Darasi na 5
DAGA ZAUREN
HANYAN***TSIRA
***{DARASI NA 5}***
Malam yace:
..... ﺗﺼﺤﻴﺢ ﺇﻳﻤﺎ ﻧﻪ
Ma'ana:
"Ya inganta imaninsa"
Bayani:
Imani a harshen larabci shine amincewa. Amma a Shari'ance shine gaskatawa da samuwar Allah madaukakin sarki.
Kamar yadda yazo acikin Alqur'ani mai girma:
ﻗﻮﻟﻮ ﺀﺍﻣﻨﺎﺑﺎﻟﻠﻪ ... ﺳﻮﺭﺓﺍﺑﻘﺮﺓ : ١٣٦
Ma'ana"kuce:
Munyi Imani da Allah (shi kadai)" Amma a wajen malamai cewa sukayi Imani shine
gaskatawa da Annabi Muhammad (S.A.W) a cikin dukkannin abinda yazo dashi daga wajan Allah (s.w.t). Malamai suka qara da cewa imani yana da rukunai
guda shida (6) kamar yadda Allah (s.w.t) ya fada:
ﻭﻟﻜﻦ ﺍﻟﺒﺮﻣﻦ ﺀﺍﻣﻦ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻷﺧﺮﻭﺍﻟﻤﻼﺀﻛﺔ ﻭﺍﻟﻜﺘﺐ
ﻭﺍﻟﻨﺒﻴﻴﻦ ...
Manzon Allah (s.a.w) yace: (Imani shine)
kabada gaskiya da Allah da Mala'ikunsa da littattafansa da Manzanninsa sannan kayi imani da Ranar Al-qiyama kuma kayi Imani da qaddara Al-
kairinta da sharrinta.
Imani yana daduwa da qaruwar ayyukan kirki,
kuma yana raguwa saboda aikata mummunan aiki
da savawa Allah.
Malamai suna kafa hujja da fadin Ubangiji (s.w.t) cewa: "sai Allah ya qarawa wadanda suka shiriya (wata)
shiriyar" ~suratu Maryam~ Da kuma inda yake cewa:
"wanne dayan kune wanda (Al-qur'ani) yaqara masa imani, to amma su wadanda sukayi imani sai
imanin ya qaru garesu"
ALLAH YA TSARE MANA IMANINMU.
Idan Allah yakaimu zamuci gaba.
Insha Allah.
www.hanyantsira.blogspot.com
09039016969
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
No comments:
Post a Comment