Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

tambaya


MENENE HUKUNCIN MACEN DA TAYI AURE KAFIN TAYI ISTIBRA'I ??? DAGA ZAUREN HANYAN***TSIRA Salam Malam Ya kamata ace nayi istibra’i kafin nayi aure, amma banyiba, har nayi aure, yanzu haka ina jini na farko banyi tsarki ba, amma bada wanda na aikata laifin cikin nayi aure ba. Yaya ingancin aure na? Gani nake kamar babu auren ko ? (Dan Allah ka6oye sunana) AMSA ========================== ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ . DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI. Da farko dai inayi miki wasici da tsoron Allah, saboda zunubin da kika aikata na zina, amma gameda aure, shi aurenki yayi, saidai yinsa bayan istibra’i shine yafi alkhairy, sannan ya wajaba mutukar kinsan kinada ciki to bai halatta kibawa sabon mijinki dama ya take kiba ma'ana ya sadu dake. Saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi: “Duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa”. (Abu-Dawud: hadisi mai lamba 1847). Don haka, ya wajabta a gareki kiyi stibra’i kafin mijinki yasadu dake, sannan istibra’i jini dayane, idan kuma har kin dauki ciki, kafin kiyi istibra’i, in kin haihu kafin wata shida to ba ‘dansa bane, amma in har kin haihu bayan wata shida (6) daga fara saduwarku, to ‘dansa ne, mutukar ba’a samu shaidar da take nuna kinada ciki ba, tun kafinku fara saduwar. WALLAHU A'ALAM DoMIn neman Karin bayani kuduba: (Al-mugny na Ibnu Qudaamah, mujallady na 8\79). www.hanyantsira.blogspot.com whatsapp 09039016969 Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/ Domin samun shafinmu a whatsapp seku dannah wannan, https://chat.whatsapp.com/2AKME7ArAoc5mbmV0dDkWe وسلم عليكم ورحمت وبركاته
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate