Home »
HUKUNCIN TSARKI
» Bambanci tsakanin, Maniyyi, Maziyyi, Waziyyi
Bambanci tsakanin, Maniyyi, Maziyyi, Waziyyi
BANBANCI TSAKANIN ♣ MANIYYI ♠ MAZIYYI ♣ WADIYYI. A kwai sakonni da dama daga 'Yan uwa da sukayi tambaya (wata tambayarma tafi wata guda) akan banbancin wadannan ruwaye. Hakan yanuna kishinsu ga addini wanda yasa mukayi tunanin sanyawa a fili wadanda basu tambaya bama su amfana. Nadade ina tunanin sawa dan sauwakewa kaina amsa tambayoyi daya bayan daya. Amma inajin NAUYI wajen bada amsa yasa nakasa, yauda aka kumayi mini tambayar naga yadace in sanya tunda. "INNALAAHA LA YASTAHYI MINAL HAQ. Nana A'isha tana cewa: "Allah ya jikan MATAN MADINA kokadan KUNYA bai taba hanasu neman sanin addininsu ba" Idan mukace zamuci gaba dajin nauyin tambaya ko bada amsawa saboda KUNYA to zamu rayu cikin jahilci, wanda wannan ba uzuri bane a wurin Allah. Dan haka ga banbancin dake tsakaninsu: {1}. MANIYYI ========== Maniyyin namiji: ruwane mai kauri FARI wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji. Sannan yana tunkudo juna lokacin dayake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko damammen gari, Idan yabushe yana kamshin kwai. {1A}. MANIYYIN MACE: Ruwane TSINKAKKE, MAI FATSI-FATSI, wani lokacin kuma yana zuwa FARI, wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji. Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, zataji tsananin sha'awa da dadi lokacin fitowarsa. Kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino ko damammen gari, Idan ya bushe shima yana kamshin kwai. Sannan sha'awarta zata yanke bayan fitowarsa. HUKUNCIN FITAR MANIYYI shine: YANA WAJABTA WANKA. {2}. MAZIYYI: ========== Ruwane tsinkakke dayake fitowa, yayin karamar sha'awa, kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce kakeso, ko matarka, ko kallon matar ko namijin da kike sha'awa. Haka kuma yana fitowa yayin wasa tsakanin miji da mata, saidai shi baya tafiyarda sha'awa, kuma wani lokacin ba'a sanin yafito. Malamai suna cewa: Maziyyi yafi fitowa mata, fiye da maza. HUKUNCINSA SHINE: A WANKE FARJI GABA DAYA, DA KUMA INDA YA SHAFA, KUMA A SAKE ALWALA. {3}. WADIYYI ========== Wani ruwane mai KAURI dayake fitowa a karshen fitsari, ko kuma karshen bahaya ga wanda yajima baiyi jima'i ba, yana fitowa ga wadanda basuda aure, ko wadanda sukayi nisa da abokin rayuwarsu ta aure, ina nufin namiji ko mace. YANA DAUKAR HUKUNCE-HUKUNCEN FITSARI. Allah shine mafi sani. NAN GABA KADAN ZAN KUMA BAYANI AKAN YADDA AKE WANKAN HAILA DANA JANABA IDAN ALLAH YASO KUMA YA YARDA.
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
No comments:
Post a Comment