"KA SHAGALTU DA LAIFUKANKA KADA KA
SHAGALTU DA LAIFUKAN MUTANE"
Duk yayin da ka shagaltu da ganin laifukan
mutane, kakutsa cikin neman inane kura-kuran
mutane suke ???
Ma'ana: Kai baka yiwa kanka muhasaba (Hisabi),
to, laifunka zasu yawaita batare daka ankara ba.
Masu iya magana suna cewa:
LAIFI TUDU NE.... Saika take naka sannan zaka
hango na wani!
Duk mutumin da bai d'auki kansa mai laifi ba, baya
dinga bibiyar irin aikin da yake aikatawa yana
tantancewa, baya zama mai ganin kura-kuran
kansa! To, lallai akwai nadama a qarshen
rayuwarsa.
Domin kuwa zai tattara zunubai masu tarin yawa a
kansa, tunda ya kawar da kansa daga ganin
laifukansa, ya shagaltu da laifukan al'umma, ta
inda ganinsa ya taqaitu ga ganin laifukan mutane.
'Yan'uwa mu gyara ayyukanmu, mu wanke
zuqatanmu, mu rinqa yiwa kawunanmu hisabi, mu
kasance masu tsanin tuhumar kawunanmu, tareda
tuba daga munanan ayyukanmu, ta wannan sai mu
kasance bayi na qwarai, dalilin haka sai Allah ya
tausaya mana ya gafarta mana ya shigar damu
cikin rahmarsa.
*******************
Ya Allah ka gafarta mana ka rabamu da son zuciya,
ka shiryar damu hanya madaidaiciya, ka tabbatar
damu a kan tafarkin tsira yazuwa Al-jannah.
www.hanyantsira.mywapblog.com
Home »
GUZIRI MAFI KYAWU
» KADA KA SHAGALTU DA LAIFUKAN MUTANE [08:49 PM, 18-Mar-15]
KADA KA SHAGALTU DA LAIFUKAN MUTANE [08:49 PM, 18-Mar-15]
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
No comments:
Post a Comment