Darasi na 9 DAGA ZAUREN HANYAN***TSIRA ***{Darasi na 9}*** Hukunce Hukuncen Azumi. Malam yace: ........... ﻭﺍﻟﺼﻴﺎ ﻡ .......... Ma'ana: Da (sanin hukunce hukuncen) Azumi. BAYANI: Wajibine akan duk wani mukallaf mai hankali yasan hukuncin Azumi, wadannan kuwa sune: 1- Sharudan Azumi. 2- Rukunan Azumi. 3- Abubuwan da suke vata Azumi. 4- Abubuwan da aka karhantawa mai Azumi. 5- Sunnonin Azumi. Duk wadan nan ya kamata mai azumi yasansu. kuma Insha Allah zamuyi bayaninsu daya bayan daya. Musani Azumi yana daga cikin manya-manyan ayyukan da ake bautawa Allah (S.W.T). Saboda girmansa nema Ubangiji madaukakin sarki yake cewa: Azumi nawa ne acikin hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito cewa: "DUK WANI AIKIN DA DAN ADAM YA AIKATA WANNAN NASANE SAI DAI AZUMI SHI WANNAN NAWANE, NINE KUMA NAKE YIN SAKAYYA IDAN ANYISHI". Saboda girmansa da Albarkar dake cikinsa ne yasa Sahabbai idan yakusa qarewa suke kuka kuma suke fatan Allah ya nuna musu wani. Allah yanuna mana wannan wata lafiya yabamu ikon azumtarsa. Yasa muna cikin wadanda za'a 'yanta a cikinsa. Darasi nagaba zanci gaba. INSHA ALLAH. www.hanyantsira.blogspot.com whatsapp 09039016969 Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/ Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM,WHATSAPP, da sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.Manzon Allah (saww) yace:"WALLAHI IDAN ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA,YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAKUMMA"
Home »
FATAWA AKAN AZUMI.
» darasi na 9
No comments:
Post a Comment