Home »
HUKUNCIN TSARKI
» Ladabin shiga bandaki (4).
Ladabin shiga bandaki (4).
(12) Nisa Da Jama'a: Ana bukatar dukkan wanda zaiyi bayan gida yayi nesa da jama'a ta yadda ba zasu ganshiba kuma baza suji nishin saba, bazai yi kyauba ace kana bayan gida mutane suna ganinka ko suna jin nishinka, koda a bayan bishiya ko ganyan kargo sai ka boye, amma sau da yawa mutane suna tafiya a mota da motar ta tsaya sai kaga kowa ya tsaya dab da motar, sannan ba za'a tafi a barshiba. (13) Kada Ya Fuskanci Alkibla: Wato inda mutum yake kallo lokacin sallah, kuma kada ya juya mata baya, wannan idan a dajine, amma idan a gidane to da sauki. Darasi mai zuwa zanci gaba. Insha Allah.
No comments:
Post a Comment