Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

Ladabin shiga bandaki (3).

(8) Yarufe Kansa:
Anason wanda yake bayan gida yarufe kansa a
daidai lokacin da yakeyi.
Domin koda wani yayi kuskuren ganinsa toshi bai
ganshiba, abin zaizo da sauki, amma ba zakaji
dadiba kana bayan gida kahada ido da wani, wanda
zai iya zama dalibinka ne ko suruki ko da'.
(8) Kada Ayi Magana:
Anhana mutum yana bayan gida yana Magana,
saidai idan akwai dalili mai kwari.
Kamar kaga makaho ya nufi rijiya ko karamin yaro.
(9) Kada A Tari Iska:
An hana idan mutum zaiyi bayan gida a (daji)
yatari iska, domin zai busowa jama'a warin bayan
gidansa, sai yayi nesa, ya kuma duba ina iska take
kadawa.
(10) Kaucewa Rami:
Ba'a yarda idan zakayi fitsari ko bayan gida kayi a
ramiba saidai idan kaika haqashi, domin bakasan
menene yake cikin ramin ba, takan yiwu akwai
mugun abu.
(11) Kaucewa Wuraren Tsinuwa:
Wadannan wurare sune wuraran da mutane suke
yawan tsinema dukkan wanda yayi musu
bayangida a wurin, wadannan wurare sune:
(a) Inda mutane suke zama su huta, jikin bangone
ko karkashin bishiya komadai inane.
(b)Kan hanya:
Akwai rashin mutunci mutum yazo kan hanya ya
gicciya bayangida, wannan dabi'a musulunci bai
yarda da ita ba.
(c) Mashayar ruwa:
Hakanan baya cikin karantarwar musulunci mutum
yazo inda al'umma suke diban ruwa rafine ko wani
gulbi ko gindin fanfo koma dai inane ya aikata
wannan ta'asa.
Wadannan wurare uku musulunci ya hana a aikata
wannan danyan aiki a wurin, domin mutum yana
jawa kansa tsinuwa.
Allah ya tsaremu.
Sai darasi mai zuwa zanci gaba daga yadda muka
tsaya.
Insha Allah.
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate