Barka da zuwa shashin musulunci manufar bude wannan shafin shine Bayyana Yadda Musulunci Ya Haskaka Rayuwarmu

gyaran zuciya

tunatarwa.jpg

Domin gyaran zuciya


DAGA ZAUREN

HANYAN***TSIRA

Assalamun alaikum.
Allah yagafarta malam, wadanne abubuwane zanyi
domin gyara zuciyata da imanina ?Bissalam.

(daga Aminatu Farouk)

AMSA
*********************

ﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ .

Hakika wannan tambayar tanada muhimmanci
sosai.Kuma tabbas babu wani abinda yake gyara zuciyar Mumini face ambaton Allah (s.w.t).Allah (s.w.t) yana cewa:''KUYI SANI CEWAR DA AMBATON ALLAH NE ZUCIYA TAKE SAMUN NUTSUWA''Zikirin Allah (SWT) shine babban abinda yake raya zuciyar mumini kamar yadda Manzon Allah (s.a.w) yake cewa:"MISALIN WANDA YAKE ZIKIRIN ALLAH DA WANDA
BAYAYI, KAMAR MISALIN RAYAYYE NE DA MATACCE".
(bukhary da Muslim).
Babu abinda yake Katangewa zuciyar Mumini daga sharrin Shaitan face zikirin Allah (swt).Shugaba (s.a.w) yana cewa:
"HAKIKA MISALIN WANNAN (DA YAKE ZIKIRIN ALLAH), KAMAR MISALIN MUTUMIN DA MAQIYA (ABOKAN GABA) SUKA KOROSHI AGUJE, HAR SAI DAYA ISO WATA KATANGA MAI QARFI, YA SHIGA YA TSARE KANSA DAGA GARESU.HAKANAN BAWA BAZAI IYA TSARE KANSA DAGA
SHAITAN BA, SAIDA ZIKIRIN ALLAH"(tirmizy ne ya ruwaitoshi akan hadisi mai lamba 2,863).Sannan babu abinda yafi tseratar da mutum daga azabar Allah, kamar zikirin Allah.Manzon Allah (s.a.w) yana cewa:
"BABU WANI AIKIN DAYAFI TSERATAR DA BIL-ADAMA DAGA AZABAR ALLAH, KAMAR ZIKIRIN
ALLAH (azza wa jalla)."(Imamu Malik ya ruwaitoshi acikin Muwatta' juz'i na 1 shafi na 211 hadisi na 492.Da kuma Imamu Ahmad acikin Musnad juz'i na 5, shafi na 293, hadisi mai lamba 22,132).Babu abinda yake gyara imanin 'Dan Adam kamar ilimi da kuma aiki dashi..
Don haka munemi ilimin addini mai amfani.Kuma muji tsoron Allah. Mu aikata ayyuka na
kwarai.Allah ka shiryar damu akan tafarki madaidaici.

www.hanyantsira.mywapblog.com


whatsapp
09039016969

Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like

https://mobile.facebook.com/Hanyan-TSIRA-704286909673846/

وسلم عليكم ورحمت الله وبركاته
Share:

No comments:

Post a Comment

Advertise Your Product

Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Tallata Kayanka


Popular Posts

Author

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Translate