Darasi na 8
DAGA ZAUREN
HANYAN***TSIRA
*****{Darasi na 8}*****
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
MUHIMMANCIN TSARKI.
MALAM YACE:
... ﻭﺍﻟﻄﻬﺎﺭﺓ ...
WAD-DAHARATU
Ma'ana: Da (hukunce hukuncen) tsarki".
BAYANI: Yazama wajibi wato dolene duk wani baligi mai hankali yasan hukuncin tsarki gaba daya, domin tsarki dashi akeyin.
♣Sallah.
♣Azumi
♣Dawafi da sauransu.
Allah madaukakin sarki yana cewa a suratu Baqra ayata 221 wato:
ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺤﺐ ﺍﻟﺘﻮﺍﺑﻴﻦ ﻭﻳﺤﺐ ﺍﻟﻤﺘﻄﻬﺮﻳﻦ
Ma'ana:
"HAQIQA ALLAH YANA SON MASU YAWAN TUBA,SANNANYANA SON MASU YAWAN TSARKI"
Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: "Allah bazai karvi sallar da ba'ayi tsarkiba. Awani hadisin kuma yace:
Babu sallah ga wanda bashi da Alwala.
Awani hadisin kuma yace: Wanda yayi sallah batare da Alwalaba, kuma ya gasgata hakan to shi kafirine. Kunga sallah bata yiwuwa saida tsarki abin tsoratarwar kuma shine: Manzon Allah (S.A.W) yace:
"Banbancin Musulmi da kafiri sallah" Wani hadisin kuma yace:
"Sallah itace ginshiqin Addini, wanda ya tsayar da ita, to ya tsayar da addininsa.
Wanda kuma yabarta to yabar addininsa.
Wani hadisin yace:
Farkon abinda za'a fara tambayar mutum bayan mutuwa shine sallah. Idan ta gyaru komai ya gyaru. Idan kuma ta 6aci komai ya 6aci.Gashi ita kuma Sallar ba'a karvarta saida tsarki. Ya Allah ka tsarkakemu da imaninmu. Sai gobe kuma idan Allah yakaimu lokaci kamar
wannan zamuci gaba.
Insha Allah.
www.hanyantsira.blogspot.com
09039016969
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
No comments:
Post a Comment