MANZON ALLAH (S.A.W) YACE:
Lallai acikin aljannah akwai wata kasuwa da
ake zuwanta a ranar juma'a Idan mutane sukaje
wannan kasuwa sai wata iska tazo musu ta arewa
saita shafi fuskokinsu da rigunansu, Sai suqara yin
kyau
Sai sukoma wajen iyalansu.
A lokacin suma sun qarayin kyau
sai iyalansu suce musu wallahi anqara muku kyau.
Sai suma sukalli iyalansu suga sunqara kyau.
Sai suma suce musu lallai kuma anqara muku kyau
bayan fitarmu.
Sahih Muslim:2833
Ya Allah kasa muna cikin wadannan salihan bayi.
Home »
Rayuwar Aljannah
» AKWAI WATA KASUWA ACIKIN ALJANNAH.
No comments:
Post a Comment