Alamomi 001-030
1. Aiko Annabi (sallallahu-alaihi-wasallam) {ranar
litinin, 21/Ramadan/0013bh daidai da 10/
August/610m} yana shekara arba'in 40 da wata
shida 6 da kwana goma sha biyu 12 lissafin wata/
shekara talatin da tara 39 wata uku 3 da kwana
ishirin 20.
2. Wafatin Manzon Allah (sallallahu-alaihi-
wasallam) ranar litinin 12/rabi'ul-Auwal/11ah yana
da shekara sittin da uku da kwana hu'du
3. Tsagewar wata
4. 'Karewar Sahabbai
5. Bu'de Baitil-Maqdis.
6. 'Barkewar Annoba;- mai kama da ciwon
dabbobi.
7. Bayyanar fitintunu masu yawa.
8. Bayyanar tashoshin tauraron 'Dan Adam.
9. Yaqin Siffaini.
10. Bayyanar khawarij.
11. Masu da'awar Annabta ta qarya
12. Yalwatar Arzi'ki.
Arzi'ki zai yalwata
13. Bayyanar wuta a Hijaz, dutse mai aman wuta.
14. Ya'ki da turkawa.
15. Bayyanar Azzalumai masu duka babu dalili.
16. Yawan zubar da jini da kashe-kashe
17. 'Dauke Amana;- ma su Amana zasuyi 'karanci.
18. Koyi da Yahudu da Nasara.
19. Baiwa zata haifi uwargijiyar ta.
20. Bayyanar masu tsirara-tsirara(basa shiga ta
addini)
21. Matsiya ta, Matasa masu kiwon awaki zasuyi
yin dogayen gine-gine.
22. Yin Sallama ga wanda aka sani kawai;- mutane
za su daina yiwa mutum Sallama sai sun sanshi.
23. Ya'duwar kasuwanci;- ko ina zai zama
kasuwa.
24. Mata zasuyi tarayya da mazansu a kasuwanci.
25. Wasu tsirarun 'yan kasuwa zasu mamaye
kasuwanci;- ya zama ba ayi dakai sai da yardarsu.
26. Shaidar Zur.
27. 'Boye shaidar gaskiya.
28. Yawan Rowa;- mutane zasu zama marowata.
29. Yanke zumunta.
30. Munana maqotaka.
Allah kasa mucika da imani.
Zamuci gaba Insha Allah.
Home »
ALAMOMIN ALQIYAMA.
» ALAMOMIN TASHIN ALQIYAMA. Kashi na 1
No comments:
Post a Comment