Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

Ladabin shiga bandaki (2).

(4) Tabbatuwa ACikin Sutura:
Ana bukatar kada mutum ya yaye al'aurar sa tun
yana tsaye, sai ya tsugunna yayi dab da kasa saiya
daga suturarsa, domin ba'a yarda wani yaga
al'aurar waniba, idan ba miji da mataba, amma
halin ko inkula da wasu ke nunawa na bayyanar
da al'aurarsu ga kowa muddin jinsi gudane
wannan bai daceba, sai kaji wani yace' Ai duka
mazane, abinda kake dashi ina dashi, wannan ba
koyarwar musulunci bace.
Hakanan mata, wannan zai kaika kaga maza sun
tube suna wanka lokaci guda a dakin wanka guda,
haka namma mata, wai sun dauka abinda yake
haram shine namiji yaga al'aurar mace ko mace
taga al'aurar namiji.
Kai wani lokaci kana tafiya a cikin mota sai kayi
arba da wani gabjejen kato yana wanka a rafi, wani
kuma a gefan titi yakafe mashin ko ya ajiye kayan
tallansa.
Duk wadannan ba kyawawan halaye bane, mutum
musulmi ya nisance su.
(5) Yafi Bada Karfi A Kafarsa Ta Hagu:
Abinda a kafiso shine mutum yafi bayar da karfinsa
akan kafarsa ta hagu.
(6) Sannan Yabude Tsakanin Cinyoyinsa:
Kada ya matse, ballantana yasa matsattsiyar tufa
wacce idan yana fitsari na gaban ne kawai zai fita,
sannan idan ya mayar cikin wando sauran ya
gangaro.
Allah ya sawwake.
(7) Ya Nisanci Inda Ruwa Yake:
Musulunci bai yadda mutun yayi fitsari ko bayan
gida a inda ruwa yakeba ko kusa dashi, dan
wannan zai haifar da cututtuka.
Darasi mai zuwa zanci gaba daga yadda muka
tsaya.
Insha Allah.
Allah yasa muna aiki da abinda muke karantawa.
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate