Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

Yadda ake wankan janaba

YADDA AKE YIN WANKAN JANABAH.
==============
Salam, malam dan Allah kayi mana karin bayani
akan wankan janaba da wankan haila dan har
yanzu akwai masu damuwa akai.
(daga Abdullahi mani babba)
AMSA
====
Da farko Idan Mutum yashiga Ban-'daki (bathroom)
Zai farane da wanke Najasar dake tare dashi.
Ma'ana, Zai Fara wanke Al'aurarsa, da kuma duk
wuraren da Maniyyi (ko jinin) ya taba ajikinsa.
(Misali tun daga Cibiyarsa har zuwa cinyoyinsa).
* Kuma Zai Qulla niyyah ne yayin da yake wanke
Al'aurarsa.
* Sannan saiya wanke dukkanin Gabobinsa na
Alwala.
Amma sau dai-dai ko 2 ko 3 duk wanda mutum
yayi daidaine.
* Idan kaga dama zaka bar Qafafunka, Sai akarshen
wankan.
* Sannan Saika wanke Kanka Sau Uku.
(tare da wuyanka da fuskarka gaba dayanta).
* Saika wanke tsagin Jikinka na Dama, har zuwa
Kafarka ta dama.
* Sai kuma tsaginka na Haggu, kahada har
Qafarkata haggu din.
* Ya zama wajibi kacire zobe daga hannayenka
(Idan ya matseka) kuma dole ka Tsetsefe dukkan
yatsunka na hannu dana Qafa.
* Ka chuda Kafarka sosai.
Musamman idan inhar kanada kaushi.
* idan kazo wanke kowanne tsagi, ka tabbatar da
cewa kana Chutchuda Bayanka sosai.
* Idan kuma hannunka baya iya kaiwa, sai kasamo
wani Tsumma ko Kyalle mai tsafta, KaJiqa-shi,
Sannan ka Chutchuda dashi.
* dole ne ka chutchuda Ko ina ajikinka.
Musamman ma idan kana da Qiba.
* Dolene Ka wanke Duburarka sosai tun farko.
Kada kayi la'akari da cewar "Ai bakayi bahaya ba".
A'a. Ai nan dinma jikinka ne.
Idan baka wanke taba, to wankanka bai yiwu ba.
* Ka kula da Ramin cibiyarka.
Ka tabbatar cewa Ruwa yashiga har nan.
* Ya zama dole 'yan uwa mata su tabbatar cewa
Ruwan ya ratsa har cikin Kitsonsu yayin wankan.
* Namiji idan yanada gemu, to lallai ne ka tabbatar
cewa ka Tsetsefe shi komai Kaurinsa da duhunsa.
~ ~ ~ ~ ~ ~ ~
NOTE: Zaka iya amfani da wannan alwalar wacce
kayi yayin wankanka.
Indai har baka sake ta'ba al'aurarka ba bayan kayi
alwalar.
HAKA AKE YIN WANKAN JANABA, HAILA, NIFASI,
DA KUMA WANKAN SHIGA MUSULUNCI.
Wallahu A'alam.
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate