Darasi na 7
DAGA ZAUREN
HANYAN***TSIRA
***{Darasi na 7}***
Acikin bayani hukunce hukuncen Sallah. Malam yace:
ﻛﺄﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﺼﻼﺓ
KA AHKAMIS SALLATI.
Ma'ana:
kamar hukunce hukuncen sallah.
BAYANI: Farkon kyakkyawan aikin da yake bin imani abaya
shine sanin hukunce-hukuncen Sallah.
Wato rukunan salla, farillan sallah, sunnoni da mustahabban sallah, da kuma abinda ya shafi sharadanta da abinda ke vatata.
Da kuma yin sallah kamar yadda Annabi (S.A.W) yakeyi ta hanyar cika ruku'u da sujjada da kuma
kyawun tsayuwa.
Kamar yadda sayyadi Abdullahi dan Abbas yake cewa: Ita cikakkiyar sallah itace wacce aka cikasa
ruku'unta da sujjadarta da kuma khushu'inta da duk wani ladubbanta, domin yin irin wannan sallar
itace zata hana mutun aikata alfasha da duk wani abin qi.
Kamar yadda Ubangiji yafada:
ﺇﻥ ﺍﻟﺼﻠﻮﺓﺗﻨﻬﻰ ﻋﻦ ﺍﻟﻔﺤﺸﺎ ﺀ ﻭﺍﻟﻤﻨﻜﺮ 0 ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻌﻨﻜﺒﻮﺕ0
"ita dai sallah tana hana aikata alfasha da duk wani aikin munkari. WALLAHU A'ALAM. Sai gobe idan Allah (s.w.t) yakawo mu lokaci irin
wannan zamuci gaba.
Insha Allah. Allah ya karvi ibadunmu.
www.hanyantsira.blogspot.com
09039016969
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
No comments:
Post a Comment