Digon jinin mai haila a lokacin azumi.
DAGA ZAUREN
🕋HANYAN***TSIRA🕋
Malam macece taga jini jini a pant dinta kuma tana axumi, amma jinin ba kamar yadda takeyi idan tana haila ba. Wannan yayi fari fari bashi da duhu.
Kenan axuminta ya karye ? Dan Allah malam a buye sunana, kuma a taimakamin da addu,a ina yawan mafarkin mace 'yar uwata tana saduwa dani. da chan ban dauka a komai ba sai danaga posting dinku cewa aljannu na shafar mutum. Kenan malm aljana ce ta shafeni ko yaya ?
AMSA
__________________________
ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
Idan matar da take AZUMI taga wani jini yadigo daga farjinta, to hakika wannan Azumin nata ya
karye. Kuma zata ramashi. Shi jinin haila bashida iyakacin karancin lokaci abisa mazhabin Imamu Malik (r.a). Zai iya zuwa nan take, sannan ya dauke nan take.
Dangane da Kalarsa kuwa, eh yakan chanza kala awasu lokutan. Musamman ma idan an samu wani chanjin yanayin lafiyar jikin. Ko kuma chanjin abinci, ko kuma yawaitar shekaru.
(YA DANGANTA DA HALITTAR JIKIN ITA MAI HAILAN).
***AMSAR TAMBAYARKI TA BIYU: EH Zata iya yuwuwa wata Aljana ko kuma aljani ya
shafeki. Musamman ma idan kinajin sauran manyan alamomin kamarsu. FADUWAR GABA, CIWON KAI, FIRGITA, YAWAN
BACIN RAI BABU DALILI, QAIKAYIN GABA, etc.
*Awasu lokutan ALJANI NAMIJI zai iya zuwa miki da siffar mace yana saduwa dake. ko kuma yazo miki dasiffar mijinki ko saurayinki. wani lokacin kuma yazo miki da siffar wani mutum wanda kikejin kunya, etc. Kuma shima aljanin zai iya haddasa miki RIKICIN
JININ AL'ADA.
WALLAHU A'ALAM.
DA FATAN ALLAH YA BAKI LAFIYA DAKE DA
DUKKAN MASU FAMA DA IRIN WANNAN
MATSALAR.
*✍💖Muhd_Abba_Gana💖*
www.hanyantsirah.blogspot.com
📗📘
whatsapp
09039016969
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like 👇 👇
https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/
وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
No comments:
Post a Comment