(12) Nisa Da Jama'a:
Ana bukatar dukkan wanda zaiyi bayan gida yayi
nesa da jama'a ta yadda ba zasu ganshiba kuma
baza suji nishin saba, bazai yi kyauba ace kana
bayan gida mutane suna ganinka ko suna jin
nishinka, koda a bayan bishiya ko ganyan kargo
sai ka boye, amma sau da yawa mutane suna
tafiya a mota da motar ta tsaya sai kaga kowa ya
tsaya dab da motar, sannan ba za'a tafi a
barshiba.
(13) Kada Ya Fuskanci Alkibla:
Wato inda mutum yake kallo lokacin sallah, kuma
kada ya juya mata baya, wannan idan a dajine,
amma idan a gidane to da sauki.
Darasi mai zuwa zanci gaba.
Insha Allah.
Home »
HUKUNCIN TSARKI
» Ladabin shiga bandaki (4).
No comments:
Post a Comment