MAI RIYA YANA DA ALAMOMI GUDA UKU.
Sayyadina Ali (R.a) Yace:
"Mai RIYA yana da alama guda Uku.
1. Idan shi kadaine kasala tana hanashi.
2. Idan kuma yana tareda mutane to yana zama
mai nishadi, saiya kara yawan aiki duk yayin da
aka yabeshi.
3. Yana ragewa idan aka zarge shi.
Al-Fudail dan Iyadh yace:
"Idan kabar gabatar da aiki don jin tsoron Mutane
to kayi Riya.
Idan kuwa kayi aiki don mutane su gani to kayi
karamar shirka.
Yin Ikhlasi kuwa shine Allah ya kareka ga barin yin
guda biyun.
Muna Rokon Allah Yaa Karemu Daga Shirka da
Riya, Ya azurtamu Da Ikhlasi cikin ayyukanmu da
zantukanmu, motsinmu dayin shirunmu.
hanyantsira.mywapblog.com
Home »
» Alamomin maiyin Riya guda 3.
No comments:
Post a Comment