Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

makomar dan kafiri jinjiri

tamabyoyi.jpg

Malam menene makomar dan kafiri jariri idan ya mutu ???

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Assalamu Alaikum
Malam menene makomar dan kafiri jariri idan ya
mutu ???Wai da gaske dan Al-jannah ne ???
Allah yakarawa malam lafiya.

(Daga Hafiz Lukhman).

AMSA
-----------------------------------------------


ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.To malamai sunyi sabani akan yadda za’ayi da ‘ya’yan kafirai zuwa maganganu:

1. Allah zai sakasu a Aljanna, saboda basuyi aikin da Allah zaiyi musu azaba ba.

2. Akwai malaman da sukace za’ayi musu
jarrabawa ranar alkiyama.

3. Akwai wadanda suka tafi akan mayar da lamarinsu zuwa ga Allah, kada ayi musu shaida da wuta ko Aljanna, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.
“Allah ne ya san abin da sukayi nufin aikatawa”.kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai
lamba ta: 1384.

4. Akwai malaman da suka tafi akan cewa:
‘Yan wuta ne.Sai dai babban malamin nan Ibnul-kayyim ya rinjayar da Magana ta farko, wato suna Aljanna,saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi.
“Kowanne abin haihuwa ana haihiuwarsa ne akan
musulunci, iyayansa ne suke zamar dashi
bayahude ko banasare”Kuduba Sahihul Bukhari hadisi mai lamba ta :1385.
Su kuma gashi sun mutu suna yara kaga suna nan akan musuluncinsu.Sannan Allah yana cewa:“Bamu kasance munayin azaba ba, harsai mun aiko manzo” (Suratul Isra’i aya ta: 15).kaga su kuma basu balaga ba, balle su fahimci
abinda mazanni sukazo dashi, sannan kuma suba azzalumai bane, azabar Allah kuma tana tabbata ne
ga azzalumai.Don neman Karin bayan kuduba:(Darikul hijratain :387).Allah Shine mafi sani.

www.hanyantsira.mywapblog.com


whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate