Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

Ladabin shiga bandaki (1).

Ladubban Shiga Bandaki (Fitsari Ko Bayangida):
Akwai tsari na ladubba da musulunci yake dasu a
lokacin da mutum yake niyyar kewayawa.
Wannan zai nuna maka cewa addinin musulunci ya
karade komai:
(1) Anbaton Allah:
Ana bukatar kafin kashiga ka ambaci Allah domin
ba'a anbaton Allah a makewayi, kuma kanemi Allah
ya tsareka daga sharrin aljanu, domin irin
wadannan wurare matattarace tasu.
Sai ya karanta wannan addu'a yace:
ﺑِﺴْﻢِ ﺍَﻟﻠﻪِ، ﺍَﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻲ ﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﻚَ ﻣِﻦَ ﺍَﻟْﺨُﺒُﺚِ ﻭَﺍﻟْﺨَﺒَﺎﺋِﺚِ
Ma'ana
Da sunan Allah, Ya Allah lalle ni ina neman
tsarinka (Daka tsareni) daga aljanu maza da kuma
aljanu mata.
Idan kuma zaka fito sai kace:
ﻏُﻔْﺮَﺍﻧَﻚَ، ﺍَﻟْﺤَﻤْﺪُ ﻟﻠﻪِ ﺍَﻟَّﺬِﻱ ﺃَﺫْﻫَﺐَ ﻋَﻨِّﻲ ﺍَﻷَﺫَﻯ ﻭَﻋَﺎﻓَﺎﻧِﻲ
Ma'ana:
Ina neman) gafararka Allah, Dukkan godiya ta
tabbata gareka, wanda ya rabani da wannan
kazantar kuma ya bani lafiya.
Kusani ba'a shiga bayi da dukkan wani abu da
yake dauke da sunan Allah, kamar zobe, ko carbi.
Hakanan kuma ba'a katse bayangida da dukkan
wani abu da yake da sunan Allah.
(2) Fara Gabatar Da Kafar Hagu A Lokacin Shiga.
kafar dama kuma lokacin fitowa.
(3) Ayi A Tsugunne:
kada mutum yayi fitsari ko bayan gida a tsaye, sai
dai idan wurin kangone ko yana tsoron fitsarin ya
fallatso masa, sannan ba wanda zai ganshi.
Darasi mai zuwa zanci gaba daga yadda muka
tsaya.
Insha Allah.
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate