Abubuwan da aka haramtawa mai janaba.
ABIN DA AKA HARAMTAWA MAI JANABA YINSA (MAZA DA MATA). Sau da yawa mukan samu kanmu a halin janaba, kuma mu aikata wasu abubuwa da shari'a bata halatta mana ba. Amma yanzu InSha Allah zan sanar da 'yan uwa abubuwan da basu halatta muyi suba a yayin da muke cikin Janaba. 1- Assalat (Sallah) 2- Adawaf (Dawafin dakin Allah) 3- Shafar Alqur'ani Mai Girma ko kuma Daukarsa. 4- Karatun Qur'ani: An haramtawa mai janaba karatun Qur'ani, bai halatta ba a gareshi, saidai wasu malaman suna cewa, zai iya karanta wata aya domin neman tsari. Janhurun Malamai sun hadu akan haka. 5- Shiga Masallaci: Ya haramta akan mai janaba ina mai kafa hujja da hadisin Nana Aisha (R.A) tace: "Manzo (S.A.W) yace: Ku fuskanci wadannan gidajen daga masallaci, domin cewa baya halatta ga mai Haidha da Janaba shiga Masallaci". Abu dawud ya rawaito. An karbo daga Ummu Salmah (R.A) tace: "Annabi (S.A.W) yashiga masallaci, sai yayi magana da murya mai karfi, yai kira da madaukakiyar muryarsa, yace: Hakika masallaci baya halatta ga mai Haidha da kuma mai Janaba." Ibn Maja da Dabari. Allah yasa mugane kuma mu amfana da abin da muke karantawa.
No comments:
Post a Comment