👹Tarkon Shaydan akan dan adam👹 DAGA ZAUREN 🕋HANYAN***TSIRA🕋 TARKUNAN SHAIDAN GUDA 6 AKAN DAN ADAM. Tarkon farko na shaiɗan shine: Yasa a kafircewa Allah ta hanyar * shirka, domin yasan idan aka mutu a haka baza'a samu rahamar ubangiji ba. Idan ka tsallake wannan sai yakaika mataki na biyu. *karamar shirka. Domin yasan tana ruguza kyawawan ayyuka. Idan ka tsallake wannan saiya kaika mataki na gaba. *Zalunci. Yasaka kadinga zaluntar jama'a domin yasan koda kana ayyukan alheri abanza, domin dasu zaka biya bashi. Mata ki nagaba *ya ruguza maka tsarin rayuwa, kazama bakasan muhammancin lokacin kaba, kana ɓata lokutanka agurin abubuwan da aka haramta maka. Mataki nagaba, *rage kaifin ayyukan alkhairi, yasa kadinga qinyin mai muhimmanci kana barin mafi muhimmanci. Sai takun karshe * yasanya ƙiyayya da zolaya awajan mutanan da yayi nasara akansu. Ya zamto kullun in banda isgili da tsokana ba abinda yakeyi da zuciyar wadanda yayi nasara akansu, har zuwa ranar mutuwa harka sauka daga kan gaskiya. Ya Allah ka tsaremu daga sharin shaytan la'ananne. Dan Allah kuyi share ta facebook/whatsapp saboda 'yan uwanku su amfana. www.hanyantsira.blogspot.com 📗📘 whatsapp 09039016969 Domin samun shafinmu a Facebook sai kuyi searching "hanyan tsirah* Koh kudanna nan kuyi like 👇 👇 https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/ وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Home »
Kariya daga Shaytan
» tarkon shaydan akan dan adam
No comments:
Post a Comment