Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

TAMBAYA

tambaya-da-amsa.jpg

TAMBAYA

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Assalamu alaikum mallam kamar yanda wasu suke fada a kwai wani hadisi da yake nuna cewa in dan mutum yayi sallam a baya alhali jam,i bai ciki ba bashida sallah mallam mene gaskiyar maganan

-AMSA-
*************************

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

hadisine ingantacce wanda yayi sallah a bayan sahu shi kadai bashi da sallah haka annabi (S.A.W) yace dan haka idan kazo masallaci bai kamata ka tsaya a bayan tsahu kai kadai ba sai se in sahun dake gabanka ya cika sai ka tsaya a bayan sahu kai kadai toh wannan babu laifi amma abinda ake magana shine ga sahu a gaba bai cika ba sai ka tsaya a baya ka fara sallah kaika dai har ka gama wani baizo kun hadu ba toh kai baka da sallah, wannan hadisin malamai sun masa fassarori daban daban kan maganganu guda uku na farko suke cewa wannan hadisin ya shafi koh wace irin sallah nafila da kuma ta farilla sannan wannan hadisin yana alauhumin babu yanda zakayi sallah a bayan sahu kai kadai yazo sallan ka ta inganta akwai masu wannan ra,ayin akwai kuma wayanda suke cewa da akwai wannan hukuncin amma an shafeshi amma zance mafi inganci wannan hukuncin yana nan tabbas cikin musulunci kuma idan mutum yayi sallah a bayan sahu shi kadai matukar a gabansa akwai wuri ya ki shiga dan ra,ayinsa toh bashi da sallah amna idan yazo ya samu waje ya cika bayan zaiyi ya samu sahu a gaba sai ya tsaya a baya yayi sallah shi kadai har aka gama sallah toh wannan sallarsa tayi saboda me saboda rashin kudura wajen ya shiga gaba dan gaban tarika ta cika kuma ka,ida sannaniya cikin shari,a shine duk abinda aka wajabta maka ana kallon abu guda biyu kafin wajibtin nan ya tabbatu akanka abu na farko ikon aiwatarwa abu na biyu kana sane da abun yayin da aka rasa hudura kaso kasamu waje sai ka kasa toh wannan kasawan ta sauke ma wajibtin yanzu wajibine ka shiga cikin sahu amma kazo sahun ya cika ba yanda za,ayi ka shiga kaga wajab cin shiga ya fadi idan ka tsaya baya kayi sallah toh sallah tayi kyau abu na biyu kuma dayakesa a sauke ma wajibci shine mantuwa ka tashi yin abu sai ka manta baza a kamaka da laifin cewa kakiyi ba koh da wajibine abun saboda mantuwa sai lokacin da ka tuna toh yanzu wajibcinsa ya hau kanka ALLAHU A,ALAM

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

TAMBAYA

tamabyoyi.jpg

TAMBAYA

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Malam ina da tambayoyi guda biyu kamar haka:

{1}. Shin Malam ya halarta miji ya sanya hannu a cikin farjin matarsa a matsayin nau'i na biyan bukatarta da kuma kara mata jin dadi yayin saduwa ?

{2}. Shin akwai lokacin da (safe, rana,
yamma,dare), yafi cancanta miji ya sadu da matarsa abisa koyarwa ta sunnah ?

Allah ya Kara daukaka. Amin.
(Daga Sulaiman Muhammad Faisal).

AMSA
************************

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

1. Eh da zarar an daura aure atsakaninku, to
matarka ta zama halal agareka kanada damar taba ko ina asassan jikinta. Sannan dangane da sanyah hannu agabanta domin tayar da sha'awa alokacin saduwa, shima ya halatta. Mutukar dai yin hakan bazai kai izuwa ga
cutarwa agareta ba.

{2}. Eh ya halatta mutum yasadu da matarsa aduk
lokacin da sukaji sha'awar yin hakan.
Amma akwai wasu lokuta guda 3 mafiya dacewa wadanda Allah ya fadesu acikin Suratun nuur.Sune kamar haka:

{1}. Kafin Asubah.

{2}. Lokacin barcin Rana (wato Sanda ake tube sutura saboda zafin rana).

{3}. Bayan sallar Isha.
Wadannan loakatai su ake kira lokutan al'aura na muminai.
Don haka ma Allah ya umurcemu da cewar
kadamu kyale bayinmu da masu yimana hidima,
da Qananan yaranmu suna shigo mana batare da izini ba awadannan lokuta.
Wallahu a'alam.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

TAMBAYA

tambaya-da-amsa.jpg

Tambaya

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Malam ina yawan wani mafarki wanda yake
tayarmin da hankali.
Sai naga a mafarkin ana nuna min TASHIN QIYAMA a zahiri.
Ana nuna min lallai tashin qiyama gaskiyane,nakanyi mafarkin exactly iri daya kullum innayi
baccin rana kuma nakan farka arazane a firgice cikin tashin hankali. Amma ban tabayin irin mafarkin da daddare ba ko
sau daya. Malam toh koh menene hakan.?
Nagode
(pls hide my id)

AMSA
********************************

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Shidai mafarki Kashi 2 ne.

{1}. Mafarki mai kyau wanda yake zuwa daga Allah
(swt).

{2}. MUMMUNAN MAFARKI wannan daga shaitan yake zuwa.(kamar yadda sahihan hadisai suka tabbatar).Shi Mafarkin da yake zuwa daga Allah din yarabu
zuwa kashi 3.

{1}. Yakan zo ta fuskar Umurni ko hani (kamar
mafarkin Annabawa kenan (a.s).

{2}. Yakan zo da bushara... Kamar ka ganka a aljannah, ko ka ganka cikin Koshin lafiya, etc.

{3}. Yakan zo da Gargadi.. Kamar irin wannan naka din kenan. Saboda haka mafarkin ganin tashin alkiyamah,kuma acikin Tashin hankali, WANNAN GARGADI
AKEYI MAKA. Ina baka shawarar cewa ka gyara halayenka da
dabi'unka. Kuma idan kana da iyaye araye, to wajibi ne kaje ka gyara dangan takarka dasu.
Idan kuma akwai abinda kasan kana aikatawa aboye, to LALLAI KAYI KOKARI KA DENA!!

Allah y shiyemu baki daya.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

TAMBAYA

tamabyoyi.jpg

TAMBAYA

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Salamu alaykum.
Malam tambayata anan shine; idan mutum yanada alwala saiya sumbaci matarsa (kissing dinta), alwalarsa ta karye ? Kuma meye mafita?.

(Daga:SUNUSI SANI ALASSAN KAFIN MAIYAKI).

AMSA
*******************************

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Hadisi ya inganta daga Sayyidah AISHA (RTA)
cewa: "MANZON ALLAH (S.A.W) IDAN YAGAMA ALWALA
YAKAN SUMBANCI WATA DAGA CIKIN MATANSA, SANNAN YAFITA ZUWA SALLAH BA TARE DAYA SAKE ALWALA BA"
(Abu dawud, nisa'eey suka ruwaito shi)

Dangane da wannan mas'alar akwai maganganu
guda uku da malamai sukayi. SHAFI'IYYAH SUNCE Shafar mace ko kissing yana karya alwala kai tsaye.
MALIKIYYAH DA HANBALIYYA SUNCE:
Alwalarsa bata karyeba, saidai in yayine da niyyar sha'awa.

HANAFIYYA SUNCE:
Alwalarsa bata karye ba saidai in wani abu yafito daga gabansa.

WALLAHU A'ALAM.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

TAMBAYA

tamabyoyi.jpg

TAMBAYA

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Slm Malam dan ALLAH yahalatta mutumin da yake
da aure yaringa kallon film din BLUE FILM shi da matarsa ?

(Daga Aminu SBS)

AMSA
==========================

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

A'a bai halattaba, yin hakan haramunne, Allah (s.w.t) ya tsinewa mai kallon tsiraici da wanda
yake nunuwa.Akwai zunubi mai tarin girma, domin gudun kada mutum yafada zina yasa yayi aure, idan akace mutum yayi aure baya samun biyan bukata da
matarsa ta sunnah dole saiya kalli kafirai maqiya Allah da Manzonsa suna tafka masha'a suna aikata
zuna a fili yazama auren nasa bai katangeshi daga zina ba kenan.Duk ma'auratan da suka sabarwa kansu da irin
wannan muguwar dabi'ar tunda wuri sudaina. Bazasu ta6a samun biyan bukata ta wannan hanyar
ba. ABIN DAYA KAMATA SUYI SHINE:
=================
matsayinsu na ma'aurata su cire kunya su zauna
su tattauna tsakaninsu, akan shi mai gidan ko ita
uwar gidan wanne abu yafi so ko wanne abu tafiso tayi masa ko yayi mata a lokacin kwanciyarsu ta
aure ??? Wannan shine matakin daza su dauka amma maganar kallon B.f haramunne Allah (s.w.t) yana
fushi da ma'auratan da basa kishin junansu.
Da fatan ma'aurata zasu kiyaye. Allah ka aurar da matasanmu maza da mata su
huta da wannan bala'in albarkacin Muhammadu
Rasulullah (s.a.w).

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

TAMBAYA

tambaya-da-amsa.jpg

TAMBAYA

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Assalamu alaikum mallam kamar yanda wasu suke fada a kwai wani hadisi da yake nuna cewa in dan mutum yayi sallam a baya alhali jam,i bai ciki ba bashida sallah mallam mene gaskiyar maganan

-AMSA-
*************************

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

hadisine ingantacce wanda yayi sallah a bayan sahu shi kadai bashi da sallah haka annabi (S.A.W) yace dan haka idan kazo masallaci bai kamata ka tsaya a bayan tsahu kai kadai ba sai se in sahun dake gabanka ya cika sai ka tsaya a bayan sahu kai kadai toh wannan babu laifi amma abinda ake magana shine ga sahu a gaba bai cika ba sai ka tsaya a baya ka fara sallah kaika dai har ka gama wani baizo kun hadu ba toh kai baka da sallah, wannan hadisin malamai sun masa fassarori daban daban kan maganganu guda uku na farko suke cewa wannan hadisin ya shafi koh wace irin sallah nafila da kuma ta farilla sannan wannan hadisin yana alauhumin babu yanda zakayi sallah a bayan sahu kai kadai yazo sallan ka ta inganta akwai masu wannan ra,ayin akwai kuma wayanda suke cewa da akwai wannan hukuncin amma an shafeshi amma zance mafi inganci wannan hukuncin yana nan tabbas cikin musulunci kuma idan mutum yayi sallah a bayan sahu shi kadai matukar a gabansa akwai wuri ya ki shiga dan ra,ayinsa toh bashi da sallah amna idan yazo ya samu waje ya cika bayan zaiyi ya samu sahu a gaba sai ya tsaya a baya yayi sallah shi kadai har aka gama sallah toh wannan sallarsa tayi saboda me saboda rashin kudura wajen ya shiga gaba dan gaban tarika ta cika kuma ka,ida sannaniya cikin shari,a shine duk abinda aka wajabta maka ana kallon abu guda biyu kafin wajibtin nan ya tabbatu akanka abu na farko ikon aiwatarwa abu na biyu kana sane da abun yayin da aka rasa hudura kaso kasamu waje sai ka kasa toh wannan kasawan ta sauke ma wajibtin yanzu wajibine ka shiga cikin sahu amma kazo sahun ya cika ba yanda za,ayi ka shiga kaga wajab cin shiga ya fadi idan ka tsaya baya kayi sallah toh sallah tayi kyau abu na biyu kuma dayakesa a sauke ma wajibci shine mantuwa ka tashi yin abu sai ka manta baza a kamaka da laifin cewa kakiyi ba koh da wajibine abun saboda mantuwa sai lokacin da ka tuna toh yanzu wajibcinsa ya hau kanka ALLAHU A,ALAM

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

TAMBAYA

tamabyoyi.jpg

TAMBAYOYI

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Malam ina da tambayoyi guda biyu kamar haka:

{1}. Shin Malam ya halarta miji ya sanya hannu a cikin farjin matarsa a matsayin nau'i na biyan bukatarta da kuma kara mata jin dadi yayin saduwa ?

{2}. Shin akwai lokacin da (safe, rana,
yamma,dare), yafi cancanta miji ya sadu da matarsa abisa koyarwa ta sunnah ?

Allah ya Kara daukaka. Amin.
(Daga Sulaiman Muhammad Faisal).

AMSA
************************

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

1. Eh da zarar an daura aure atsakaninku, to
matarka ta zama halal agareka kanada damar taba ko ina asassan jikinta. Sannan dangane da sanya hannu agabanta domin tayar da sha'awa alokacin saduwa, shima ya halatta. Mutukar dai yin hakan bazai kai izuwa ga
cutarwa agareta ba.

{2}. Eh ya halatta mutum yasadu da matarsa aduk
lokacin da sukaji sha'awar yin hakan.
Amma akwai wasu lokuta guda 3 mafiya dacewa wadanda Allah ya fadesu acikin Suratun nuur.Sune kamar haka:

{1}. Kafin Asubah.

{2}. Lokacin barcin Rana (wato Sanda ake tube sutura saboda zafin rana).

{3}. Bayan sallar Isha.
Wadannan loakatai su ake kira lokutan al'aura na muminai.
Don haka ma Allah ya umurcemu da cewar
kadamu kyale bayinmu da masu yimana hidima,
da Qananan yaranmu suna shigo mana batare da izini ba awadannan lokuta.
Wallahu a'alam.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

yadda ake warware sihiri a musulunci

YADDA AKE WARWARE SIHIRI

TAMBAYA:

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Assalamu alaikum.
Dan Allah malam a fitar dani daga cikin duhu gameda abin da yake damuna. Mahaifiya tace taje gurin Boka ayi mata maganin ciwon mara da yake damunta, tace tana da ciki yakai shekara guda da rabi, amma likitoci sunyi scanning sunce ba komai tosai Bokan yace mata asiri akayi mata, kuma zaiyi mata magani nan take ta haife abinda yake cikinta amma zata kawo tunkiya da dubu bakwai, sai take min magana in kawo kudi a sayi tunkiyar kuma akai masa dubu bakwan, to gaskiya malam zuciyata bata aminta da Bokan bane. Shiyasa Nakeso kabani fatawa shin irin wannan hanyar ta magani ta halatta a addini ? Idan bata halatta ba wacce hanya zanbi wajen qin biyan kudin da kuma sanar da ita ? Wassalam nagode malam Allah yaqara basira.

(Daga Binta Umar).

AMSA
------------------------------------------

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To ‘yar uwa, tabbas ba'a warware sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin
Alqur’ani. Wasu malaman sunyi bayani cewa:Ana iya warware sihiri ta hanyar karanta wadannan ayoyi kamar haka:

1- Ayatul-Kursiyyu.
2- Quliya.
3- Ikhlas.
4- Falaki da Nasi.
5- Sai kuma ayah ta: 117 zuwata 122, cikin Suratul
A’araf.
6- Sai kuma Ayah ta: 79-81 cikin Suratu Yunus.
7- Sannan sai Ayah ta: 65-70 cikin Suratu Dhaha.Za’a karanta su, sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya guda bakwai, sannan ayi wanka dashi a waje mai tsafta.Haka ake magance sihiri cikin yardar Allah. Bai halatta ki taimaka mataba, wajan bada
wadannan kayan da boka yanema duk da cewa mahaifiyarkice.
Saboda ba’a yiwa iyaye biyayya a wajen sabon Allah.Ya wajabta gareki kayi mata nasiha cikin hikima,kisanar da ita cewa:Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa:“Duk wanda yaje wajan boka, ya tambaye shi wani
abu, Allah bazai amshi sallarsa ba, ta kawana
arba’in”Muslim ya rawaito acikin hadisi mai lamba ta:2230. Kinga idan mutum ya mutu acikin wadannan
kwanaki akwai matsala, musamman ma tun da akwai hanyar da shari’a ta yarda da ita.Sannan awani hadisin kuma yana cewa:“Duk wanda yaje wajan boka ya gaskata abin daya fada, to tabbas ya kafurce da abinda Annabi Muhammad yazo dashi”Kuduba Sunanu-Abi-Dawud hadisi mai lamba ta:
3904, kuma Albani ya inganta shi.INA GANIN DA IRIN WADANNAN HADISAN ZAKI IYA
GANAR DA ITA, TA DAWO KAN HANYA. Allah Shine mafi sani.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

ZUCIYATA

tamabyoyi.jpg

Malam zuciyata tanason aikata sa6o, yaya zanyi
na hanata ?

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Salam, malam a cikin zuciya ta ina jin tsoron Allah,kuma ina son bin umarnin Allah, saidai ina yawan sa’bon Allah kuma, malam inaso a taimake ni da shawara akan hakan ?

(Daga sadis Auwal).

AMSA:
-------------------------------------------------

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.To dan uwa, ina fatan zaka karanta wannan ‘kissar
da idon basira, domin zaka sami shawarar da kake bukata gata kamar haka:

Wata rana wani saurayi yaje wajen Ibrahim ‘dan Adhama, (‘daya daga cikin magabata), sai yace
masa zuciyata tana tunkuda ni zuwa sa’bo, kayi min wa’azi. Sai ya ce masa:“Idan ta kirawo ka zuwa sa’bawa Allah to ka saba masa, amma da sharuda guda biyar.
Sai saurayin ya ce fadi mujisu Sai yace:

1. Idan zaka sabawa Allah, to kabuya a wurin da bazai ganka ba, sai saurayin yace:
Tsarki ya tabbata ga Allah, yaya za’ayi na boye masa, alhalin babu abin da yake ‘buya gareshi ???Sai yace:Yanzu bakajin kunya kasa’ba masa alhali kuma yana ganinka.

2. Idan zaka sabawa Allah to karka saba masa acikin kasarsa, sai saurayin yace:
Tsarki ya tabbata ga Allah, ina zanje, alhali duka duniya tasace ???Sai yace masa:
Yanzu bakajin kunya kasa’ba masa alhali kana zaune a saman kasarsa ?

3. Idan zaka sabawa Allah to kadaina cin arzikinsa.Sai saurayin yace:Tsarki ya tabbata ga Allah, ta yaya zan rayu alhali duka ni’imomi daga gareshi suke ?Sai yace masa:
Yanzu ba kajin kunya ka sa’ba masa alhali yana ciyar da kai kuma Yana shayar dakai, Yana baka
karfi.

4. Idan ka sabawa Allah, to idan mala’iku sukazo tafiya dakai Wuta, kace bazaka tafi ba Aljanna za ka.Sai saurayin yace:Tsarki ya tabbata ga Allah ai sunfi ‘karfina, korani
zasuyi.

5. Idan ka karanta zunubanka a takardarka ranar
alkiyama kace ba kaine ka aikata suba.
Sai saurayin yace:
Tsarki ya tabbata ga Allah, ina mala’iku masu kiyayewa, sai yafashe da kuka yatafi yana maimaita
wannan Kalmar ta karshe.IN HAR KANA TUNA ‘DAYA DAGA CIKIN WADANNAN IDAN ZAKA AIKATA ZUNUBI, TO TABBAS ZAKAJI KUNYAR ALLAH.Tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki.
Ya Allah ka tsarkake mana zukatanmu daga sabo.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

LIMAMIN MU YA MANTA AYA A SALLAH

tambaya-da-amsa.jpg

LIMAMINMU YA MANTA AYA DAYA A FATIHA ?

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

LIMAMINMU YA MANTA AYA DAYA A FATIHA ?

Assalamu alaikum, malam barka da qoqari.Mal. Ya matsayin sallar da liman ya tsallake aya
guda a cikin fatiha ???
Jazakallah.
(Daga Halliru abdullahi)

AMSA.

=======================

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.To dan'uwa Annabi (s.a.w) yana cewa:"Babu sallah ga wanda bai karanta fatiha ba"kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta:723.Malamai sunyi sabani akan Idan liman ya manta
aya daya a Fatiha, a sallar da take ta farilla, bai tuna ba, sai bayan yayi sallama, wasu malamai sukace zaiyi sujjadar rafkannuwa.
Amma zance mafi inganci shine:Idan har ba'a samu lokaci mai tsawo ba, to sai yatashi yasake raka'a daya.Idan kuwa an samu tazara mai tsawo tsakanin
lokacin daya tuna da kuma lokacin sallamarsa, to
zai sake sallar ne gaba dayanta, saboda fatiha
rukuni ce ta sallah bata tsayawa sai da ita, kamar yadda hadisin daya gabata yake nuni.Domin neman Qarin bayani sai aduba Fatawaa
Alajna Adda'ima:5/331.
Allah shine mafi sani.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

MUTANE UKU ALLAH BA ZAI MUSU RAHAMA BA

tunatarwa.jpg

Mutane 3 Allah bazai yi musu rahmaba.

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

MUTANE UKU ALLAH YA HARAMTA MUSU SHIGA ALJANNAH
Manzon Allah (SAW) Yace:"Mutane uku Allah ya haramta musu shiga Aljannah.

1. Wanda ya dawwama yana shan giya.

2. Da mai wulakanta iyayensa.

3. Da wanda yake barin Iyalansa suna aikata Fasadi.

[Nasa'I, Hakim, Bazzar, Ahmad].

Ya Allah ka tsaratar damu daga fushinka.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

MANYA MANYAN AIYUKAN ZUNUBAI

tamabyoyi.jpg

Manya Manyan Aiyyukan Zunubi

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

WADANNE AYYUKANE SUKAFI KOWANNE AIKI GIRMAN ZUNUBI ?

Abdullahi dan Mas'ud yace:Wata rana na tambayi Manzon Allah (S.A.W) nace:Ya Manzon Allah a Duk cikin laifukan da ake yiwa Allah wane laifi ne yafi kowane laifi girman Zunubi a wajan Allah (s.w.t) ?Sai Manzon Allah (S.A.W) yace:

1. Ka sanya wa Allah kishiya (Shirka) Alhalin Shi ya halicce ka shi kadai. Sai Abdullahi dan Mas'ud yace tabbas wannan
babban al'amari ne.
Sai kuma me?

2. Manzon Allah (S.A.W) yace:Ka kashe danka don kar yaci abinci tare dakai a
rayuwa, dan kar kadauki da wainiyarsa.
Sai Abdullahi yace:
Sai kuma me?

3. Manzon Allah (S.A.W) yace:Kayi Zina da matar makwafcin ka.Yan Uwa kunji a duk cikin laifukan da yafi girman zunubi a wajen Allah bayan shirka.Bayan ita sai Kisan kai, ba wani laifi da ya kai lafin
Zina a musulunci girman zunubi.
Duk wanda ya dauki zina amatsayin sana'a, ko a matsayin aikin yi toh Wallahi ya gaiyato fushin Allah akan sa, kuma yana sone ya jefa Al'umma acikin masifa cikin bala'i, kuma zai gamu da
masifu, zai gamu da bala'i zai gamu da walakanci tun a duniya kuma zaiyi mum munan karshe, a
lahira kuma zai gamu da azaba mafi muni.
Allah ya kare mu daga aikata wadan nan manyan laifuka, ya kuma karemu daga sharrin shaidan,Allah ya shiryemu baki daya.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

gurare da aka haramta wa maxe ta kalla a jikin yar uwanta mace

tambaya-da-amsa.jpg

Wadanne gurarene aka Haramta mace takalla ajikin 'yar uwarta mce ?

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Malam menene hukuncin mace tabayar da jikinta
ga mata yan’uwanta don ayi mata wanka saboda kwalliya ko irin dilka da halawa din nan wai haramunne Koda ta rufe mamanta da mazaunanta ?Idan haramun ne kenan daga ina zuwa inane
tsiraicin mace da bai kamata yar’uwarta mace ta gani ba ?
Jazakallahu khairaljazaaa.
(Daga Murjanat Sunusi).

AMSA
-------------------------------------------

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.To ‘yar uwa malamai sunyi sabani gameda tsaraicin mace ga ‘yar’uwarta musulma.

Akwai wadanda suka tafi akan cewa:

1- Bai halatta ‘yar uwarta mace taga wani abu a jikinta ba, sai abin daya saba bayyana a tsakanin
mata.Idan suna zaune isu-isu, kamar kafa da hannu da fuska da wuya da makamacin haka.

2. Saidai abin da mafi yawan malaman fiqhu suka tafi akai shine:
Al’aurar mace ga ‘yar uwarta musulma tana farawa ne daga cibiya zuwa guiwa, kamar yadda al’aurar maza take a tsakaninsu.
Don haka bai hallata tabari wata mace takalli samada wannan wurin da aka iyakance ba.

3. Amma idan kafira ce matar to malamai sunyi bayani cewa bazata kalli wani abuba, sai abin da
yasaba bayyana, don haka sai a kula lokacin da za’aje dilka wajan wacce ba musulma ba, don kada garin neman gira a rasa ido .
Sannan a bisa wannan bayanin da kikayi, dilkar da kika siffanta zata zama bata halatta ba, tunda za’a
ga abin da shari’a bata hallatata a gani ba.
WALLAHU A'ALAM

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

shaawar boye...

tunatarwa.jpg

Sha'awar 6oye

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Wata rana Wani Sahabin Manzon ALLAH (S.A.W)
Mai Suna Shaddad Bin Aus (R.A), Yafashe Da
Kuka.Sai Aka Tambaye Shi Dalilin Yin Kukan nasa.Sai YaCe:-
"Wani Abu Ne, Da Naji Daga Manzon ALLAH
(S.A.W) Na Tuna, Shi Yasani Kuka.NaJi Manzon ALLAH (S.A.W) Yana Cewa:
Ina Jiwa Al'ummata Tsoron SHIRKA Da Sha'awar boye)"Sai Nace:"Ya RASULULLAHI (S.A .W)! Al'ummarka Zatati
Shirka a Bayanka???
Sai YaCe:"E! Amma Bazasu Taba Bautawa Rana Ko Wata Ko
Dutse Ko Gunki Ba.
Sai Dai Zasu Riqa Yin RIYA Da Ayyukansu.

2. Sha'awar Boye Kuma, Dayansu Sai Yawayi Gari Yana Mai Azumi.Sai Wata Sha'awa Daga Sha'awoyinsa Ta Bijiro
Masa, Sai Ya Bar Azumin Nasa (ma'ana ya karya azumin).(Imam Baihaqi Ya RuwaitoShi a Cikin Shu'abul-
Iman).HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL!WANNAN SHINE HALIN DA YAWANCIN MUSULMI A YAU SUKA TSINCI KANSU.YA ALLAH KA TSERATAR DAMU DAGA WANNAN
BALA'I MAICI BAL-BAL KAMAR WUTAR DAJI.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

Tambaya na 1...

tamabyoyi.jpg

Tambaya ta 1

DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Assalamu Alaikum.
Malam dan Allah a boye sunana:Nice ina tare da saurayina amman ba'a gari daya
muke ba, kusan kullun muna waya amman sai yanemi muyi sabon Allah.wato mu makin imagination muna sex da juna.
(i.e masturbation).
kuma nayi ta mishi wa'azi amman kullum abun karuwa yakeyi.
Mallam matsalar itace da farko da muka hadu a lokacin I dnt knw his character saina mishi
alkawarin bazan barshi ba, zan aure shi, kuma yanzu har ga Allah na canza ra'ayi akansa saboda halayen sa.Shin mallam idan na rabu dashi menene hunkucin alkawarin danayi ?

(Daga wata baiwar Allah).

AMSA
**************************

Allah yasaka miki da alkhairi.
kuma Allah ya Qara miki tsoron ALLAH afili da boye.Tabbas irin wadannan abubuwan da kikace saurayinki yana umurtarki dasu, suna daga cikin hanyoyin da shaidanun samari sukebi domin lalata
'ya'yan mutane.Ai kinyi masa alkawarine abisa zatonki cewar shi mutumin kirkine irin wanda kowacce mace takeso ta aura.Amma tunda halayensa sun nuna cewar shi shaydani ne, kuma mai neman lalata, wato irin
namijin da kowacce mace mai addini take QIN ta aura, to tabbas yazama WAJIBI ki Qaurace masa.
(kamar yadda Malam MAI AHALARI ya fada).
Kiqara godewa Allah tunda ya tsareki daga bin ra'ayin wannan shaydanin kuma kyawun fuska ko
dukiya ko zaqin bakinsa bai rudeki ba.
**Allah yana cewa:
"KARKU KARKATA IZUWA WADANNAN DA SUKA ZALUNCI KANSU, SAI WUTA TAQONA KU"
Malamai sukace:
DUK WATA ALAQAR DA BA'A QULLA TA DOMIN ALLAH BA, TO MUSIBACE QARSHENTA"Allah ya kiyaye.Yadda kika soshi tunda farko domin Allah, to yanzunma KI RABU DASHI DOMIN ALLAH.
zaki samu lada mai yawa awajen Allah.
domin Allah yanason masu yin soyayya ko kiyayya dominsa.
Kici gaba da addu'a. INSHA ALLAHU zaki samu wanda yafishi.
WALLAHU A'ALAM.

www.hanyantsira.mywapblog.com

whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka

Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate