Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

YADDA AKEYIN SALLAR JANA'IZAH

YADDA AKEYIN SALLAR GAWA. DAN ALLAH KUTSAYA KU KARANTA. Dukkanin Malamai na Mazhabobi sunyi ittifaqi akan cewa SALLAR GAWA (JANAZAH) FARILLAH CE TA KIFAYAH. (wato irin farillar nan wacce wani zai iya daukewa wani). Saidai an ruwaito daga Asbag (daya daga almajiran Imamu Malik) cewar Shi Sunnah ce awajensa. Za'a iya yin Sallar gawa a kowanne Lokaci ko dare ko rana, Inji IMAM SHAFI'IY (R.A). Amma IMAMU AHMAD DA IMAM ABU HANEEFAH (R.A) Sunce: Makruhi ne ayi sallar Janazah a lokutan nan guda Uku. 1. bayan Sallar asubah har zuwa fitowar rana. 2. Bayan sallar la'asar har zuwa faduwar rana.. 3. Lokacin da Limamin Jumu'a yahau kan mimbari yake khudubah. Shi kuwa IMAMU MALIK (R.A) Yace: Za'a iya yin Sallar Janazah a kowanne lokaci in banda lokacin fitowar rana da kuma lokacin faduwarta, yace Makruhi ne. SHARUDANTA: Dukkan Maluman Mazhabobin sunyi ittifaqi akan cewa: Wadannan sune sharudan ingancin Sallar Janazah: Tsarki da alwala. Suturce Al'aurah. * Kallon Alqiblah. Amma Sha'aby da Ibnu Jareer sunce: Za'a iya yi ko ba tareda alwala ba. Imam Shafi'iy da Abu Yusuf sunce Limami yana tsayawane adaidai kan mutum Namiji. Ita kuma mace Liman zai tsayane adaidai tsakiyar ta. Amma IMAMU MALIK DA IMAM ABU HANEEFAH Sunce: Liman zai tsayane adaidai Qirjin Namiji, ita kuma mace zai tsaya ne adaidai adaidai tsakiyarta. KABBARORINTA: Anayin Kabbarori hudu asallar janazah abisa ittifakin Mazhabobin nan hudu. Saidai an ruwaito Kabbara 3 daga Imam Ibnu Sireen. Sannan akwai wata ruwayar daga Abdullahi bn Mas'ud (rta) yace: "Manzon Allah (saww) yayi kabbara 9 abisa Janazah, Sannan yayi 7, Sannan yay 5, Sannan yayi 4. Kuyi ta kabbarawa mutukar Limaminku ya kabbara. Koda ya Qara abisa hudu to sallar bata 'baci ba". Imamush-Shafi'iy yace Zaka cira hannuwanka zuwa kafadunka ayayin dukkan kabbarorin. Amma IMAMU MALIK DA IMAM ABU HANIFAH sunce bazaka cira hannuwanka ba saidai akabbarar farko kawai.. Karanta Fatiha bayan kabbarar farko, Farilla ne awajen Imam Shafi'iy da Imamu Ahmad. Amma Imamu Malik da Abu Haneefa Sunce: BA ZAKA KARANTA KOMAI BA DAGA CIKIN AYOYIN ALQUR'ANI. Sannan anayin Salatun Nabiyyi (saww) sannan kuma sai Addu'a ga mamacin da sauran al'ummar musulmi abayan Kabbara ta biyu data uku da ta hudu respectively. Sannan mutum zaiyi sallama ne guda biyu abisa Mazhabobi uku. Amma Hanbaliyya sunce Sallama daya zakayi a damanka. Aduba Samrud-dany Babin Sallar Janazah da kuma Rahmatul-Ummah shafi na 81. WALLAHU A'ALAM. Allah ya yasa mu cika da imani. www.hanyantsira.mywapblog.com
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate