Darasi na 6
DAGA ZAUREN
HANYAN***TSIRA
***{Darasi na 6}***
acikin bayanin
FARILLAH AINIH DA FARILLAH KIFAYA.
malam yaci gaba da cewa:
ﺛﻢ ﻣﻌﺮﻓﺔ ﻣﺎ ﻳﺼﻠﺢ ﺑﻪ ﻓﺮ ﺽ ﻋﻴﻨﻪ
SUMMA MA'ARIFATU MA YUSLEEH BIHI FARDHA AINIHY.
Ma'ana: "sannan yasan abinda zai gyara farinlan ainihinsa dashi".
... BAYANI....
Abinda ake nufi da Farillah ainih shine:
Duk wani aiki ko umarni da Allah (S.W.T) ya wajabtawa kowanne baligi mai hankali to yazo dashi shi da kansa. Shine aikin da wani bazai iya dauke masa shiba
wato kamar:
Sallah.
Azumi.
Zakka.
Hajji.
Umrah.
kalmar Shahada, da sauransu. Kamar yadda yazo acikin suratul- Asr " Ina rantsuwa da zamani haqiqah dan Adam yana cikin asara saidai wadanda sukayi imani suka kuma yi aiyuka masu kyau na kwarai".
FARILLA KIFAYA. Farillace wacce wani zai iya daukewa wani, misali: Wajibine kowa yazama likita, amma idan aka samu a gari wani yazama likita to ya daukewa sauran, sai dai kuma ayi qoqari wasuma su iya dan gaba. WALLAHU A'ALAM. Ina marhaba da duk wani qyara da za'ayi mini,kunsan dan adam akwaishi da kuskure. Allah ya bamu ikon sauke farillan dake kammu
Sai gobe zamuci gaba.
Insha Allah.
www.hanyantsira.blogspot.com
09039016969
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
No comments:
Post a Comment