LABARIN WANI SARKI MAI HIKMA. DAGA ZAUREN HANYAN***TSIRA Dan uwa/ yaruwa bani minti biyu ka daure ka karanta zuwa karshe: tare dayin share wa yanuwa:;.... LABARIN WANI SARKI MAI HIKIMA. Acan wajajen kasashen gabas akai wani Sarki daya dade akan gadon sarauta yana mulki, daya fuskanci ya tsufa sai ya yanke shawarar yin murabus, to amma inda Gizo ke sakar shine wanda zai gajeshi, maimakon kawai ya zabi wani daga cikin yayansa ko a mukarrabansa (yan majalisarsa) sai yasa aka tara dukkan samarin garin a fadarsa, yace musu, " Shekaru sun cin mini, lokaci yayi a gareni da zan koma gefe in nada Magaji, kuma a cikinku na yanke shawarar zaba" Matasan nan duk suka rude wannan ya kalli wannan, wancan yadubi wancan, zuciyarsu cike da tunanin ta yaya ? sarkin yaci gaba da cewa: Yanzu zan baku iri na shuka (seed) kowa yaje ya shukashi, yabashi ruwa ya kula dashi har tsawon shekara guda, akawo min naga irin abin da zaku samu, duk wanda na zabi tasa shine sabon sarki a wannan masarauta. Aka raba wa matasa iri daban-daban kowa yatafi gida cike da burin zama sarki idan shuka tayi kyau. Cikin matasan nan da aka ba akwai wani da ake kira Bilal, da zuwansa gida sai ya shaidawa Mahaifiyarsa dukkan yadda ta wakana a fadar Sarki, tayi murna dajin wannan labari, nan take ta taimaka masa da tukunya da kasa mai kyau wadda zatayi saurin shuka, suka shuka irin nan na sarki. Kowace rana Bilal yakan ba shuka ruwa, sai yayi tsaye yana kallo yaga yadda zata fito,haka yayi tayi har wajen sati uku, amma abin mamaki ba abin daya fito daga kasa, yazuba ido har zuwa na hudu na biyar kai har na zuwa shida amma ko tsagewa kasar batayi ba, ballatana shuka ta fito. Zance ba haka yake ba acikin gari, domin matasa sai murna suke shukarsu sai girma take tanayin kyau, hakan ba karamin tayar da hankalinsa yayiba, sannan gashi duk inda yaje maganar kenan, sai yayi shiru kurum, bai sanar da kowa abin dake faruwaba. A kwana a tashi har wata shida suka shude, matasa a gari nacike da farin ciki, shi kuwa Bilal na cikin damuwa, yanata zuba ruwa ba shuka, kullum zuluminsa yazai fuskanci sarki da tukunya ba komai. Ina ya Allah,babu ya Allah, shekara kwana,inji yan magana, ranar da Sarki ya alkawarta tacika, gari ya zama tamkar ranar Sallah, ko'ina matasa zaka gani dauke da tukunyar bishiya iri daban-daban sunyi kyau ga tsayi, sun wa fadar Sarki tsinke. Amma al'amarin Bilal kuwa awannan rana yatashi ne cikin fargaba har saida Mahaifiyarsa ta kwantar masa da hankali ta ce "kaje da abin da kasamu ya fi kin zuwa kanada gaskiya, kuma kokarin kake nan" Da shigarsa, sai fada ta kaure da dariya da sowa, ana nuna shi da tukunyarsa ba komai, yasami gefe daga baya can kurya ya rakabe tareda sunkuyar da kai kasa, gabansa na dakan uku-uku. Can jimawa sai Sarki ya suitors fada, kowa yaduka yakai gaisuwa sannan akai shiru ana sauraransa, zuciyoyi cike da fata da burin dacewa a samu sarauta, haka abin yake ga jama'ar gari wadanda sukai dako ko Allah zaisa nasu yafito cikin nasara. Sarki yayi murmushi gami da tashi yana tafiya cikin kasaita da ganin shuke-shuke iri daban- daban. "Yace yau itace ranar dana alkawarta muku cewa daya daga cikinku zai zama sabon Sarki a masarautar nan kuma na yaba da abin da idanuna suke ganemin, a saboda da haka...katsam! saiya hango tukunya ba komai aciki mutum a gefe na boyewa, nan da nan yayi umarni da azo da ita damai ita. Bilal yaji wata rashin lafiya gaba daya ta kamashi, cikinsa sai kululu yakeyi, yaji kafafuwansa sun kasa daukarsa "shikenan na kashe irina za a kasheni" yafada a zuciyarsa. Bai gama tunanin yaji anyi sama dashi sai gaban Sarki, ai tuni sai fada ta rude da dariya da kyakyaci da sowa, wasu harda faduwa dan mugunta. Sarki ya daga hannu nan take kowa yayi shiru, waje yayi tsit. "ya sunanka?" Sarki ya tambaya. "Suna na Bilal" yafada jiki na rawa. Sarki ya dubeshi sannan ya dubi taron jama'a cikin murya mai karfin sauti da izza ya ce "Kuyi gaisuwa ga sabon Sarkinku mai suna Bilal". Habawa! ai sai wuri yarude da gunguni na mamaki, idanu sukai zazzago baki a bude cikeda tambayoyi, ya mutumin da yakasa shuka iri na tsawon shekara zai zama Sarkinsu?. Bilal yadago kai a firgice, shin abin da kunnuwansa sukaji gaske ne ko Almara ko mafarki? Sarki ya sharesu yaci gaba da maganarsa kawai yana mai cewa. "Shekarar data wuce nabaku iri daban-daban a shuka a kawo min yau" yadan nisa can yaci gaba. "To amma baku sani ba DAFAFFEN IRI nabaku (wanda baya shuka) da kukaga yaki fitowa sai kuka canza da wani daban, Bilal kadai ne MAI GASKIYA da bai canzaba, yakawo min tukunya ba komai, dan haka kowa yayi gaisuwa ga sabon Sarki ku kwashe wadannan ciyayin kuban wuri". To masu karatu anan na kawo karshen wannan labari nawa. Ina. fata an fa'idantu da nishadantuwa, zan rufeda wannan hadisin dan sakon yafi shiga: Monzan Allah (S.A.W) yace: Gaskiya tanasa ayyuka nagari, ayyuka nagari suna kaiwa zuwa Aljanna. Mutum bazai gushe yana fadar gaskiya ba harsai an rubata shi a matsayin mai gaskiya awurin Allah. Karya na kaiwa zuwa ayyuka marasa kyau, wanda suke kai mutum wuta. Mutum bazai gushe yana karya ba harsai an rubuta shi Makaryaci a wurin Allah. "(Bkhr 8:116). Ubangiji Allah yabamu ikon fadin gaskiya dayin gaskiya. Ya tsaremu da fadin karya. www.hanyantsira.blogspot.com whatsapp 09039016969 Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/ وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته