
Assalamu Alaikum Malam gidanmu yana kusa da masallaci, muna jiwo kiran sallah da ikama ta lasifika, koya halatta in bi sallar jam’i daga laspika ??? (Daga Husna Ahmad). AMSA: ----- DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI. To ‘yar’uwa wannan mas’alar takasu kashi biyu: 1- Idan ya zamana dakinki yana like da masallacin, to tabbas wannan ya halatta, saboda Nana A’isha (R.A) tabi sallar kisfewar rana daga ‘dakinta, a zamanin Annabi (s.a.w) kamar yadda Bukhari ya rawaito hakan a hadisi mai lamba ta: 184, sannan Abdur Razzaq ya rawaito cewa: Ta kanbi ragowar salloli daga dakinta” kamar yadda yazo a littafinsa na (al-Musannaf, hadisi mai lamba ta: 4883). Saboda ‘dakinta ajikin masallacin Annabi (s.a.w) yake. 2. Idan ya zama ‘dakin baya kusa da masallacin, to zance mafi inganci shine: Bai halatta kibi ba, saboda a zamanin Annabi (s.a.w) sahabbai suna haduwa a wuri ‘daya ne idan zasuyi sallar jam’i, basa rarrabuwa. Wannan sai yake nuna cewa, hakan shine siffar sallar jama’i, sannan jera sawu a sallah, wani yana bin wani dole ne a sallar jam’i. Allah Shine Masani.
No comments:
Post a Comment