domin kada ta manta sabanin
dauka.
8. Saduwa:
Baya halatta saduwa da mace tana al'ada, idan taqi yadda da mijinta ya sadu da ita domin tana Haila ba za'ace ta sabawaAllah ba hasalima tayi
biyayyane gareshi.
Bai halatta a sadu da mace tana al'adaba harsai al'adar ta dauke kuma tayi wankan tsarki, koda al'adar ta dauke amma batayi wankaba to bai halatta a sadu da itaba harsai tayi wanka.Ya halatta miji ya taba duk inda yakeso a jikin matarsa alokacin da take al'ada bayan tayi kunzugu inbanda daga cikbiyarta zuwa gwiwarta wannan kan bai halattaba harsai jinin yadauke kuma tayi wanka.Hakanan itama ya halatta ta taba ko ina a jikinsa
duk da tana al'ada.
9. Tabbatar Da Rashin Tsarki:Al'ada tana tabbatar da wacce take da ita bata datsarki.
10. Wajabta Wanka:
Al'ada tana wajabta wanka, wato dukkan matar datayi al'ada kuma al'adar ta dauke to wankan tsarki ya wajaba akanta.Shi kuma bayani akan abinda ya shafi wankan tsarki tuni ya gabata, da fatan Allah yayi mana jagora ya karba mana ayyukammu.
www.hanyantsira.mywapblog.com
whatsapp
09039016969
07038774163
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like: HANYAN TSIRA
Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER,y
BBM,WHATSAPP, da
sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN
ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Home »
HUKUNCIN TSARKI
» ABUBUWAN DA AKA HARAMTA GA MAI JININ HAILA
ABUBUWAN DA AKA HARAMTA GA MAI JININ HAILA
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
No comments:
Post a Comment