Darasi na 3
DAGA ZAUREN
HANYAN***TSIRA
LITTAFIN AHALARI
***{DARASI NA 3}***
....MUQADDIMA ~1~
Malam yace:
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ .
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM"
Dasunan Allah mai Rahma mai Jinqai.
.........BAYANI
"MUQADDIMA" wajene da malamai suke bayanin Abinda littafinsu ya qunsa, da dalilin da yasa sukayi littafin. Idan mukace "Malam yace" anan muna nufin abinda mawallafin littafin yafada. Malam yabude littafinsa da bismilla domin koyi da Al-qur'ani mai girma kuma da aiki da hadisin Shugaba (s.a.w) inda yake cewa: "Duk wani aiki daya zamo ma'abocin kima da daraja ba'a farashi da Bisimilla ba, toshi mai yankakkiyar albarkane. Ma'anar ALLAHU kuwa shine abinda halitta kaf
yakamata tariqeshi a matsayin abin bautarta da gaskiya, Kamar yadda Imamu Dahhaku yafada
Daga Sayyadi Abdullahi dan Abbas (r.a) yace: ALLAH (s.w.t) yafada acikin Al-qur'ani magirma
ﺍﻟﻠﻪ ﻻﺇﻟﻪ ﺇﻻﻫﻮﺍﻟﺤﻲ ﺍﻟﻘﻴﻮﻡ .
"ALLAHU LA'ILAHA ILLAHUWAL HAYYUL QAYYUM"
Ma'ana Allah dai shine Allah (daya cancanci a
bauta masa domin) babu wani Allah abin bautawa da gaskiya sai dai shi. Rayayyene shi wanda yake tsaye da zatinsa, da kuma rayuwar halitta gaba daya. Wallahu A'alam.
In Allah ya yarda zamuci gaba daga wajen da muka tsaya.
www.hanyantsira.mywapblog.com
09039016969
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
No comments:
Post a Comment