Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

NA RISKI LIMAN A RAKA'A TA BIYU, KOZAN IYA YIN ADDU'AR BUDE SALLAH ???

NA RISKI LIMAN A RAKA'A TA BIYU, KOZAN IYA YIN ADDU'AR BUDE SALLAH ???

NA RISKI LIMAN A RAKA'A TA BIYU, KOZAN IYA YIN ADDU'AR BUDE SALLAH ??? DAGA ZAUREN 🕋HANYAN***TSIRA🕋 Assalam Malam inada Tambaya ?. Shin idan an fara sallah kazo zakabi jam'i, zaka karanta addu'ar da ake yine bayan kabbarar harama ??? Amsa: ===== ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ . To dan uwa abin da malamai suka fada shine: Mutukar ya riski liman a mike, to zaiyi addu'ar bude sallah, sannan ya karanta fatiha, koda kuwa a raka'a ta biyu ne. Saidai idan ya riski liman a ruku'u, to zai shiga tare dashi, kuma addu'ar bude sallah zata fadi daga kansa, saboda wurin yinta yawuce. Raka'ar da kafara samu tareda liman, ita ceraka'ar farko a wajenka, wannan yasa zakayi addu'ar bude sallah, koda kuwa shi liman a raka'a ta uku yake kota hudu. Wannan shine zance mafi inganci. Idan ka riski liman a tsaye amma abin daya rage yayi ruku'u, bazai isa ka karanta addu'ar bude sallah ba, sannan ka karanta Fatiha, to zaka karanta fatiha, kabar karanta addu'ar bude sallah, saboda addu'ar bude sallah sunnah ce, karanta fatiha ga mamu kuwa wajibice a wajan wasu malaman. Domin neman Karin bayani sai kuduba Al-majmu'u na Nawawy mujallady na 3/276 da kuma Majmu'ul fataawa 30/150. Allah shine mafi sani. *✍💖Muhd_Abba_Gana💖* www.hanyantsirah.blogspot.com 📗📘 whatsapp 09039016969 Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like 👇 👇 https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/ وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate